DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yayi
“Ni dinma da kyar, zuwa zan na kaita na dawo sai mu wuce, Mummy na son gani na.”
“Sannu da gida Dadah.”
“Har yanzu fushin ne Baba na? Baka yarda dani ba ko?”
Shiru yayi yana gyara wa iman zama a jikin sa
“Komai yazo karshe in Sha Allah, dani zaku tafi ina so na sanar da kowa abinda baku sani ba, dama dazu baban naku ya kira akan Kamal ya gamu da hatsari yana asibiti ma toh kaga zuwa ya zama dole.”
“Subhanallah, accident yayi? Banji ba wallahi.”
“Wallahi wai mota ce ta buge shi a Katsina yana tafiya a kafa.”
“Ikon Allah, garin yaya? Allah ya bashi lafiya bari na maida ta sai na dawo.”
Yace yana tashi, da sauri ta mike tana sake riƙe shi.
“Ja’ira kamar za’a kama ta.”
Sukayi dariya gaba daya.
***Da gudu ta bude motar ta shige gidan tana kwala kiran Ummi, da sauri ta goge kukan da take ta fito ran ta fari kal ta rungume yar ta ta cikin wani irin yanayi
“Ummi nah.”
“Umm.”
“Ina ta neman ki, har kuka nayi.”
“Toh gani ai, no more kuka ko?”
Tace tana shafa kanta cikin tsantsar kauna. Hannu ya harde yana kallon su, ji yake kamar ya je garesu ya haɗa su ya rungume su, dagowa tayi ya kanne mata ido daya yana murmushi. Sai ta turo baki tana tashi daga durkusan da tayi.
“Muje ciki.” Tace tana rike hannun Iman din. Shigewa sukayi suka bar shi a tsaye, ƙasaitaccen murmushi yayi ya bi bayan su.
Kai tsaye daki suka shiga ta kwantar da ita saman gadon tana zame mata riga, ita kuma tana mata surutai. Budo kofar yayi ya shigo ta dago tayi masa kallo ɗaya ta dauke kanta, ya lura da yadda take share shi duk haushin jiya ne, matsowa yayi har cikin tsakiyar dakin yana karewa ko ina kallo kafin ya sauke idon sa akan kayan ta na lawyers dake ajiye a gefe guda, takawa yayi har wajen ya dauka yana jin sabon nishadi na ziyartar sa.
“Barrister AFS ( Aminatu Farouk Shagari).” Ya furta cikin wani irin shauk’i. Bata kula shi ba ta sauya wa Iman kaya zuwa marasa nauyi ta rike hannun ta suka bar dakin, zaman sa yayi yana sake duba kayan karatun ta yana jin dadi mara misaltuwa.
Wajen Baba Altine ta kaita bayan taje ta rufe gidan da sakata sannan ta komo dakin da niyyar daukar wayar ta.
Ta gaban sa ta wuce ta dauki wayar zata bar dakin yasa mata kafa kadan tayi lu zata fadi yasa hannu ya taro ta, ido ta zaro a tsorace tana kallon sa numfashin sa na yawo a saman fuskar ta. Kici kicin kwacewa ta hau yi ya rik’e ta gam yana sake saka idon sa sosai a cikin nasa domin ya gane irin tasirin da hakan ke dashi..
“Ka kyale ni.” Tace tana sake yunkura wa tana kokarin dole sai ta kwace.
“Wai karfi kika fini? Karki manta da soja kike magana, just keep calm babu abinda zan miki.”
Juyar da kanta tayi gefe ya sa hannu ya juyo da fuskar yana cije baki kadan kadan
“Fushin ne?”
Sshiru tayi masa
“I’m very sorry, bansan me ya hau kaina bane, bana iya controlling kaina duk sanda na ganshi kusa dake. Nasan yayi min halaccin kula min daku kuma in Sha Allah zanyi kokarin controlling kaina kinji?”
Bata tanka ba.
“Say something.”
“Ka daga ni be dace ba.” Tace tana hadiye yawu da kyar, murmushi yayi yana sake dora mata nauyin sa sosai
“Babu rashin dacewa dan miji ya kebe da matar sa, zan tabbatar miki da bani da hannu akan wannan takardar bogin da aka kawo miki, ban saki matata ba saboda haka babu wanda ya isa ya hanani kebewa da ita, kinsan yadda nayi kewar ki kuwa?”
“It’s still doesn’t change anything, please ka kyale ni.”
Kura mata ido yayi cikin kankan da murya, ya sa hannu a saman fuskar ta yana bin ko ina kafin yace
“Ba zan taba iya kyale ki ba, ko da ace saki nayi miki ai na uku bane ko? Balle wallahi ban sake ki ba, kuma zan tabbatar miki da haka.”
Shiru tayi cikin rashin sanin me zata yi, bata so ta yarda dashi ya zurma ta ta riga tasan hukuncin hakan, motsawa tayi da dan karfi bakin ta ya hadu waje guda nasa, da sauri irin na wanda yake a matuƙar buƙace ya shiga kokarin ganin ya fanshe abinda yake ji game da ita.
Sai daya dau lokaci me tsawo yana aika mata da sakon da yake isa kowanne lungu da sako na zuciya da gangar jikin ta. Bata iya hana shi ba sai ma sakin jikin ta da tayi sosai tana karbar sakon nasa.
“Ummi.” Muryar Iman ta dawo dasu daga dogon zangon da suka tafi, da sauri ta ture shi tana sakin kuka, kallon ta yayi ya zura mata ido yana jin ransa fes, kukan me kuma zatayi bayan da gaske tayi enjoying abinda ya faru.
“Ki share hawayen ki kafin ta shigo ta ganki kina kuka, ta zarge ni.”
Harara ta balla masa tana goge fuskar ta daidai lokacin Iman ta shigo.
Mik’ewa yayi yana zura hannun sa cikin dogon wandon sa,
“Zanyi tafiya zuwa Abuja, zan dawo gobe ko jibi, daga nan zanzo da kowanne hukunci dake tattare da auren mu.”
“Ya jikin Kamal?” Tace tana kallon sa
“Alhamdulillah duk da bansan ya ake ciki ba…” Wayar sa ce tayi kara ya zaro ta yana dubawa
“Barka da warhaka Daddy.”
“Barka dai, ya gida?”
“Lafiya lou, ashe kamal be ji dadi ba, Allah ya kara sauki yanzu zamu tawo in Sha Allah.”
“Alhamdulillah WallAhi, tsautsayi ya hadu dashi, gashi ya dage da son ganin Aminatu, idan babu damuwa kazo da ita dan Allah, bamu san me yake son fad’a mata ba.”
“Babu damuwa, zamu zo tare in Sha Allah.”
Ajiye wayar yayi
“Ki shirya baban Kamal ne ya roki alfarmar muzo tare wai Kamal din nason ganin ki.”
Dan jim tayi tana tuno warning ɗin maman shi, sai kuma ta tuna tana bukatar ganin shi sosai, gida mishi kai tayi alamar toh
***Kuka ta kwana tana risga cikeda nadamar abinda ta aikata, ganin danta yasa komai ya dawo mata sabo, bata kyauta wa Aminatu ba, bata kyauta ba ta zama daga cikin mutane masu son kansu, da tayi hakuri da duk yanzu babu abinda ya faru, tsantsar kiyayyar data gani a idon sa kadai ya ishe ta gane a wanne bigire a ajiye ta azuciyar sa.
Dauki da ledar magani Nura ya shigo ya zauna gefen tabarmar dake ajiye a wajen yana duban ta
“Kiyi hakuri Inna, ina kyautata zaton zai sake dawowa.”
“Tunanin da kake kenan? Ka kuwa duba banbance banbancen dake tsakanin mu? Kalle mu cikin tsantsar talauci da kauyanci, ka tuna yadda jikin sa yake da ke fitar da tsantsar hutu da jin dadi, me zaiyi dani? Bayan ban zame mishi uwa ta gari ba.”
“Duk wannan daban, kasancewar ki mahaifiyar sa ya kore komai.”
“Nura kenan.”
“Dan Allah Inno mu bar maganar nan haka, karbi ga magungunan nan kisha kin daiji shafi’u me chemis yace jinin ki ya hau sosai, ki sha sai ki kwanta ki huta dan Allah.”
Bata sake magana ba ta karbi maganin ta balla tasha ta koma ta kwanta kanta kamar zai rabe biyu saboda azabar ciwon da yake mata.
***Tun daya koma office ya kasa aiwatar da komai, baki daya ya rasa gane inda dai ajiye alakar shi da Aminatu, da kuma billowar Farouk a lokacin da bai dace ba. Ba yaro bane shi dan a ƙalla ya doshi shekaru talatin da biyar, yana bukatar mace a kusa dashi, dan haka ya zama dole ya tuntube ta yaji matsayar sa dan bazai yiwu su dinga yi masa wasa da hankali ba.
Lambar ta ya lalubo zai kira sai kuma ya fasa ya ajiye yana sake gyara zaman sa sosai, gwara kawai ya bari weekend yaje face to face ayi magana yasan matsayar sa.
Wulakancin da Farouk yayi masa ya kasa barin ransa, a takaice dai ba’a taba masa abinda ya tsaya masa haka ba irin na Farouk din, ko dan dama tun asali ba wani shiri suke ba oho.
Kiran Hajiyar sa ne ya shigo masa, ya daga da sauri don wanna zuwan da yayi be samu ya leka su ba bacin ran Farouk yasa ya dawo ba tare da ya shirya ba.