DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dadah.”
Fitowa tayi tana kallon gidan, karo na biyu bayan lokacin ta sake dawowa.
“Barka da zuwa Dadah, ashe kina tafe.”
Yace yana bayyana farin cikin sa a waje,
“Barka dai, ya jikin Kamal din?”
“Alhamdulillah.”
Hannu ya mika wa uncle Aliyu sannan su Aminatu suka gaishe shi kafin su dunguma zuwa ciki. Duk Aminatu a darare take ta kasa sakin jikin ta, kai tsaye Amal ta wuce dakin ta dan dama a gajiye take da zama waje daya da su.
Farin cikin Mama ya kasa boyuwa, dama haka take chan kirkin masifa ne da ita, haka ta shiga hidima dasu kamar zata goya su, a take ta saka umarnin a gyara tsohon bangaren Dadah daya ke a rufe.
Dakin Amal maman ta nuna wa Aminatun. Dago kai tayi jin an bude kofar, ganin wace yasa ta maida kanta ta cigaba da abinda take, gefe Aminatu ta samu ta zauna tana tunanin yadda zama zai yiwu ita da Amal a daki daya.
Tana nan zaune har aka kira sallah, kofar dake nuna toilet dake manne a dakin ta nufa, murya a shake Amal tace
“Bana sharing toilet da kowanne trash.”
Juyowa tayi da sauri ta tsaya tana mata kallon mamaki
“Amal nice trash?”
“Mu nawa ne a dakin?”
“Ok nagode.” Tace sannan ta bude toilet din ta shiga, hakan ya bata wa Amal rai ta tashi tana fadan maganganu, tana jin ta sarai har ta dauro alwala ta fito, bata kula ta ba ta tada sallah a kan dankwalin ta.
Tana zaune tana addu’a Mama ta leko
“Kin idar? Taso zaku shiga chan gidan.”
“Owk tom.” Ta mike
“Dota kema ki taso.”
“Zan je gobe kaina ke ciwo.”
“Ayya sannu, gajiya ce kisha magani.”
Fita tayi Aminatu ta tashi ta nufi kofar fita, har ta kama kofar sai kuma ta tsaya tana juyowa
“Wai ke bak’ya sallah ne?”
Waro ido Amal tayi, kafin tayi magana ta yi ficewar ta.
Tsananin faduwar gaba ne ya ziyarce ta sanda suke shiga cikin gidan, haske ne ko ina kamar rana, haka ya bata damar karewa tsarin gidan kallo da yafi kama da irin wanda ake gani a Film.
Dukkan sautin sahun digadigan ta na fita ne tare da tsanantar bugun zuciyar ta, idan tace tasan musabbabin da yasa take jin hakan tayi karya, haka nan take ji kamar ta zura da gudu saboda tsabar zulumi
Haka suka shiga wuce bangare bangare na tafkeken gidan a kasan zuciyar ta tana tuna yadda suka saba da Kamal bata taba tunanin girma da yawan dukiyar su ta kai haka ba sai yanzu.
Babban falo ne daya kawatu da kayan more rayuwa, a hankali bakin ta dauke da sallama ta shiga takawa tana bin bayan su Dadah hannun ta damke dana iman.
Ammi na zaune, tallafe da kumatun ta bayan ta sha kuka, zuwan Dr Ahmad yasa ta fitowa daga ciki ta zauna a falon tana dakon fitowar su da labarin halin da gudan d’an nata yake ciki.
Zamewa tayi da sauri ganin su ta mike tana sakaya yanayin da take ciki ta maye gurbin sa da yar fara’a.
“Dadah!”
“Sannu kinji.”
“Bismillah.”
Ta nuna musu wajen zama, kamar munafuka haka Aminatu ta rabe a bayan Anty Safiyya, sam Ammin bata lura da ita ba, suka shiga gaisawa. A darare Aminatu tace
“Ina wuni?”
“Lafiya…” Maganar ta makale a makoshin ta, wani irin abu taji ya bige ta, ta kura mata ido sosai tana kallon ta, tsoro ne ya kama Aminatu ganin yadda matar take kallon ta, gashi daga ganin matar taji kamar ta taba ganin ta, kamar ta tashi ta isa gareta ta zauna kusa da ita.
“Wacece?” Ta tambaya still idon ta na kanta
“Oh wai Aminatu, matar babana ce ga diyar ta nan ma Iman, itace ai wadda Kamal din ke son gani.”
“Aminatu…” Ta maimaita sunan
Sai ta bata rai ta nuna ta da hannu
“Kece ki ka samun rayuwar yaro a matsala ko? Kece mukayi waya nayi miki kashedin fita daga rayuwar sa, me kuma kika zo yi nan?”
“Me ya faru ne?” Dadah tace
“Gata nan tafi kowa sanin halin da take ciki da dalilin da yasa ya shiga, idan ba haka ba me yasa dukkannin farkawar da zai yi da sunan ta a bakin sa, me kikayi masa haka?”
“Haba Hajiya, ba haka bane Aminatu ba irin mutanen nan bace, kila baki fahimce ta ba.”
“Haka ne ma, komai a bayyane yake yadda ya damu da al’amarin ta ko ni be damu dani.”
“Kiyi hakuri.” Tace cikin muryar kuka, hadiye abu Ammin tayi da ya tokare mata makoshi tace
“Please kije i can take care of him, an gode da dubiya.”
“Haba Hajiya, haba Hajiya, bansan ki da son kai ba, karki manta ita ma mutum ce da iyayen ta, idan kika yi haka kamar baki yarda da ƙaddara ba.”
“Kiyi hakuri Dadah na gama magana.”
Tace tana kauda kanta gefe cikin son danne abinda yake taso mata kasan zuciyar ta, yadda take jin yarinyar a ranta ya sata cikin wani irin yanayi mara dadi.
Mik’ewa Aminatu tayi, ta rike hannun Iman,ta soma takawa ta nufi kofa, ta kasa boye kukan ta saboda haka sai ta sake shi kawai, ita kenan kowa baya son ta kowa kyamatar ta yake, idan ba haka ba menene laifin ta.
“Ummi ki daina kuka kinji?”
Iman ta fada tana son fara kukan, tashi su Dadan sukayi, suka mata sallama suka bi bayan Aminatun cikin rashin jin dadin abinda Ammin tayi.
Dr Ahmad ne ya leko yana duban Ammin da take jin kamar bata kyauta ba sai dai ta kasa yarda da hakan,
“Hajiya yaron ku ya farka…”
“Alhamdulillah.” Tace cike da farin ciki
“Yana bukatar ganin ki, mahaifin sa sai kuma Aminatu, idan tana kusa ki kirata please.”
“Aminatu!”
“Eh haka yace, dan yafi damuwa da ganin nata ma akan kowa, ko dan lafiyar sa ki kirata please.”
Ya juya ciki, kanta ne ya hau juyawa, yanzu ya zatayi kenan? Da kunya ai ta koma tace suzo kuma, sai ta basar ta shiga ciki.
Yana kwance idon sa a bude fes, da sauri ta karasa tayi saurin kama hannun sa.
“Allah na gode maka.”
“Ya jikin naka? Me yake maka ciwo yanzu?”
“Ammi ina Aminatun? Dan Allah ki ce tazo.”
“Kamal wai menene ka damu da sai tazo? Baka murnar gani na sai ita?”
“Inayi Ammi, sai dai…”
“Bana son maganar ta Kamal, ka bari ka sake samun lafiya sai kaje ka ganta.”
Yake yayi ganin yadda ta dage, a hankali ya dora hannun sa a saman nata, ya kalli Alhaji Marwan dake tsaye bayan su ya harde hannun sa tun bayan shigowar Ammin yana duban su, baya so ya sa musu baki shiyasa yaki magana.
“Tabbas kinfi kowa bukatar maganar ta Ammi, saboda kinfi kowa chanchanta da hakan, ƙaddara ce ta haɗa ni da ita, haka ma ƙaddara ce ta kaini Katsina har na shiga cikin wannan halin, babu sanin ta ko izinin ta kamar yadda kike tunani, komai da ya faru tsarin Allah ne, idan ka duba yadda ya kasance. Dan Allah a tura tazo idan har tana nan, bana so nace komai sai a gabanta.”
“Bari na kira ta son, sun iso yanzu ta bar falon nan bisa korar da mahaifiyar ka tayi mata.”
Sai ya ciro wayar sa ya shiga neman layin Farouk, yana zaune a dakin sa tun zuwan su, gefe jakar akwatin Aminatun ce daya ajiye a wajen sa, yana shirya wani kuduri a ransa.
Shigowar kiran ya katse masa tunanin da yake
“Ina gida, ok tom gamu nan.”
Rigar sa daya rataye ya jawo ya saka ya fito, ganin part din Dadah a kunne da haske yasa ya nufi chan, sallama yayi ya tura kofar, duk sun zagaye Aminatun dake ta faman kuka suna bata baki, da sauri ya isa ciki yana neman ba’a si
“Me ya faru?”
“Matsala suka dan samu da Maman Kamal, kamar tana zargin ta da jefa Kamal din cikin halin da yake ciki.”
Anty Safiyya ta amsa masa tana matsawa gefe
“Zancen banza kenan, akan me? Dan kawai ya taimaka mata sai kuma cin mutunci ya shigo? I can’t tolerate cin mutunci daga kowa.”