DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Lafiya?”

Idon sa da suka soma kadawa ya dago mata cikin dashewar murya yace

“Adam yana cikin gidan nan, za’a hadu da kowa karfe sha biyu na rana, ina rokon ki da ki sanar damu abinda kika sani idan an zauna.”

Da baya da baya ta koma ta zauna ba tare da tace komai ba. Girgiza kai kawai yayi ya maida duban sa wajen Anty Safiyya yace

“Safiyya.”

“Na’am yaya.”

“Dan Aallah ki kira Abidah kiyi convincing din ta tazo yau, idan ni na kira ta ba lallai tazo ba.”

“Toh Yaya.”

Ta tashi dauko wayar, duk da tana tsoron yadda zasu kwashe idan ta samu labarin tana garin amma bata nemo ta ba, Amma dole ta kira dan ba zata iya ce masa a ah ba.
    Kira tayi ta makala wayar a kunnen ta cike da fargaba

“Rage min volume din chan Ja’afar.”

Tace kafin ta daga tana gyara zaman ta,

“Hello Assalamu alaikum.” Ta ce kai tsaye,hawaye ne ya taru a idon Anty Safiyya ta kasa magana, sai data sake maimaita sallamar kafin tayi karfin halin furta

“Anty Abidah.”

A zabure ta mike shima Ja’afar sai ya mike

“Safiyya, Safiyya kece?”

“Nice.” Sai ta sa kuka

“Kina ina? Yaushe kika zo Nigeria, fada min yanzu zan taho innalillah.”

“Ina Abuja Anty gidan su Farouk, Please kizo Anty yanzu.”

“Wait what! Kina nufin chan Kika tafi? Dadi miji Safiyya,? Suwa ya kamata ki fara nema, tun yaushe ma kike garin kenan? Don’t tell me kin kwana biyu sai yanzu kike kirana.”

“Kiyi hakuri duk tambayoyin nan idan kika zo zan amsa miki, nidai dan Allah kizo.”

“Shikenan, zanzo na dauke ki right away, ba xaki sake zama achan ba kuma, gani nan zamu kamo hanya da Ja’afar yanzu.”

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace

“Allah ya kawo ku lafiya.”

“Amin.”

Juyawa tayi wajen Ja’afar ba tare da ta zauna ba tace

“Tashi Ja’afar, a dauko mota mu wuce Abuja, dole ta baro gidan nan yau yau.”

“Mummy wace haka?” Ya tambaya

“Zaka gani idan munje.”

“Owk.”


Maganganun Iman ne ya tashi Aminatu, tana buɗe idon ta abinda ya faru ya dawo mata, kallon dakin ta hau yi zuwa lokacin ta tuna a inda take, kan gadon mahaifiyar ta, sosai taji dadin baccin fiye da wani bacci da ta taɓa yi a rayuwar ta, glasses din ta ta dauka ta saka tana saukowa daga gadon.
  Budo kofar akayi, Ammi ce da Daddy cikin shigar alfarma, kowannen su bakin sa ya gaza rufuwa suka ƙaraso tsakiyar dakin suna duban ta, zamewa tayi da sauri zata sauka Ammi tayi gaggawar riko ta, a kunya ce tace

“Ina kwana Daddy?”

“Lafiya lou yar albarka, wannan amaryar tawa sai data tashe ki kenan.”

Dariya suka sa gaba daya, sannan ta gaida Ammi ma. Toilet ta shiga da yake tana fashin sallah, tayi wanka ta fito daure da sabon towel, a gefen gado taga wata haddiyar riga me masifar kyau, hade da sababbin underwears, murmushi tayi ta hau shirya wa cike da dauki.
  Ba karamin kyau kayan sukayi mata ba, ta jima gaban mudubi tana kallon kanta.
   Flat shoe ta zura sabo me kamar slipers ta yane kanta da dan siririn mayafi.
  Idon ta ne ya sarke da nasa sanda ta fito, yana hakimce akan kujera Iman na saman cinyar sa tana masa surutu, zuba mata ido yayi kamar zai lashe ta, tayi k’asa da kanta ta ƙaraso.

“Kinyi kyau sosai.”

Yace murya kasa, ta jishi sarai amma sai ta basar ta nemi waje daya ta zauna a hankali tace

“Ina kwana?”

“Lafiya lou princess, ko nace queen, dan yanzu kin zama kamar kwai nasan ni dan kallo zan zama.”

Murmushi tayi me aji, tabbas tana jin ta a yanzu ta kai ta isa gogawa da kowa, tunanin Shagari ya fado mata, lokacin komawar ta yayi.
   
“Ya kika ji? Kamar a film ko novel ko?”

“Ina jin kamar I’m the most happiest being on Earth, farin ciki na bazai misaltu ba ya Farouk.”

“Alhamdulillah ya Allah! Allah shine kadai abin godiya.”

“Haka ne.”

“Akwai meeting by 12, komai zai bayyana.”

“Allah ya kaimu.”

Tashi yayi yana makale hannun sa a baya, ya tako har inda take, sunkuyowa yayi daidai kunnen ta a hankali yace

“Get ready, patience dina ya soma karewa, i need u by my side.”

Turo baki tayi, yasa hannu a saman bakin.

“A adana su against next time, yanzu ina gidan surukai ne I have to behave.”

“Ya Farouk!!!” Tace tana rufe ido

“Me nayi?

“Ba komai.” Tace turo baki.

“Yarinya taji tsoro.”

Yace yana murmushi kafin ya juya ya bar falon. Lumshe idon ta tayi ta bude su, kiran Anas ya koma shigowa a karo na uku, jingina tayi sosai da kujerar kafin ta daga.

“Ni kike wulakantawa ?” Yace Muryar shi a shake

“Ba haka bne ya Anas, bana kusa da wayar ne.”

“Shikenan kince kina Abuja ko? Ki tura min address din zanzo.”

“Naa…am?”

“Sai kin turo.” Ya kashe.

“Ya akayi?” Ammi data fito daga wajen Kamal ta tambaye ta

“Wai Ya Anas ne yace na tura mishi address,bansan ya zan ba.”

“Tura masa mana dama ina son haduwa dashi, idan har aka tabbatar da babu aure tsakanin ki da Farouk toh fa baki da miji sai shi, dan ni yaron yayi min.”

Murmushi tayi, ta rubuta address din Ammin na fada mata, bata son jayayya da ita, amma ita ta riga tasan hakan ba mai yiwu wa bace, Farouk ba zai taba kyale ta ba, gwara ma Ya Anas ɗin yazo ayi ta ta kare.a: DG

                       41

©Hafsat Rano

RANAR WANKA….!
    Ba’a boyen cibi

★★★★
Dukka ahalin biyu sun hallara a babban Falon gidan Alhaji Marwan, kowa ka kalli fuskar shi yana cikin zulumin abinda ya tattara su haka waje daya, Mama tafi kowa shiga tashin hankali ko kwakkwaran motsi ta kasa yi sai rarraba ido take kamar tsohuwar munafuka, a gefen kafarta Amal ta zauna, Anty Safiyya da Mummy a kujera two seater Ja’afar da Farouk a kasan su, sai Alhaji Marwan da Uncle Aliiyu, suma a waje daya, Dadah da Hajiya Turai sai Ammi a kujerar ta ita kadai Aminatu zaune daf da ita, Kamal na zaune shima a gefen Ammin yaji karfin jikin sa.
   Shigowar Daddy yasa kowa ya sake nutsuwa, a tsakiyar falon suka wurgar dashi kafin su juya su fice, dafe kirji Mama tayi ganin wanda bata taɓa tunani ba, kuka Amal tasa ta yunkura zata wajen sa Daddyn ya dakatar da ita

“Kar wanda ya motsa daga in da yake.”

Komawa tayi ta zauna ta cigaba da kukan ta kasa kasa. Tasowa Dadah tayi, ta tsaya a kansa, yana dagowa ta taska masa mari, ta kuma taska masa kafin tasa kuka

“Tir da kai Adam!”

Komar da ita wajen zaman ta Daddy yayi yana duban kowa na falon

“Alhamdulillah, kamar yadda kuka sani abubuwa da yawa sun faru ba tare da sanin takamaimai abinda yake kawo faruwar hakan ba, toh alhamdulillah, a yau komai zai bayyana kansa, duk wasu kulle kulle zasu warware.”

“Adam…Muna so kayi mana bayanin dalilin ka na raba Aminatu da iyayen ta .”

“Cin amana ta suka yi.”

“Su waye?”

“Mutanen da ke kokarin binne boyayyen sirrin su, su hau kai su zauna suna rayuwa ingantacciya ba tare da tuna komai ba, Marwan da Fatima kun yaudare ni, yaudara mafi muni…!”

“Babu wanda ya tausaya min balle ya tsaya ya tambayi ba’a sin gaskiyar komai, tabbas nayi kuskuren aminta dakai, na daukake ka fiye da kowa….”

“Soyayya mukayi me tsafta, babu wani abu me kama da rashin kirki a ciki, zuwa lokacin da muka riga muka aminta da juna, kai na fara tuntuba da maganar.”

Ya nuna Alhaji Marwan

“Kai na shawarta har ma na baka  wuka da nama wajen neman ta, haɗe da address din gidan su, a matsayin ka na wanda na dauka babban wa, kuma uba! Me kayi? Me kayi min…?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button