DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Na shiga uku Nura, wallahi tallahi dana ne, kana gani ya tafi amma baka tsayar dashi ba.”
“Idan har da gaske shine, kina zaune zai dawo da kafafun sa, waye ya kawo shi yanzu? Ra’ayin kansa ko? Toh shi zai dawo dashi kiyi shiru karki tara mutane.”
“Shikenan nayi shiru.”
Tace tana kama bakin ta kamar yarinya karama. Ciki suka koma duk ta kasa komai data rufe idon ta hoton fuskar sa kawai take gani, ta girma sosai ya zama babban saurayi me ji da kyau da gayu, shigar sa kadai ta tabbatar mata da shi din waye, anya zai karbe ta a matsayin mahaifiyar sa kuwa? Yanzu da bata da maraba da mahaukaciya duba da yadda duk ta lalace ta koma kamar wadda tayi jinya ga babu suturar arziki.
Ganin an kwana babu labarin Kamal yasa Alhaji Marwan baza jami’an tsaro sosai aka shiga neman sa, banda kuka babu abinda Ammi take, hakan ya karawa mishi damuwa sosai dan ba Hajiya Turai bata san wainar da ake toyawa ba.
Dakin sa ta shiga ta tarar dashi yana waya, zama tayi a gefen sa idon ta duk ya ɓaci saboda kukan dataa sha, ajiye wayar yayi bayan ya gama ya dube ta cikin kulawa yace
“Ki kwantar da hankalin ki in Sha Allah za’a ganshi.”
“An kira yarinyar da yake zuwa gani a Kano? Ina zargin ta dama ni chan hankali na be kwanta da ita ba.”
“Sirikar Aminini ce ashe, yarinyar da muke ta fafutukar nema ashe jikarmu ce, dan haka bani da matsala da yarinyar, idan kika ganta ma nasan kema irin ta Kamal din zakiyi, ki ji ta kwanta miki.”
“Bana son ta gaskiya, karo na farko dana fara jin mijina yana yabon wata bani ba.”
“Kishi?” Yace yana murmushi, gefe ta kawar da kanta tana bata fuska.
“Kinsan Adam yana raye?” Yace yana duban ta, duburburce wa tayi tace
“Ban gane ba?”
“Hello inspector.” Yace yana daga wayar
“What!!!” Ya mike tsaye da sauri
“Gani nan zuwa.” Ya katse kiran yayi hanya da sauri
: DG
37
©Hafsat Rano
★★★
Tafiya yake ba tare da yasan inda yake taka ƙafarsa ba, so yake yayi kuka ko zaiji sauƙin zuciyar shi, sai dai ashe kukan ma samu ne, tsawon shekarun nan yana rayuwa ne da mutanen da bashi da alaƙa takusa ko ma ta nesa dasu, mahaifiyar data kawo shi duniya na rayuwa a wani waje cikin tsananin talauci, da kunci, tabbas ba’a kyauta masa ba, sai dai akan Aminatu kusan shi gata akayi masa, rayuwa ce yayi ta cikin tsananin gata da dadi, ita kuwa aka dora mata rayuwar da bata dace da ko da me aikin gidan ba balle ita, ya ɗaya tilo da take buƙatar dukkan gata, gata mace me rauni.
Tunanin ta yadda zai fara sanar da kowa komai yake, idan har ya cigaba da boye gaskiyar abinda ya sani be kyauta wa Aminatu ba, haka be yi adalci ga iyayen da suke rikeshi bisa amana ba, suna bukatar yar su, itama tana bukatar iyayen da zasu nuna mata gatan data rasa.
Idon sa ya runtse tuno labarin rayuwar ta data bashi, da irin abubuwan data fuskanta, ya tausaya mata kwarai sai dai a yanzu shine abin a tausaya wa, rashin sa’ar iyayen k’warai masu nagarta.
“Baka gaji da tafiyar kasan bane?”
Ya tsinkayi wata murya a saman kansa, juyowa yayi ya kalli mutumin
“Ya kamata ace ka dan huta ai, bayan ka gano komai me ya kamata kayi?”
“Me kake nufi?” Ya katse shi yana duban shi
“Ina biye dakai tun barin ka gida, na kuma san abinda ya kawo ka, ina fatan bayyanar gaskiya be saka ka yanke hukunci da rayuwa ba.”
“Me yasa kake bina, ina kuma ruwan ka da rayuwa ta, waye kai ma a takaice.?”
“Wanda ya chanja maka rayuwa daga ta tsantsar talauci zuwa mafi kuloluwar daraja.”
“Adam!” Yace yana zaro ido
“Nine, Ina fata haduwar mu ba zata zamar wani babban al’amari ba.”
“Me nayi maka? Me yasa ka zabi da kayi wasa da rayuwa ta?”
“Idan kace wasa da rayuwa kana nufin ban kyauta maka ba, dubi suturar jikin ka, ka dubi kanka, kana tunanin ban maka gata ba? Toh ka bude kunnen ka kaji..”
“Ina so abin da ka binciko ya zama tarihi a ranka, wajibi ne ka boye komai ka cigaba da rayuwar dana zaba maka, idan baka sani ba, MD ne ya zabarwa yarsa irin rayuwar da take, shine silar komai, ya rabani da abubuwa guda biyu mafi soyuwa a gareni, shiyasa na zabar wa abinda zai haifa rayuwa mafi kaskanci.”
“Karya kake wa Daddy, babu abinda yayi maka karya kake, kuma wallahi sai na tona komai ko da zan dawo rayuwa ta ta asali.”
Murmushi yayi gami da cije lebensa na kasa
“Idan har na bar maka damar yin hakan ko? Yaro kenan, sunana kawai kake ji amma na wuce tunanin ka.”
“Ta Allah ba taka ba, duk abinda kake kullawa sai ya koma kanka.”
Hannu Adam ya harde yana duban shi, tafiya Kamal ya cigaba da sauri da sauri ba tare da ya sake waiwayo wa ba.
A wani irin yanayi iska ta dauki karar motar ta kai masa kunnuwan sa,da sauri ya juyo kafin ya iya tantance komai tayi sama dashi. Ƙarar daya kwalla ita ta jawo hankalin mutanen dake wucewa ta wurin jefi jefi.
A kid’ime yayi waje yana kwala wa Driver sa kira, kuka Ammi tasa tana binsa ganin kamar baya hayyacin sa
“Dan Allah ka sanar min abinda ya faru.”
“Kamal ne ya hadu da accident a Katsina.”
Abinda kawai ya iya cewa kenan ya fada mota, kuka ta saka me karfi ta fado motar.
Wani irin gudu driver yake kamar zai tashi sama, babu abin da kake ji sai sautin kukan Ammi, ikon Allah ne kawai ya kaisu, direct asibitn da aka kai shi suka wuce suna zuwa kasar tsaye suka nufi accident and emergency unit.
A lokacin ya riga ya zama unconscious be san wanda yake kansa ba, dukkannin fuskar sa an rufe ta da bandage sai karaya a hannun sa na haggu.
Tsananin tashin hankalin da suka shiga ba zai misaltu ba, sai ga Alhaji Marwan na share hawayen tsananin tausayin dan nasa, ba’a ta Ammi da kowa yasan yadda uwa kan shiga tashin idan abu ya samu danta.
Isowar Daddy ya d’an saukaka abun, kwarai ya tausaya wa aminin nasa yadda yaga ya koma a lokaci daya kamar wanda yayi kwanciyar shekara.
Tun bayan fitar Anas babu wanda ya sake magana a cikin su, kamar kurame sai dai idon sa na kanta duk sanda ta dago sukan hada ido sai yayi saurin basarwa yana maida kallon sa kan yar sa. Fita Baba Altine tayi ta basu waje dan sam bata ji dadin yadda akayi wa Anas ɗin ba, gefn Amal tayi zaman ta tana kallon yadda mutanen asibitin ke kaiwa da komowa.
Kiran wayar Farouk din akayi, kamar bazai daga ba ganin Iman na kokarin farkawa yasa shi dagawa dan kar a tashe ta, Ja’afar ne, baya kasar shima ya tafi karatu sai yanzu yake samun labarin dawowar Farouk din a wajen Dadah da sukayi waya shine ya gwada kiran tsohon layin sa na Mtn aikuwa sai gashi ya shigo.
“Da gaske ka dawo? Wow nayi mamaki wallahi.”
“Uhum… Na dawo, kana lafiya?” ya amsa masa
“Lafiya lou, sai dai banji dadin tafiyar ka ba Allah, ina tunanin baka san halin da Mummy ta shiga ba bayan tafiyar ka.”
“Ja’afar, kana ji? Ina wani abu yanzu very important, muyi magana anjima.”
Be jira amsar sa ba ya katse kiran yana jan dan karamin tsaki. Kallon ta yayi yaga shi take kallo, harara ya sakar mata
“Dan na kori dan iskan chan kike share ni ko?”
Yace yana baro kujerar da yake kai
“Ba haka bane…”
“Yaya ne? Ina lura dake har wani tasowa kikayi da ya kiraki.”
Ya zauna kusa da ita sosai a gefen gadon kafadarsa na gogar ta ta, wani iri taji tayi kokarin matsawa ya sake matso ta sosai.