DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kamal, look at me, menene? Kayi shiru kaji?”

“Daddy… Ami…natu.”

“A kira maka ita?” Yace yana shafa kansa, daga kansa yayi alamun eh

“Toh shikenan, kayi hakuri gobe zatazo kaji?”

Daga kansa yayi yana maida idon sa ya rufe.

“Kaga ni? Yarinyar nan me tayi masa? Yana wannan halin yana kiran sunan ta? Wannan wacce irin masifa ce? Wallahi bazan yarda ta lalata min rayuwar yaro ba.”

“Ya kamata ki duba lafiyar shi kafin ki tsaya tunanin komai, ni yanzu ta lafiyar sa nake, ba ta komai ba.”

Ran ammi ne ya ɓaci, ta kara jin haushi ta tsanar yarinyar da bata taba gani ba.

Rashin Sani!!!! Yafi dare duhu

Rano ????: DG

                       38

©Hafsat Rano

★★★
Kamal be sake farkawa ba saboda yadda karfin allurar yake, da safe ya farka amma sai dai har lokacin ba a hayyacin sa yake ba, dole aka sake masa wata allurar saboda ciwukan da ke jikin sa ma.
  Abincin kirki Ammi ta kasa ci saboda yadda abin ya dake ta, Hajiya Turai kuwa sai da aka bata magungunan ta na hawan jini sannan aka samu ta dawo daidai, dukkan su sun kasa matsawa daga in da yake, hakan kadai ya isa ka gane irin gata da soyayyar da suke masa.
  Babban likitan da aka hada su dashi dake nan Abuja Dr Ahmad (Ruhi Daya) ne ya iso cikin shigar sa data dace da tsari da zubin hallitar sa, tun fari shi Daddy yaso ayi wa magana ganin Alhaji Marwan din ya kafe da son dole sai ya fidda shi waje yasa ya kyale, sai dai tsaikon da za’a samu yanzu kafin a fitan yasa dole ya amince aka kira shi.
   Har wajen motar sa Alhaji MD ya k’arasa ya yi masa iso zuwa katafaren part d’insa inda aka ajiya Kamal din, har suka karasa suna tattauna wa akan abinda ya samu Kamal din da kuma abubuwan da Daddyn yake so ya taimaka masa dashi, a nutse ya amsa da zai yi iya yinshi sannan suka karasa ciki.
   Cikin kwarewa da sanin makamar aiki na cikakken consultant a bangaren ƙwaƙwalwa ya shiga bincike da son gano ko akwai wani damage a brain d’insa, a haka dai physically babu wani abu da zata nuna ko ya samu wata matsala ,sai dai yana bukatar bincika shi sosai, kai tsaye babban asibitn sa dake Maitama ya umarci a kaishi, anan yayi undergoing several tests kuma Alhamdulillah babu wata matsala internally sai wadda ta bayyana kowa ke ganin ta.

Cire glass din idonsa yayi bayan yasa tsaftacecen handy ya share zufar dake saman goshin sa ya kalli Alhaji MD yace

“Ina ganin zaman sa anan ɗin zai fi samun kulawa fiye da gida, sannan ka bamu dama muyi aiki sosai in Sha Allah zaka ji dadin aikin mu fiye dana kasashen wajen, please let give it a try, for now a ajiye fita dashi.”

“Shikenan, na yarda da ingancin aikin ku da asibitin ku, please kayi iya kokarin ka wajen ganin yarona ya samu lafiya, shi kadai nake dashi i can’t bear….”

Saurin katse shi yayi

“Babu abinda zai faru dashi in Sha Allah, ya riga yayi passing danger stage din so mu cigaba da addu’a.”

“In Sha Allah. Mun gode Dr.”

Fita yayi ya samu su Ammi ya sanar dasu abinda ya faru, cikin kankanin lokaci asibitin ya soma cika da yan uwan Ammi da abokan harkar Alhaji Marwan na kusa dana nesa, tuni labari ya game ko ina sai dai ba’a bar kowa ya ganshi ba sai ta window saboda yadda yake bukatar hutu.


Hasken ranar daya risketa har inda take kwance yasa ta gane gari ya waye sosai, da sauri ta tashi tana laluben wayar ta da glass din ta da sukayi nasu waje, sakawa tayi tana duba wayar cikin tsananin mamaki take kallon lokacin , karfe bakwai har da mintuna, a zabure ta mike tayi saurin fadawa bandaki ta dauro alwala tazo ta gabatar da sallah tana rokon Allah gafara akan makarar da tayi.
  Bayan ya idar ta zauna a wajen tana tunanin abinda Farouk yayi mata na regecting kiran ta da ya dinga yi, a takaice dai yayi fushi, fushin da bashi da dalili ko tushe.
  Tashi tayi ba tare da ta cire hijabin jikinta ba ta koma daki ta tashi Baba Altine, zaman dirshan tayi a kasan dakin bayan Baban ta fita ta shiga azkar a nutse, tana cikin yi ne Kamal ya fado mata, jiya ta kirashi babu amsa duk sai taji babu dadi hankalin ta kuma ya gaza kwanciya, be taba tafiya hakan ba ba tare da sallama ba, sannan yanayin daya fita a ranar ya tsaya mata a rai sai dai ta kasa gane dalili ko hujjar da ya sashi aikata hakan.
   Gefen gado ta koma ta haye ta kudundune a cikin Hijabin ta shiga kiran layin nasa tana fatan ya daga duk da dai tasan safiya ce. Babu amsa dole ta hakura ta ajiye wayar ta rufe idon ta.

Bata tashi ba sai wajen goma, lokacin Baba Altine ta gama gyaran gidan har ta siyo kokon ta da ya zama mata kamar al’adah tasha abinda. Wanka ta fara yi ta shirya a cikin wata doguwar rigar atamfa koriya wadda Anas yayi mata da sallah sannan ta wuce kitchen ta hado tea da biscuit ta zauna tana ci.

“Kwana biyu Kamalu shiru nace, lafiya kuwa?”

“Wallahi nima abinda ke raina kenan, shirin yayi yawa gashi na kikkirashi baya dagawa.”

“Toh, Allah sa lafiya, ki kara gwadawa Allah sa ba kuma sace wayar akayi ba.”

“Toh Amin dai, bari na sake kira.”

Ta danna kiran tana ajiye cup din hannun ta.

Lokacin wayar na hannun Ammi suna zaune da wasu mata kiran ya shigo, sunan data gani yasa ta jan tsaki ta mike ta dan matsa gefe kafin ta daga

“Ya daga.” Tace wa Baba Altine

“Kamal. Ina ka shige kwana nawa ina ta kiran ka, wallahi baka ji yadda muka damu ba.”

“Toh munafuka, kin tura min yaro in da zai halaka ba ki masan matsalar da kika saka shi ba ko? Na tabbata abinda ya kaishi Katsina ya gamu da wannan mugun abun ya na da alaƙa dake, tun da kika shigo rayuwar sa shikenan ya chanja, komai ke komai ke, sai ki zuba ruwa kisha tun da kin kassara masa rayuwa.” Ta karashe tana share kwallar data zubo mata

“Dan Allah kiyi hakuri, me ya samu Kamal din? Wallahi bani da masaniya.”

“Karki sake kiran sa, baya bukatar ki mu iyayen shi kadai mun ishe shi,ki fita daga rayuwar sa ba zan juri rasa shi ba zan kuma iya yin komai akai.”

Tana kaiwa ta katse kiran tana komawa wajen zaman ta kamar babu abinda ya faru.
Kuka Aminatu tasa tana fada wa Baba Altine abinda ya faru, duk ta rude idan wani abu ya faru da Kamal ba zata taba yafe wa kanta ba, me ya kaishi Katsina bayan tasan bashi da wani abu da zai kaishi chan din tunda ya taba fada mata tun bayan barowar su Daddy basu sake komawa da sunan zama ba, dama aiki ne ya kai su garin, yan uwan su da sukayi saura basu da yawa a garin ba kuma ma zuwa wajen su suke ba.
Rasa inda zata sa kanta tayi, zaman ma sam ya gagare sai zagaye take,ita kenan duk wanda zai rabe ta sai ya shiga matsala, kamal ɗin da take ganin shi a matsayin dan uwa na jikinta shima ana neman illata masa rayuwa. Dole ta kyale shi kamar yadda mahaifiyar sa ta buƙata amma kuma tana son sanin halin da yake ciki gashi bata san wa zata tuntuba da maganar ba.

***Wanka yayi mata ya chanja mata sannan ya riko hannun ta suka fito falon, Dadah na zaune da anty Safiyya suna hira akan tafiyar da Anty Safiyyan zatayi Kaduna, miƙa hannu Dadah tayi da murnar ta, make kafada Iman din tayi tana buya a jikin baban ta.

“Zo kinji.” Tace tana sake gwadawa

“Barka da safiya Anty.”

“Barka Farouk, ashe anan ta kwana shine baka miko mana ita ba, ko da yake ba yarda zatayi ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button