DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Bata kyauta ba kam, na rasa kuma me ya sa ta hakan bayan ba halin ta bane.”

“Tashi.” Yace yana mika mata hannu, dagowa tayi ta kalli hannun kafin ta maida kanta kasa ta cigaba da kukan ta.
  Damko hannun nata yayi ya mikar da ita tsaye yana girgiza mata kai

“Karki sake kuka, kin bar kuka tun daga ranar dana dawo gare ki, wannan ya zama na karshe.”

“Me yasa kowa yake min haka?”

“Muje.” Yace yana nufar kofa da ita

“Me zakayi Farouk?”

“Alhaji Marwan ke kiran mu, yanzu zamu dawo.”

Yace yana fita da ita.


Shiru kawai Ammi tayi bata sake magana ba ta zauna tana matsawa Kamal din gefen kafadar sa.
Shigowar su yasa ta dakata, kallo daya tayi musu ta dauke kanta zuciyar ta babu dadi.
Fuskar Kamal ce ta washe sosai ganin ta, ya lura da yadda idon ta yayi, ya san kuma hakan na da nasaba da abinda Ammin tayi mata, duk da bai ji dadi ba amma yasan hakan baya daga cikin halayyar Ammin, be san me yasha kanta ba, har ta iya aikata abinda be yi tunani ba.

“Ammi, Daddy, Ya Farouk da Aminatu, ina so na sanar daku abinda ya kaini Katsina, da abinda yasa na takura da son ganin Aminatu da har ya jawo matsala tsakanin ta da Ammi.”

“Go ahead, karka ji komai kaji, muna sauraron ka.”

“Nagode Daddy.”

“Duk da bansan takamaimai alakar Adam da ku ba, bansan me kukayi masa ba da har yake bibiyar rayuwar ku, ya kuma yi abinda yafi komai muni, Ammi ki dubi Aminatu da kyau, kiyi mata kallo ba irin kallon da kikayi mata a yanzu ba, zaki gane abinda zan fada.”

“Daddy I’m sorry, I’m very sorry to say, ni din ba danku bane, baku kuka haife ni ba.”

“Kamal!!!!” Alhaji MD ya daka masa tsawa

“Me kake so kace? Kana da hankali ko ka tabu, waye ya gaya maka wannan banzan labarin?”

“Daddy ka yarda dani, bani da ikon boye muku gaskiya tun bayan dana san gaskiya, Daddy wallahi ni ba danku bane, Aminatu ita ce yarku, yar da kuka haifa da cikin ku, aka chanja muku ita, duk a bisa umarnin Adam.”

“Kamal me kake shirin cewa ne wai? Ban gane ba!”

“Ammi ki yarda dani, akwai kwararan hujjoji, komai na cikin waya ta nayi recording din sa, ina fatan idan kun gani zaku yarda dani.”

Juyawa dakin ya hau yi, daga Aminatu har Ammi babu wanda yake iya tantance komai, komai na dakin ya shiga rarrabe wa Aminatu, lu tayi zata fadi Farouk da maganar ta dake shi shima yayi saurin tare ta, lumshe idon ta tayi tana son tantance mafarki take ko kuwa gaskiya ne?

“Baka da hankali Kamal, ka haukace ko ƙwaƙwalwar ka ta tabu?”

“Idan kuka duba wayar still baku yarda ba ,daga nan zaku iya daukata a mahaukacin ma.”

“Bani wayar!” Ya karba a hannun Ammi da ta soma kuka ta kasa magana, hannun sa har rawa yake ya bude wayar ya shiga wajen, sautin muryar Kamal ɗin ce ta karade dakin cikin tattaunawar su da sister Asibi, zuwan sa Shagari, haduwar sa da Adam kafin accident din ya faru.
Da baya da baya Alhaji Marwan ya shiga ja har ya isa kujerar dake daura dashi ya fada yana dafe kansa.
Kuka sosai Ammi take, haka ma Kamal da Aminatu da bata masan a wanne matsayi zata ajiye abinda yake faruwa ba. Me ya kamata tayi yanzu? Me zata ce? Tsawon rayuwar ta tayi shi ne da tunanin ranar da zata hadu da iyayen ta, bata taɓa tunanin ta wannan yanayin zata hadu dasu ba, dukkan su kowa ya kasa motsawa daga in da yake, nauyi kunya da wani irin yanayi Ammin ke ciki, yarta! Yar cikin ta tayi wa abinda bata taɓa tunanin ko mai aikin gidan zata yiwa ba, ina tunanin ta ya tafi, ina hankalin ta, so take ta sake kallon ta, ta tabbatar da gaskiyar komai,amma ta kasa, ta gaza mik’ewa ta aiwatar da abinda yake cin ta.

Waje Farouk ya samu ya zaunar da ita ganin duk sun rikice ya isa gaban Kamal din ya dafa shi

“Me ya faru da har ya saka ka yin tafiyar?”

“File ɗin ta, file dinta dake dauke da sunan ta, Aminatu MD, sannan da passport din dake jiki na Ammi da Daddy, sai kuma labarin ta data taba bani, tabbas ba abu bane me sauki garemuba dukka, amma wannan shine gaskiya. Asibi, Adam, Inno kadai sun isa shaida, za’a iya neman su a tabbatar da haka.”

“Na yarda da kai.” Yace yana shafa kansa.

“Kira min mahaifin ku farouk, kira shi yazo nan na rasa yadda zan ɓullo wa al’amarin na.”

“Ok tam.”

Ya zaro wayar sa, ya kira Daddy.

“Daddy…”

“Ku taho nan Farouk, Adam na hannu yanzu haka, yana cikin gidan nan a dakin horo na, ka gaya wa MD kuzo yanzu, komai yazo karshe!”


Assalamu alaikum
Kuyi hakuri pls na shiga hidimar biki ne, kunsan yadda biki yake musamman idan aka ce naku ne..
Bikin best friend d’ina ne kuma zata auri dan uwa na. Ku sanya musu albarka da bakunan ku masu albarka Allah sa ayi a sa’a

Sai kuma ku shirya suburbudar Adam dan ni har na samu muciyar da zan sambade shi da ita.????????????
Shegen Goraa: DG

                       40

©Hafsat Rano

★★★★

“Bani shi.” Yace yana karbar wayar

“Ina ganin ko zaku zo nan ɗin saboda barin Kamal shi kadai anan ɗin matsala ne, idan yaso sai ayi komai nima akwai abinda ya shigo min yanzu haka, na ma rasa yadda zan.”

“Shikenan ina ganin mu bari zuwa gobe, bari nazo yanzu ni.”

Ya ajiye wayar yana nufar bangaren Dadah, yaji dadin zuwan da Adam ɗin yayi da daren dan hakan yayi masa sauki wajen kamashi.
   Kamar yadda suka saba ya shigo cikin gidan kai tsaye babu shamaki saboda matsayin sa na kanin matar gidan kuma sananne tsawon lokaci, Daddy na zaune a falo yana tunani yadda za’a yi ya turo kofar ya shigo, da murmushi ya tarbe shi kamar kowanne lokaci ya kuma bashi wajen zama yana tambayar shi kwana biyu. Bayan tattaunawa da sukayi kadan Daddyn ya tashi ya bashi wuri gami da kira Mama ta fito da mamakin zuwan nasa.
  Bangaren su Farouk ya nufa ya tura kofar, baya nan saboda haka ya dawo wajen securities din daya bawa umarni tun safe yace Ibrahim na fitowa su kama mashi shi, sannan ya koma ciki.


Kuka Aminatu take sosai wanda ta gaza boye shi, sam bata taba tunani ko kawowa a ranta wani abu makamancin haka zai ɓullo mata a irin wannan lokacin data cire rai da komai, mahaifiyar ta? Yau ita ce gaban ta cikin yanayin da ta gaza fuskanta yadda zata ajiye shi.
  Kadan kadan yake murza hannun ta cikin salon son rarrashin ta, sai dai ta gaza tsaida hawayen, idan da za’a fada mata cewa zata riski irin wannan ranar zata iya karyatawa, sai gashi ta risketa cikin yanayin da bata taba zato ko tsammani ba.
  Shigowar Daddyn ya tsaida komai, da sauri Alhaji Marwan ya tare shi da abinda ya ke faruwa, sosai maganar ta dake shi, ya tsorata ainun da lamarin Adam, ashe zai iya aikata haka garesu? Tabbas Adam yayi nisa cikin kiyayyar su, ya zama dole su ajiye duk wata alaƙa su hukunta shi hukunci me tsanani.

“Ina ganin dole a samu sauran mutanen da suka taimaka wajen bashi hadin kai, tabbas suna bukatar hukunci me tsanani.”

“Abinda nayi tunani kenan.”

“Dole gobe kowa ya zo, ya zama yana nan kuma ya zama dole Dadah ta fayyace wa kowa babban sirrin dake lullube a zuciyar ta.”

“Ina fatan ya zama abu mai sauki da zamu iya dauka.”

Alhaji Marwan yace yana kallon Aminatu da yake jin kamar ya dauke ta ya saka ta jikin sa, tun ranar daya fara ganin ta ya kasa tantance abinda yasa yaji wani iri game da ita, ashe jinin sa ne yake yawo a cikin jikin ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button