DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Barka da safiya Hajiya.” Yace cike girmamawa
“Barka dai, ya aikin?”
“Alhamdulillah babu dadi.”
“Haka ne dama sai hakuri, Allah ya bada sa’a.”
“Amin.”
“Na zata zaka shigo wannan satin ina ta jiran ka dan akwai muhimmiyar maganar da zamuyi sai kuma naji shiru.”
Sosa kansa yayi
“Abubuwan ne suka sha kaina, satin nan zan shigo in Sha Allah.”
Ya samu kansa da boye mata zuwan da yayi wanchan karon.
“Shikenan sai kazo.”
Shafa kansa ya dinga yi yana nazarin dalilin kiran mahaifiyar sa, ya santa sarai bata wasa da al’amuran da suka shafe shi, last zuwa da yayi sai data yi masa korafin maganar Aminatun
Wayar da take tayi saurin katsewa saboda shigowar Daddyn da bata yi tunanin a lokacin zai shigo ba.
“Sannu da zuwa.” Tace cikin rashin gaskiya, be fuskanci komai ba ya amsa mata a sake yana wucewa dakin sa, dazu da suka tsaya a Kaduna ya hangi Mummy a motar ta, gaba daya sai yaji ya gaza sukuni da ransa, ya rasa dalilin da har yanzu ya kasa mancewa da ita a zuciyar sa, gashi ta kafe sosai ta hanashi rabar ta balle har ya samu nasarar shawo kanta.
Turo kofar tayi dauke da tray din abincin sa, ta ajiye gami da dora wayar ta saman mirror kafin ta juya ta fita. Kallon abincin yayi sam bashi da appetite ya matsar dashi gefe ya saka abin sallah ya gabatar da sallar da ta tsere masa. Yana sallar ta leko ta koma ta cigaba da wasu aikace aikacen
Yana zaune yana addu’oin sa wayar ta dake ta faman kuka ta ishe shi, dan buɗe murya yayi da nufin kiran ta shiru sai kawai ya yanke hukuncin dagawa ba tare da tunanin komai ba. Wanda ya kira ya soma magana kai tsaye ba tare da tunanin tsayawa ya saurari wanda ya daga kiran ba
“Zan shigo gobe da safe, zanzo kamar yadda na saba zuwa a matsayin Ibrahim, ina so na tabbatar na katse numfashin Kamal kafin ya farfaɗo ya sanar da MD wacece asalin yar tashi, ba yanzu nake bukatar ya sani ba har sai na tabbatar da duk dukiyar sa ta dawo hannu na.”
“Kina jina?”
Yace bayan ya gama maganar, tsaki yaja kadan ya katse kiran yana tunanin network ne
“Adam.” Daddy ya furta da karfi
Tsawon wannan lokaci dama shine yake raina masa wayo yana takowa har cikin gidan sa bisa amincewar matar sa? sanin cewa wanda ya riga ya mutu baya dawowa yasa be taba kawo komai ba, ya yarda dashi fiye da yadda ya yarda da kowa har ya amince da tayin auren Maman da yayi masa kai tsaye babu ko dogon bincike, ashe??? Ya zama dole ya shigo hannun sa a goben nan, ba zai taba bari damar ta kubce masa ba. A gaggauce ya rubuta masa text message da wayar Maman sannan yayi saurin gogewa yana ajiye wayar a mazaunin ta.
Rano ????????DG
39
©Hafsat Rano
★★★★
Da sauri ya jawo wayar sa ya kira MD, yana dagawa be jira komai ba yace
“Zaman Kamal a asibtin nan akwai hatsari, zan iso asibitin yanzu, kafin zuwa na a tabbata babu wanda ya shiga in da yake.”
“Shikenan sai kazo.”
Ya ajiye wayar, duba lokcin yayi dare ya soma yi ya fito.
“Lafiya Alhaji?” Ta tsare shi cikin kulawa
“Eh babu komai, wani aiki ne ya taso da yake bukatar fitar tawa.”
Yayi gaba dan ko fuskar ta baya son gani.
Yana isa asibitin ya ja MD gefe ya sanar masa da abinda yake faruwa, hankalin sa ya tashi, dole suka tuntubi likita a aka basu sallama a take sannan ya haɗa su da wanda zai kula da Kamal din kafin yazo da safe.
Dukkan su babu wanda be yi mamakin dalilin da yasa za’a dauke Kamal, haka suka nufi gidan kowa da tunanin sa, matakan tsaro sosai aka kara a kowanne gida sannan Daddy ya samu ya kwanta da tunanin abinda gobe zata haifar.
Komawa yayi ya haye gadon ya mike kafa,
“Ku shirya mu wuce toh, amma ya za’a yi da Baba?”
Daga kanta tayi cikin nazari kafin tace
“Ko taje gida?”
“Ummm anya? Why not taje gidan Dadah, idan yaso sai suyi zaman su da mai aikin ta har mu dawo.”
“Ok bari na fada mata.” Tace
Rakata yayi da ido yana lumshe su kamar na wanda ya sha wani abun, sarai ta ganshi sai ta basar dan ita yanzu ya soma bata tsoro. Jim kadan ta dawo ta sauko da yar karamar trolly dinta ta jera musu kayan su ita da Iman da duk abinda tasan zasu bukata.
Juyowa tayi tana kallon sa, so take ta chanja kayan jikin ta sai dai ganin yadda ya kafa ya tsare yasa ta fasa ta zaro hijabi ta ɗora a saman doguwar riga, dama chan Iman a shirye take.
“Na gama.” Tace tana kallon sa
“Kin fasa chanja kayan jikin naki?”
“Ni nace zan chanja kaya?”
“Na gane ai.” Yace yana mik’ewa
“Oya baby muje ko?” Ya riko Iman din
“Ina?” Ta kalli mahaifiyar ta da sauri tana matsawa kusa da ita
“Ummi ina zamu?” Tace tana kallon jakar dake ajiye
“Unguwa zamu, kije wajen sa Daddyn ki ne babu abinda zai miki kinji”
“Har dake?” Tace tana sake matsawa kusa da ita
“Har dani.”
Murna tayi ta kama hannun sa
“Muje uncle.”
Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, yana bukatar lokaci da zai shaku da yar sa, sai a yanzu yayi dana sanin barin garin da yayi. Kada kansa yayi yaja jakar tare da kama hannun ta suka fita.
“Nace ba, ko zaki kira Anas ki sanar masa kar yazo bama nan?”
Baba Altine tace tana daukar yan kayan ta
“Ok zan kira shi.”
Tace sannan suka rufe gidan.
Kai tsaye gidan Dadah suka nufa, Iman ce a gaba sai Baba Altine da Aminatu a baya, suna zuwa suka tarar dasu shirye, da murna Dadah ta tarbe ta ta rungume ta cike da jin dadin ganin ta. Bayanin komai Farouk yayi mata sannan suka fito. Babbar mota ce me kujeru biyu a baya saboda haka basu wani takura ba, Uncle Aliiyu da Farouk ne a gaba, sai Anty Safiyya, Dadah, Aminatu da Amal a baya sai yaran Anty Safiyyan guda uku.’ da Iman
Hira suke tsakanin Dadah da Anty Safiyya, sai Farouk da uncle Aliyu dake tasu a gaba wadda ta shafi siyasar kasar mu ta gado.
Aminatu da Amal kamar basa motar babu wanda ya bude baki yayi magana duk da kuwa suna manne kusa da juna. Ta gefen ido Amal ke satar kallon Aminatun tana jin wani iri game da ita, tunanin yadda za’a kwashe da maganar auren ta da Farouk da take ganin ya kamata ace akwai mafita a ciki, gashi babu wanda ya kuma daga zancen a cikin su Daddyn sunyi biris kamar basu san da auren ba, gashi ita ba wani take kulawa ba kuma ita sam bata ma yarda da aka ce wai Mummy ta shayar da ita ba, idan har haka ne ba zata yafe wa Mummy ba dan ta cuce ta iya cuta.
Daddy be iya bacci ba, jira yayi ta yi gari ya waye kar ma yazo ko yana bacci. Kiran farko a kunnen sa ya yunkura da kyar ya fada toilet ya daura alwala ya fara gabatar da raka’atanil fajr kafin ya wuce masallacin dake kan layin su dan gabatar da sallah.
Bayan an idar ya dawo gidan, jami’an tsaron dake tsaye a gate gidan ya tattara waje daya ya sanar dasu abin da yake so suyi masa, sun amsa da toh kafin ya koma ciki ya hau shiri dan yana ji a ransa yau komai zai waka na.
Wajajen takwas na safe ya fito harabar gidan ya samu kasan rumfar da ya saba zama musamman da yammaci ya zauna, sannan ya aika aka karbo masa breakfast din sa a wajen.
Tun yana zaune yana duban lokaci har rana ta soma dagawa da tasa dole ya koma ciki yana tunanin abinda ya katse shi da zuwa bayan yayi masa reply a matsayin Maman ce.
Yammaci ne me cike da ni’ima, sake fitowa Daddy yayi ya zauna yana kallon ko ina a harabar gidan komai na sake dawo masa kamar a lokacin yake faruwa. Idan bai manta ba, a irin wannan lokacin ya same shi, cikin kankan da murya ya shigar da kansa, be san ya akayi ba,be san me ya faru ba, kawai ya samu kansa da amince masa kai tsaye, ya sakar masa ragamar komai na harkokin sa, a halin yanzu shine yake juya alakar dukiyar sa mafi yawa. Dan karamin tsaki yaja ya shiga shafa kansa, tabbas idan ka biye ma zuciya zata kai ka ta baro ka, gashi shima ya biye wa tasa, ba tare da dogon bincike ba ya afka ga tarkon da yake tunanin fitar sa akwai kalubale babba.
A daidai lokacin motar su ta kunno kai, duk a gajiye suke saboda tafiyar musamman Aminatu da ba sabawa tayi ba, yaran sunyi bacci yafi sau nawa suna farkawa.
Da kallo ya shiga bin motar har suka samu waje sukayi parking, Ido ya zura sosai ganin da gaske Dadan ce yasa ya mike da sauri cikin mamaki yace