DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ni ba haka bane.” Tace tana tashi tsaye, saurin chapko hannun ta yayi ya maida ita ya maida ita wajen da ta tashi yana dora kafadarsa a saman ta ta

“Mesa kike gudu na, bakiyi missing d’ina bane?”

“Ya Farouk?” Ta kira sunan shi

“Ehen ina jinki.”

“Dan Allah ka daina wa Ya Anas haka, kaga babu dadi, yayi min kokari sosai a lokacin da na fitar da tsammani da samun wani jin dadi ko cigaba a rayuwa, shine ya rike mu tamkar nasa, ya kula da dukkan al’amuran mu, ya tsaya tsayin daka wajen ganin na samu ilimi me amfani, wanda idan babu shi da tuni rayuwar mu ta lalace, watakila ma da tuni na zama mabaraciya ko na mutu saboda wahala.”

Tashi yayi sosai ya kalle ta idon sa na kankancewa

“Kina nufin dai yanzu ya fini wajenki ko? Saboda ya kashe muku kudi ke da Iman, shikenan, Ina so ki tambaye shi nawa ya kashe akan ku tun daga ranar farko zuwa yanzu sai na biya shi, tun da abin ya zama gori…”

“Subhanallah, kar kayi misunderstanding d’ina, ba abinda nake nufi ba kenan.”

“Me kike nufi? Shikenan dan yayi wahala daku sai ya bashi damar shiga hurumin da bana saba? Nayi magana kuma kin juya min magana ta, alamun ma ni yanzu bani da wani amfani wajenki.”

“Ya Salam!” Tace tana kallon shi,

“Wannan ba Ya Farouk d’ina bane, Ya Farouk d’ina me saurin fahimtar rayuwa ne kuma me yiwa mutum uzuri ne ko da yayi ba dai-dai ba.”

Kin tankawa yayi ya sake hade rai shi a dole an bata masa rai, ganin haka yasa tayi shiru itama saboda ta lura neman rigima kawai yake, ba kuma zata biye masa ba balle har ya samu galaba akanta.
  Dogon zango suka dauka ba tare da kowa ya sake magana ba, sosai ranta ya ɓaci, dan bata ga abinda tayi masa da zai sashi reacting haka ba, ganin zaman ya ishe ta yasa ta mike don zuwa waje dan ba zata iya cigaba da zama dashi haka yana share ta ba

“Zan koma gida.” Tace tana mik’ewa, da sauri ya kalle ta

“Iman din fa?” Yace cike da mamaki

Idon ta ne ya ciko da kwalla tayi saurin sa hannu ta goge

“Ba kana nan ba?” Ta amsa masa kai tsaye

“Akan nace masa dan iska ko?”

Yace yana kura mata ido, kin amsa masa tayi saboda yadda ranta ya ɓaci, ya gaza fuskantar ta s ranaram kishi ya rufe masa ido, gaba tayi kawai tana ji Iman din na kokarin tashi ta bude kofa tayi ficewar ta.

“Ya jikin nata?” Baba Altine tace

“Da sauki, ina ga idan drip din ya kare su sallame ta, muje gida.”

“Kamar ya? Muje gida ko naje gida? Na zata zaki zauna a sallame tan ne ko?”

“A ah, zai iya kula da ita ai, muje kawai.”

“Fada kukayi?” Baban tace

Gefen da Amal ke zaune Aminatu tayi saurin kallo ganin hankalin ta na wani wajen daban yasa tace

“Ya kasa fahimta ta.”

“Shikenan sai kuma kiyi zuciya da yarki? Wannan ai shashanci ne.”

“Toh ya zanyi? Tsawon lokaci ina zaman jiran dawowar sa, ya dawo kuma amma ba da halin da na sanshi ba.”

“Aminatu ita fa rayuwa da kika gani ba zaki ce mutum ya zama yadda kike sanshi a koyaushe ba, mutane na iya chanjawa, Sai dai chanjawar su ba zai sa kema ki chanja ba.”

Jikin ta ne yayi sanyi, ta zauna tana tunanin mafita, suna zaune likita yazo ya wuce su, ya shiga ciki, jim kadan ya fito yayi nasa wuri. Ba’a wani jima ba sai ga Farouk ya fito rike da Iman a kafadarsa ya wuce su, ido Aminatu ta zubawa bayan sa ganin be ko bi ta kansu ba, ji tayi kamar ta tashi tabi bayan sa sai dai bata da wannan karfin halin, tsam Amal ta tashi tabi bayan sa, Baba Altine ta yanka mata harara cikin bacin rai tace

“Me kikayi kenan?”

“Ya zanyi toh?”

“Muje.” Tace tana mik’ewa

Fitowa sukayi reception babu alamar su, suna fitowa parking lot suna fita daga asibitin. Wani iri taji ta rasa dalilin da Ya Farouk zai mata haka. Gida suka wuce Baba Altine nata yi mata fada akan abinda tayi, ko gaba kar ta sake irin wannan wautar. Ita dai jin ta kawai take bata iya cewa komai ba.

****Kwata-kwata ta kasa sukuni, tana yi tana duba wayar ta ko zata ga ya kira ta amma shiru kake ji, gashi kwarai tana so taji lafiyar yar ta, wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka, yayi mata laifi amma ya fita daukar zafi.
Ganin wankin hula na neman kaita dare yasa ta ajiye komai ta kirashi, lokacin ya gama shirya Iman cikin sabon kaya ya bata abinci da chocolate ta gama rigimar ya kaita wajen Ummin ta ya samu tayi shiru bayan ya bata wayar shi yayi mata downloading wani cartoon, shigowar kiran ya katse mata kallon ta, kuka ta saka masa hakan yasa shi saurin rejecting kiran.
Sororo tayi rike da wayar a hannu, mamaki ne ya cika ta , dan son sake tabbatar wa ta kuma kira a take akayi rejecting, Sosai zuciyar ta ta sosu, ta zame ta kwanta ranta na mugun suya.

Shigowar Dadah dakin uku tana son daukar Iman din Amma sam taki yarda, a shigowar ta na karshe ne take ce masa ina Aminatun bata bukatar yarta ne? Duba da rashin ta da tayi kwana biyu? Da yake har yanzu be gama sakin jiki da ita ba yasa yace mata yanzu zai zo ya kai mata ita.

****Ja’afar na ajiye wayar yayi saurin kiran Mummy dan yasan bata san da dawowar Farouk din ba, lokacin tana tsaka da aiki a system ɗin ta, da sauri ta ture komai ta shiga kiran layin Farouk din.
Kura wa kiran ido yayi, a hankali ya zare wayar daga hannun ta ganin har tayi bacci wajen kallon, katse wa kiran yayi ya cigaba da bin wayar da ido har sanda wani kiran ya sake shigowa.

“Farouk!”

“Na’am.”

“Yanzu Farouk ka bar kasar nan tsawon lokaci sannan ka dawo duk ban sani ba? Ka kyauta min kenan? Kasan yadda naji dana samu labarin tafiyar ka? Amma shine har ka dawo baka neme Ni ba?”

Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, kallon tasa yar yayi ya tuna yanzu shima fa uba ne, idan tasa yar tayi masa haka ya zaiji? Cikin kankan da murya yace

“I’m very sorry, kiyi min afuwa.”

Share hawayen fuskar ta tayi cikin dakewa tace

“Ina son ganin ka yaushe zaka zo?”

“Gobe ko jibi in Sha Allah.”

“Kazo gobe.”

“In sha Allah.”

Ajiye wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya, kura wa Iman ido yayi yana jin soyayyar ta na bin kowanne lungu da sako na jikin sa. Tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Aminatu yayi, sai yaji duk be ji dadi ba, atleast idan bazai bi ta a yadda ta ke tunani ba kada ya kuma bata mata rai.


Duk sunyi jigum babu wanda yake iya magana da dan uwan sa, gashi har an kwana babu alamun zai farka, dakin likitan ALHAJI Marwan ya shiga ya nemi a basu transfer,zai tsaya yi masa dogon bayani yace shi sam be yarda ba, dole ya amince ya sallame su suka dauke shi suka yi Abuja dashi ba tare da yasan me yake faruwa ba.
A chan gidan kuwa Hajiya Turai ta tada bori bayan ta samu labarin abinda ya faru, gaba daya masu aikin gidan sun taru a kanta tana ta kuka da kururuwa a kaita wajen jikanta, duk sunyi jigum jigum motar su ta shigo gidan, da sauri ta tashi daga zaman dirshan din da tayi ta nufi kan motar tana kuka.
Duk wanda ya ga Kamal a lokacin sai ya masa kuka, tuni Alhaji Marwan yayi nisa a shirye shiryen fitar dashi waje.
Cikin dare ya farka, duk suna kansa, da wani irin abu ya soma kafin ya fara magana da k’yar irin ta wanda ya galabaitu da wahala. Babu wanda yaji me yake cewa saboda yadda maganar tayi kasa, Ammi na kuka Hajiya Turai na yi, cikin yanayin kamar an fuzgo maganar ya furta

“Dad..dy.. A…mm..i.. itace.”

“Karka takura ma kanka da magana, dan Allah.”

Ammi tace tana kuka sosai, kukan shima yasa yana mika mata hannu, da sauri Daddy ya isa gareshi yana riko hannun sji

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button