DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kaje ka bata ni wajen ta, sannan ka nuna musu tarin dukiya, ka aure ta ka raba ni da ita, shin akwai adalci anan?… Tun daga lokacin na fara neman hanyar da zan lalata ma komai daka mallaka, ban samu dama ba.”

“Lokacin dana fuskanci Fatima na dauke da juna biyu nayi bakin ciki sosai, na kuma kuduri aniyar daukar fansa ta ko zan mutu a garin haka, hakan da nayi kadai nasan na gama da ku, rayuwar kunci da talauci da kaskanci yar ku tayi, sannan na sa aka rufe mahaifar ta saboda bana bukatar ku cigaba da haihuwa.”

“Ni na chanja ya’yan na dauki taku na bada ita a inda nasan ko kare kuke kiwo ba zai yi irin rayuwar nan ba.”

“Yanzu wannan dalilin ya isa ka lalata min rayuwar ya?”

“Kai kasan zafin so? Kasan yadda yaudara take da ciwo? Baka sani ba ko?”

Murmushin yayi

“Ban taba dana sanin abinda na aikata muku ba, kun chanchanci fiye da hakan ma.”

Kuka ya hana Ammi magana, sam bata taba tunanin hakan zai zama babbar matsala a rayuwar ta ba, yanzu dama rashin haihuwar ta Adam ne? Bayan raba ta da yarta da yayi har da karin wannan, sama da k’asa kawai numfashin ta keyi, duk hankalin kowa ya koma kanta, Kamal duk ya rikice duk dauriyar sa sai yaji yana neman kasa wa.

“Menene alakar auren Aminatu da Farouk da kai?”

“Shiri na ne, ni na kulla komai, ban dauka zai sota ba, sai dana fuskanci yana son ta, sai nayi kokarin dora Amal akan turbar soyayyar sa, mu muka aika mata da takardar saki, mukayi komai cikin tsari, saboda ina so tayi rayuwa cikin kunci har sanda zata mutu!”

Tashi Farouk yayi, Daddy ya sa hannu zai dakatar dashi, sam yaki ma kallon Daddyn har sanda ya damke shi.

“Kai ne kayi min wasa da rayuwa kamar ka sami kwallo, ka bata min lokaci da komai, akan wani banzan dalilin ka mara tushe.”

“Sake shi Farouk!”

Daddy ya daka masa tsawa. Sakin sa yayi ya koma ya zauna

“Menene alakar ka da Hajara.”

“Ina tunanin na amsa maka wannan tambayar dazu, ko da yake bari na maimaita.”

“Zafin ranka yasa nayi amfani dakai wajen kawo maka baragurbi na kuma tabbatar da ka yarda dani, Hajara yarinya tace, ni nake sata komai, kuma da ita muke komai.”

“Ita ta taimaka min wajen ganin komai yazo min da sauki, ita ta kai takardar sakin Aminatu ita da Aminiyar ta sai dai bata bari aminatun ta ganta ba saboda bacin rana, haka ma dakikiyar matar data rike Aminatun.”

“A takaice dai duk wani abu kaine, kai ne ka raba Aliyu da kasar sa, ka raba ni da Abidah, kaine ka shirya komai.”

“Aliyu yayi kokarin shiga abinda babu ruwan sa, ganin zai kawo min cikas yasa na batar dashi ta hanyar da zai dade kafin ya waiwayo gida.”

“Ban aikata wa Anty Abidah abinda kake zargin mu ba, nayi amfani da hakan ne wajen saka maka zargin ta don nasan a irin zafin kanka ba zaka taba zama da ita ba. Duk wanda yasan sirri na nayi kokarin ganin na nisanta shi da ku, Anty Abidah ta shiga hurumin da ba nata ba, dole aiki ya biyo ta kanta.”

“Wanne irin sirri ne haka?”

Dadah ce ta katse shi

“Zan sanar daku, ina rokon gafara tun kafin kusan komai, zuciya ta cike take da nadama da dana sani, duk da bawa baya gujewa ƙaddarar sa, na dau hakan kuma na rungume ta hannu biyu ina kuma fatan mutane da yawa su dau darasi a cikin labarin da xan bayar amma ina so Amal da Kamal su dan bamu waje,da, idan yaso sai ku duba abinda ya dace.”

“Shikenan babu damuwa.”

Tashi sukayi suka shiga ciki sannan ta fara


“Mu hudu ne a wajen mahaifan mu, mata biyu maza biyu, bayan aure na Allah yayi wa mahaifan mu rasuwa, tun daga lokacin rikon kanwata Habiba ya dawo hannu na da mahaifin ku muka cigaba da rayuwa tare. Bayan wani lokacin kanin mahaifin ku Adamu shima ya dawo gidan da zama, hakan ya bsu damar sabo da juna da kanwata har na fuskanci akwai soyayya tsakanin su.
  A kwana a tashi har sanda zance ya fasu, mukayi murna sosai nida mahaifin ku, sannan aka hau maganar aure gadan-gadan.
   Duk shirye shiryen da ya kamata iyaye suyi wa ya’yan su nida mahaifin ku mun yi, har zuwa lokacin da aka saka biki yazo, daga cikin gidan aka cire musu waje aka gyara musu suka tare abin su.
     Mahaifin ku ya kasance me tafiye-tafiye, hakan ba karamin takura min yake ba, tun da a lokacin ina kan ganiyar kuruciya ta, haihuwa ta biyu kawai, sosai nake cutuwa da tafiyar sa, sai dai kunya da nauyi ya hanani sanar dashi, haka muka cigaba da zama ba tare da na sanar da kowa ba.
     Watarana da daddare bayan kowa ya kwanta, na zabga tagumi ina tunanin abinda ya damen, Habiba ta shigo dauke da leda, kamar ko yaushe idan Adamu ya siyo mata wani abu nima sai sun miko min, hakan yasa na gane ko ledar mecece,a gefe na ajiye dan sam bani da ra’ayin ci a halin da nake. Zama ta danyi muka taba hira kadan kafin tayi min sallama, har taje kofa sai na tsaida ta nace ta turo min Adamu idan ta koma zan aika shi ya siyo min maganin ssuro, da toh ta amsa ta fita, bata jima ba sai gashi ya shigo rik’e da ledar maganin sauron, karba nayi na ajiye sannan na bukaci ya zauna muyi hira, dariya yayi ya zauna muna tattaunawa har zuwa karfe goma ma dare, kamar yadda addini yace, idan mace da namiji suka kebe toh lallai na ukun su shaidan ne, hakan ce ta faru dani da kanin mahaifin ku, bamu farga ba , har sai da mai afkuwa ta afku, shigowar Habiba da ihun da tayi ne ya ankarar damu kuskuren da muka tafka, lallai wannan itace bakar ranar da bazan taba mantawa da ita ba.”

Runtse ido sukayi yadda labarin ya bige su, baki daya kunya ta mamaye su,babu wanda ya iya cewa kala har zuwa sanda ta ɗora

“Bazan iya tantance muku kalar tashin hankalin da muka shiga ba, washegari sai ga mahaifin ku ya diro, daurewa kawai muke muna farin ciki amma babu wanda yake ciki, kwana biyu tsakani Habiba ta hau ciwo me zafi, wanda zallar tashin hankali da firgici ne ya haifar mata dashi.
   Haka mukayi ta faman jigilar asibiti da ita har mahaifin ku ya koma, ba laifi ta samu dan sauki sai dai bata umm balle a ah, kullum bata da aiki sai kuka, komai ya tsaya mana, walwala da farin ciki yayi kaura daga gidan mu, kwatsam sai ga ciki ya bullo, wanda bani da tantama cikin Adamu ne, tashin hankalin da ba’a sa maka rana, wannan wanne irin tsautsayi ne? Ashe itama Habiba tana dauke da nata cikin, abin ya hade mana sosai kullum sai dai mu zauna muyi ta kuka, har zuwa lokacin da haihuwa tazo mata, tsananin hawan da jinin ta yayi yasa ta jijjiga, bata kai ga haihuwa ba Allah ya karbi ranta da ga ita har abinda ke cikin ta.
   Munyi kuka mun yi nadama mara amfani, kwana bakwai tsakani shima Adamu ya bita, nidai kamar zararriya haka na zama, ciwo ne ya taso min gadan gadan ciki wata bakwai, nayi ta addu’ar Allah yasa ya mutu kafin yazo duniya, sai dai kash, Allah ya ƙaddara sai ya taka doran ƙasa, haka yazo da rai,matsayin dan mahaifin ku.
    Nayi nadama mara amfani, na rok’i Allah gafara nayi kuka har sai da idanu na suka kafe, na cigaba da boye gaskiyar saboda gudun kunyar duniya.
    Bayan abinda Adam ya aikata ne yasa tsoron Allah ya dada kamani, dama nasan bashi da gadon mahaifin ku, sai dai na kasa sanarwa kowa, ganin lokaci na kure min yasa na yanke shawarar sanar da kowa waye Adam, amma kafin nan sai na fara kiran sa na sanar dashi komai, na kuma nuna masa Lallai kai da Aliyu kuna bukatar ku sani.
   Ban sani ba ashe, ba zai taba amincewa ba, a lokacin yayi iya kar kokarin sa wajen roko na akan na bar maganar, ganin na kafe ne yasa shi ya shiga barazana da rayuwar ku.
    Sannan abinda ya faru da Abidah sharri yayi mata, kasancewar taji dukkan abinda muka yi magana akai yasa ya bata mata suna, saboda yana so tayi nesa da rayuwar mu, na san komai sai dai ba zan iya budewa kowa ya sani ba, barazanar sa ce ta hanani aiwatar da komai, na cigaba da zama da tabon a zuciya ta.
  Dan Aallah ki yafe min Abidah, ban kyauta miki ba na saka Alkhairi da sharri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button