DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Hira sosai Amal ta shiga yi mata, kallon ta kawai take yi ba tare da ta gane komai ba, ido kawai tasa mata.

“Zan sha ruwa.” Ta furta a hankali, da sauri Amal ta tashi ta dauko mata ruwan, kokarin tashi tayi taji zafi, kuka ta saka yayi saurin tasowa,

“Sannu.”

Daga masa kai tayi tana gogen hawayen da bayan idon ta. Ruwan ya bata Amal na tsaye kamar zatayi kuka.

“Gida zan tafi.” Tace tana kallon sa.

Zaiyi magana aka turo kofar, wani irin faduwa gaban sa yayi yasa hannu ya rike wajen zuciyar sa da sauri.

“Daddy!”

Amal ta fad’a tayi wajen sa da sauri, rike ta yayi ya matsar da ita gefe bayan ya shafa kanta, Maigari ne ya fara shigowa,sai Baba, Inno na bin bayan sa, sai Lawan Da Yahya. Garbati da Ilu suna take musu baya. Da sauri Inno tayi wajen gadon tana sakin kuka.

Gyaran murya maigari yayi, Inno tayi shiru duk aka nutsu ana kallon sa.

“Garbah!” Ya kira sunan Garbati yana masa alamun ya matso.

“Maimaita abinda kace.”

Gyara tsaiwar sa yayi cikin dakiya ya nuna Farouk da hannun sa

“Gashi nan, jiya ana ruwan nan ta gefen daki na naji kamar ana kuka, da har na share sai na kuma jin kukan na tsananta, kamar wasa na dauko toci ta na leko, in haska sai ga tashin hankali, ido na cikin nasa yana aikatawa karamar yarinya, nayi kukan kura na rike shi, muka haure da kokawa, shine fa ya samu yayi min mugun duka, kuma ya dauke ta ya gudu, duk da haka sai dana bisu a baya, naga gidan daya shigar da ita, shine fa nayi gaggawar zuwa sanar da iyayen yarinyar.”

Tun da ya fara magana Farouk ke  kallon sa, gaba daya jijiyar kansa ta fito, numfashin sa ya shiga fita da sauri da sauri, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, Daddy kuwa kasa yayi da kansa yana jin kamar kasa ta zage ya shige, sai dai bashi da ta cewa, duk abinda gaskiya ta bayyana zai goyi bayan ta, ba zai taba goyon bayan zalunci ba ko da daga dan cikin sa ne.

“Kaji abinda ake tuhumar ka dashi, shin kana da abinda zaka kare kanka, duk da dai ga zahirin ganin ku tare da mukayi anan, amma ko zaka fada mana dalilin da ya jawo hakan.”

Maigari ya fada yana duban shi, kokarin magana yake ya kasa, motsa bakin sa yake ya kasa, kallon Garbati kawai yake cikin tsananin bacin rai, bai taba tunanin akwai mutane masu aiki irin na dabbobi kamar shi din ba, kallon Amal yayi yaga ta zuba masa ido kamar me son ganin wani abu, ya sake maida kansa wajen Aminatu, itama shi take kallo, tana share kwallar dake zubo mata. Runtse idon sa yayi ya bude ya maida kallon sa wajen Daddy, yanayin daya ga fuskar sa kawai ta gamsar dashi abin da zai je yazo idan har ya kasa fitar da kanshi daga wannan daurin. Kokarin daidai ta kansa yayi ya shiga kokarin magana a nutse duk kuwa da tarin tashin hankalin da yake ciki

“Allah ne…”

“Kai ne kayi mata Fyade ko ba kai bane!” Daddy ya fada cikin k’araji dan ya gaji so yake kawai ya amsa da a ah ko Eh.

“Daddy Wallahi tallahi Allah ne shaida ta…”

“Will you shut your mouth, amsar ka kawai nake so kai ne ka aikata mata Fyade ko kuwa?”

“Fyade!”

Dr Iman da shigowar ta kenan ta karbi kalmar, duk suka juyo suka kalle ta.

“I’m sorry to interrupt, kuna nufin dama yaron nan ba mijin ta bane, fyade yayi mata suka rufa min yace shi mijin ta ne?”

Da sauri Farouk ya kalle ta zuciyar sa na sake tsinkewa.

DAURIN GORO????????????????????

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????

2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863

GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????

09032345899

Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali????????????????????????????????????????????????????????
: DG 5

ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

©️Rano

     
                        (5)


Duk suka maida kallon sa gare ta, takowa tayi ciki tana kallon fuskar Farouk din.

“Me kike cewa Dr?” Daddy ya tambaya yana kallon fuskar Farouk din

“Nice likitar data karbi case din yarinyar, a yadda mukayi magana na zata matar sa ce, dan shi dinma ya nuna min hakan, duk da cewa akwai karancin shekarun ta da nashin ma kansa, sai dai ya amsa laifin sa kuma ya bada hakuri, amma kuma naji wata maganar daban duk da ba dani ake ba, amma ina da right na sani saboda matsayi na na likitar ta.”

“Babu wata matar shi, makaryaci fyade yayi mata kila ma sai daya sha ya bugu sosai sannan.”

Garbati ya fada yana huci. Kasa hakuri Farouk yayi ya kalle shi cikin konar rai

“Sharrin da zakayi min kenan, kasan nasan komai shine kake kokarin jona min laifin da ka aikata?”

“Ni? Ni zaka wa sharri, na ganka ido da ido, shine zaka maida abin kai na, na shiga uku, wallahi Maigari karya yake min so yake ya maida abin kaina.”

Sake duban sa Farouk yayi yace

“Kaji tsoron Allah, ka sani akwai mutuwa akwai hisabi, kar kaga idon mutane anan, ka fadi gaskiya ko dan rayuwar yarinya karama.”

“Wallahi tallahi sharri yake min, shine ya aikata karya yake min wallahi.” Garbati ya fada yana karashe wa da fashewa da kuka kamar gaske.

Dafa kai Daddy yayi ya kalli farouk, ya gaji da wasan yaran nan da suke musu, magana daya yake son ji, idan shi ya aikata ya amsa eh ko a’ah. Rike masa riga yayi cikin bacin rai

“I’m asking u for the last time, Kai ne ko ba kai ne ba?”

Kukan Amal da Aminatu ne ya kara karfi a wajen, juyawa Farouk yayi ya dube su daya bayan daya, sosai kukan nasu yake taba masa rai, kallon Daddy yayi ya shiga girgiza kai.

“Alhaji ina ganin tun da ga yarinyar nan a zaune, duk da karama ce amma ba zata kasa tantance wani abu ba, ina ganin a tambaye ta, idan yaso kowa ne ya aikata mata wannan abin, a cikin su, to fa dole ne a aura masa ita bayan hukuncin da shari’a ta gindaya ga wanda ya aikata irin wannan laifin, dan kaf kauyen nan namu babu wanda zai yarda ya karbi aurenta, musamman yanzu da zance ya zagaya ko ina, ina tsoron sai dai ta karasa rayuwar ta a haka.”

Maigari ya katse su, sakin sa Daddy yayi ya hankada shi har sai daya kusa bigewa da karfen gadon, dago idon sa yayi ya sauka cikin nata, wani irin abu yaji ya taba shi, wanda be taba jin irin sa ba, raunin da ya gani a cikin idon ta, yarintar ta da tsantsar tausayin ta suka hadu. Idan har yaji daidai abinda mai gari ya fada, yana nufin aura wa Garbati ita kenan, auren da yake nufin lalacewar rayuwarta har abadah, auren da yake nufin yanker war duk wani jin dadi na rayuwar ta, auren da yake nufin rayuwa da mutum wanda bashi da maraba da dabba, dabbar ma mafi kaskanci acikin dabbobi. Kasa dagowa yayi ya rasa me yake masa dad’i, yana jin sanda Maigari ya kira sunanta, yana jin lokacin da ya tambaye ta, kukan ta ya kara karfi, be san yaushe ba, be san yaya ba, kawai ya samu kansa da amsawa a maimakon ta tun kafin ta samu damar yin magana. Da wani irin karfi Daddy ya riko shi, ya shak’e shi, kakari ya fara kamar wanda yake shirin mutuwa cikin sauri Baba ya shiga tsakani. Yayi kokarin bangare shi daga rikon da yayi masa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button