DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

To be continued…..DG
                       42

©Hafsat Rano

★★★★★★

“Ki yafe min, ban kyauta ba, ban yi halacci ba, sai dai babu yadda zanyi ne shiyasa, hakan shine kadai mafita a garemu baki ɗaya.”

“Alhamdulillah.” Uncle Aliiyu yace yana murmushi

“Tabbas wannan ranar na jima ina jira, ko a yau Allah ya karbi raina zanyi farin ciki matuka.”

Shiru wajen ya dauka kowa da abinda ke masa yawo akai, ta gefen ido Daddy ke kallon Abidah cike da nauyi da kunyar ta, juyowa tayi suka hada ido tayi saurin hade fuska ta mike

“Ina ganin bani da hurumin shiga rayuwar ku, wannan abune da ya shafi family dinku, saboda haka ni zan wuce, Allah kara rufa asiri.”

“Haba Anty Abidah, dan Allah kar kiyi haka, kiyi hakuri ki yafe wa Dadah, tabbas ba’a kyauta miki ba, amma nasan ki da hakuri da yafiya, dan Allah kiyi hakuri.”

“Aliyu karka damu, ni dama ai na dade da yafe wa duk wanda ya zalunce ni, shi kanshi Adam na yafe masa, saboda ko a yanzu haka aka barshi bashi da wani amfani, kaga kenan tun a duniya ya ga sakamakon sa.”

Baro kujerar da take tayi, ta iso gaban ta, ta riko hannun ta,

“Ina neman alfarmar da ki yafe min, ban kasance me adalci ba, amma wallahi bani da zabi ne, kowanne bawa baya wuce ƙaddarar sa.”

Zuciyar Mummy tayi sanyi ganin yadda matar da girman ta take hawaye, tunanin rayuwar da sukayi a baya da irin zaman da sukayi na dadi da mutunta juna, ba zata iya fadar aibun ta ba ko ko rashin kyautawar ta, dan adam ajizi ne, kowa kuma nayi laifi. Kasa jurewa tayi, ta riƙe ta sosai tana kokari boye nata kukan tace

“Na yafe miki Dadah, Allah ya yafe mana baki daya.”

Sai ta sake ta tana maida fuskar ta gefe ganin Daddy na shirin tasowa

“Safiyya, Ja’afar, Farouk ku tashi mu tafi.” Tace tana yin hanya

“Dakata!” Ya tsaida ita

“Ki tsaya a k’arasa komai, abinda ya shafi rayuwar Farouk ne, idan ma ni kike gudu karki damu, ba zan tilasta miki ba ai.”

Da wani kallo ta jefe shi, yayi murmushi yana komawa wajen zaman sa, a darare ta koma ta zauna kafin Daddy yace

“Dukkan sirrikun dake rufe sun bayyana, kowanne da musabbin aikata shi, tsakani na da Adam da Hajara sai dai nace Allah yayi min sakayya, sannan maganar ‘yayan da muka haifa tare kotu ce kadai zata tabbatar da nawa ne ko nashi ne, sabo…”

“Wallahi tallahi karya yake min, duk abinda ya fada da sa hannu na a ciki, chanja yara, takardar saki da duk wani abu nice me kai masa rahoto, amma wallahi maganar yara naka ne, babu wani abu makamancin haka da ya shiga tsakanin mu tun bayan auren da mukayi.”

Ta katse shi cikin kuka, murmushin takaici Daddy yayi ya cigaba da bayanin sa

“Saboda haka na saki Hajara saki uku! Ba zan iya zama da mace irin ta ba. Alhaji Marwan kai akafi yiwa cuta mafi girma da kai da mai dakin ka, ina baka damar bin diddigin duk wanda suke da hannu cikin rayuwar Aminatu, a nemo su ayi musu hukunci daidai dasu.”

“Sannan na riga na kirawo yan sanda, su tafi dasu daga nan sai a kai maganar kotu, idan yaso sai ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata, saboda daukar doka a hannu ya saba ma sharia, Farouk kayii musu magana su shigo.”

Yace yana komawa baya, tashi Farouk yayi, ya fita jim kadan suka shigo tare da yan sandan su biyar maza hudu mace daya, suna zuwa suka sara wa Daddy, suka koma gefe daga musu kai kawai yayi sannan yace

“Gasu nan ku tafi dasu.” Yaa nuna Adam da Mama.

Tsit wajen yayi sai ihun kukan Mamaa tirje tirje ta hau yi tana magiya, babu wanda ya saurare ta, rike hannun Daddy tayi ya fisge yana dauke kansa, bashi da bukatar ganin ko da me kama da ita ne a yanzu, iyakar cutar wa sun masa, sai dai yace Allah ya saka masa.
  Babu wanda ya iya magana har aka fita dasu, Adam nata zage zage da cin mutunci, jikin kowa yayi sanyi musamman Amal data yi tunanin za’a hada da ita, bata taɓa sanin mahaifin nata ya kai haka ba, he used her ya samu abinda yake so, ya kuma nuna mata shi aka cuta, bata san abubuwan daya aikata sun kai haka ba, hatta sharrin data yi wa Dadah da Ja’afar akan maganar sakin shi ya sakata, bayan babu sanin su duk dan ya riga ya gama juya mata tunani. Kunya da nauyin mutumin daya riƙe ta da amana take, Daddy yayi mata halacci be nuna banbanci tsakanin ta da ya’yan shi ba.

Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji Marwan daurewa duk da baya jin dadin komai yace

“Ina bawa kowa hakuri bisa abinda ya faru, lallai akwai rashin kyautawa ga kowanne bangare, sai dai hakan ba zai hana hukunta masu laifi ba,ina fatan duk wanda hukunci ya biyo ta kansa yayi hakuri, mu dukka abu daya ne, kuma zamu cigaba da rike juna da mutunci. Sannan ina sanar da dawowar ya ta, duk da wasu a cikin ku sun santa, sai dai wannan sanin yasha banban dana baya, Aminatu yata ce ta cikina, kowa yaji yadda aka chanja mana ita, ina fatan kowa ya karbe ta hannu bibbiyu, ba wai a matsayin matar Farouk ba, a matsayi ‘ya ga Marwan Dikko!”

Da sauri Mummy ta dubi Aminatun, duba na tsanaki kafin ta dauke kanta tana mamakin yadda abin ya zama.
    Hajiya Turai tafi kowa shiga farin ciki, takanas ta taso ta dawo wajen Aminatu, ta sata jikin ta tana murna, tabbas jinin tace, babu tantama ko shakku. Duk da kasancewar Dadah tayi farin cikin samun labarin, sai dai bata da kuzarin nuna hakan duba da yadda kunya da nauyin ahalin ta mamaye ta, saboda haka bata iya cewa komai ba sai kokarin danne abinda ke taso mata na nauyi da kunya kawai take.
    Amal kanta sai da maganar ta girgiza ta, ta shiga duban Aminatun da wata kama daban ba wadda tasan ta a baya ba,duk da amintar dake tsakanin Alhaji Marwan da Daddy, sai dai nisa da tazarar dake tsakanin su ta fannin arziki ba abu bane karami, ta ko ina MD ya yaga wa Daddy. Gashi ita bata ma da tudun dafawa kasancewar uban da take tunkaho dashi da babu duk daya, hakan ne yasa ta jin shakku, tabbas Aminatu ta yaga mata ta ko ina, tayi mata nisan da har abadah ba zata taba kamo ta ba, gashi ita yanzu bata ma san makomarta ba,ko Daddy zai cigaba da rike ta kamar yadda ya fara? Shine bata sani ba.

     Duk da Ammi ta kadu sosai jin cewa Adam na da hannu a rashin haihuwar ta, sai dai taji dadi, atleast ta samu hanyar da zata nemi maganin matsalar ta a addinance. A kasan ranta ta tausaya masa, duk abinda yayi a dalilin son da yake mata ne, wanda ita kanta tasan bata kyauta masa ba, amma kuma abinda yai mata yayi tsauri sosai, sai dai tana fatan hakan ya zama izina ga yan baya, wani zai iya jure ma yaudara amma wani ba haka ba, zai iya salwantar da rayuwar wadda ta yaudare shi kamar yadda Adam yayi mata ko ma fiye da haka.
  
Ganin an tafi wata maganar daban yasa Farouk daurewa yace

“Am…am… Daddy dama maganar    da kace na bari a zauna…”

“Auw kaga naso na manta.” Alhaji Marwan yace yana murmushi

“Game da maganar auren su, ya kamata asan halin da ake ciki, tun da dukkan bincike ya nuna bashi da masaniya akan komai, dukkan abin da ya faru plan ne babu abu daya daya kasance gaskiya, bayan haka ma ko da ya kasance da gaske ya aikata sakin a bisa tirsasawa aka gusar masa da tunani, ko bisa rashin sani toh akwai maslaha akai kamar yadda yazo idan har ya tabbata bashi ya sha kayan mayen da kansa ba kuma ba’a cikin hanyacinsa yayi haka ba, to hakika sakin baiyi ba domin alkhalami ya sauka daga kansa sakamakon baya hayyacinsa, Sannan ya tabbata acikin hadisi Manzo s,a,w yana cewa:_
ان الله تجاوز عن امتي الخطا والنسيان وماستكرهواعليه
_Ma’ana Allah ya daukewa al-ummah ta laifuka guda uku (3) Na farko: Abinda sukayi bisa rashin sani. Na biyu: Abinda sukayi bisa Mantuwa. Na uku: Abinda sukayi bisa tilastawa Abinda aka tilasta mutum yayi kenan ba’a Son ransa ba.
Sai dai dukkan shaidu sun nuna bai aikata ba, bashi da masaniya ma akan abinda ya faru, hakan ya tabbatar da auren su yana nan, da ace dai tayi wani auren ne toh fa tabbas ta kubce masa.
WALLAHU A’ALAM????????
  Ina fatan hakan zai wanke duk wani kokonto daga zuciyar kowa.
Aminatu ta koma dakin ta su cigaba da zaman su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button