DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Kasa Aminatu tayi da kanta tsananin kunya duk ta rufe ta, babu wanda maganar batayi wa dadi ba in ka cire Amal, Ammi da Mummy da ba zaka iya tantance abinda ke ransu ba.
Mik’ewa Ammin tayi tana kama hannun Aminatun kafin tace
“Ayi min afuwa, ina bukatar yarinya ta a tare dani, saboda haka sai na sake bincike sosai akai, ba zanyi saurin saka rayuwar ta a matsala ba.”
Tana kaiwa nan ta jata suka shige ciki,rai bace Alhaji Marwan ya mike Daddy ya dakatar dashi
“Tana bukatar yar ta, karka manta shekara ashirin da doriya ba kwana ashirin bane, ka kyale ta dan Allah.”
“Shikenan.”
Ya koma ya zauna, kasan zuciyar shi farin ciki ne dan shima yana bukatar hakan, yana so ya nuna mata gatan data rasa, ya sa mata sabo dashi kafin ta koma wajen Farouk din.
Ita dai Mummy bata ce komai akai ba, ta umarci Anty Safiyya, Ja’afar da Farouk da su tashi su tafi tun da an kare maganar, zancen zuwa kotu kuwa ita ta yafe, bata bukatar komai idan aka tsaya a haka ma Adam yaga ishara.
Farouk be so ba, yaso ko ganin Aminatu ne yayi kafin su tafi, amma baya so Mummy ta ga kamar baya damuwa da ita da lamarin ta, haka suka dunguma har Uncle Aliiyu da yaransu suka bita zuwa Kadunan.
Har sun dau hanya uncle Aliyu ya dakatar dasu yace yayi mantuwa, Iman yaje ya dauko ya fito da ita, da ido Mummy ta dinga bin sa har ya ƙaraso ya bude saitin da take zaune a mota ya mika mata ita
“Ya kamata kiga jikata kafin mu tafi.”
Kallon Iman din tayi kai tsaye ta gane wace, duban Farouk tayi daya gaza boye farin cikin sa tace
“Son?”
“Yes Mum.”
Murmushi tayi ta kura wa yarinyar ido tana jin kaunar ta a cikin zuciyar ta.
“Very cute, Masha Allah.”
“Uncle Aliyu ka bar min ita mana.” Tace tana murmushi
“Anty ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, sai dai da kyar idan Hajiya Fatima zata bar miki dan naga take taken ta.”
“Waye yafi kusa da ita?” Tace tana bata fuska.
“Kece.”
“Shikenan na kwace ta, hakan zai sa tayi gaggawar dawowa da Son matar sa, dan nagano ta so take ta wahalar min da shi.”
Dariya suka sa baki daya, har Iman din da zuwa yanzu ta saba dasu.
“Zaki bini na baki chocolate?”
Tace tana shafa kanta, make kafada tayi tana kallon Farouk
“Tare zamu tafi na riga na tambayi Ummin ki kinji dota.”
Yace dan yasan me take so tace masa, a tambayi Ummin ta, bata kara magana ba ta kwanta a jikin Mummyn, dadi ne ya lullube ta, har bata san sanda ta rungume ta a jikin ta ba.
Dole Uncle Aliiyu ya koma ya sanar wa Daddy sun tafi da Iman kafin ya dawo su dauki hanya.DG
43
©Hafsat Rano
★★★★★★
Shiga daki sukayi, Aminatu ta zauna a gefen gadon tana sunkuyar da kanta, zama Ammin tayi tana daukar wayar ta, mita take tayi tun dazu, hakan ba karamin dad’i yake wa Aminatu ba, wai itace yau ta samu me tsaya mata, lallai uwa me dad’i, tana jin Ammin tana ta waya da yan uwan ta na jiki, tana sanar dasu taron da ta shirya na murnar dawowar Aminatun wanda sai a lokacin Aminatun ke samun labari, ita dai bata ce komai ba har ta gama ta ajiye wayar kafin ta zauna gefen ta
“Kinsan dalilin da yasa naki amincewa da komawar ki? Ba wai bana son Farouk bane,ina tunanin nafi kowa son ki dashi, sai dai ba zan yarda da abinda ya faru a baya ba, dole ne yanzu ya zama kamar sanda zan aurar dake na farko, sai na gyara ki, yadda babu raini tsakanin ki da miji ko kuma uwar miji, zaki fito a cikakkiyar ya ga Marwan Dikko, zan shirya miki gagarumin bikin da kowanne lungu da sako na kasar nan zai dauka, ina fatan kin fahimce ni?”
“Na fahimta Ammi.”
“Good.”
Tace tana tashi,
“Ammi…” Ta dakatar da ita
“Umm??”
“Ina so muje Shagari dukkan mu, nayi wa kaina alkawarin ba zanje ba har sai sanda na hadu da iyaye na.”
“Yaushe kike so muje? Duk da nasan dole binciken da za’a yi yabi ta kansu, dole ne za’a kama ita matar da ta rike ki, da duk wanda yake da hannu, amma dole sai zuwa sanda aka tura case ɗin Adam ɗin kotu, so yanzu kike so muje ko bayan nan?”
“Yanzu dai.”
“Shikenan, bayan taron sai muje, ina da bukatar ganin ta nima.”
Kamal na kwance duk da yaji dadin yadda abubuwan suka kasance, amma ya kasa manta fuskar Inno sanda ta biyo shi tana kiran shi, dukkan motsin da zai yi sai ya tuna, ransa babu dad’i amma kuma kasan zuciyar shi na kwadaita masa sake ganin ta. Shigowar Ammi yasa ya saita kansa ya k’ak’alo murmushi.
“Ya jikin naka?” Tace tana zama a gefen sa
“Da sauki Ammi.”
“Sannu.”
“Ina ganin zamu je chan garin, nan da kwana uku, zuwa lokacin ka kara samun karfin jikin ka, sannan akwai taron da za’a yi gobe a gidan nan na murnar dawowar Aminatu.”
“Owk Allah ya kaimu.”
“Amin.” Tace tana mik’ewa.
“Ammi…”
“Kana bukatar wani abu ne?”
“A ah, babu komai.”
Yace yana had’iye wani abu, dawowa tayi ta zauna tana duban sa
“Menene?”
“Nagode Allah ya saka da Alkhairi Ammi, duk da kun gano bani da wata alaƙa daku amma baku chanja min ba, kun cigaba da kula dani kamar…”
“Ya isa!” Ta daka mishi tsawa
“Yanzu Kamal ni kake wa godiya? Har kake cewa baka da alaƙa dani? Kasan me kake cewa kuwa? Haihuwar kace kawai banyi ba amma baka da maraba da dan dana haifa da cikina, ni nan na shayar dakai, nayi maka tarbiyya, duk wani abu tsakanin uwa da d’a Kamal kai nayi wa, ko musulunci ya tabbatar da ni ɗin mahaifiyar kace ta shayarwa, saboda haka ka zama muharramina, kai dana ne, har duniya ta nade ba zaka daina amsa sunana a matsayin mahaifiyar ka ba.”
Tashi tayi ta fice daga dakin da sauri dan bata so tayi kuka a gaban sa, kukan ya saka shima, dan ba karamin tabashi maganganun sukayi ba, da yasan haka zai bata mata rai da be ma fara ba.
Da daddare sai ga Anas ya iso, tana ganin kiran sa ta sanar wa Ammin, shigo dashi falon tasa akayi, ta fita da kanta wajen sa, cike da girmamawa ya gaishe ta, ta amsa a sake dan tun kafin zuwan sa take daukin haduwa dashi, bayanin kanta tayi masa a matsayin mahaifiyar Aminatu, wanda hakan ya ɗan sashi zama shock, ta lura da hakan sai kawai tayi murmushi ta tashi.
Yana zaune ya kura wa tangamemiyar Tv ido hankalin sa na ga tunanin maganganun Ammin ta fito, sanye take da Hajabi dogo, da ido ya bita har ta samu waje ta zauna.
“Sannu da zuwa Ya Anas.”
“Aminatu, idon ki kenan.”
“Kayi hakuri, ya aiki?
“Alhamdulillah, gashi muna ta fama.”
“Allah ya taimaka.”
“Amin.”
“Menene alakar ki da gidan nan Aminatu? Kinsan waye me gidan kuwa? Ba karamin me kudi bane karki je kisa kanki a matsala.”
Murmushi tayi
“Ya Anas Allah ya amsa addu’a ta, ya haɗa ni da iyaye na.”
“What! Kina nufin Alhaji Marwan Dikko mahaifin ki ne?”
Daga mishi kai tayi
“How comes?” Yace cike da mamaki
A nutse ta bashi labarin yadda komai ya kasance, jinjina kansa kawai yake har ta kare,
“Allah mai iko, na tayaki murna sosai, zan sanar wa Hajiya kuwa gobe gobe dama zan je.”
“Nagode sosai da karamcin ka gareni.”
“Babu komai, wannan labarin yayi min dadi, nasan tabbas Hajiya zata ji dadin labarin.”
“So ya maganar mu? Ina muka kwana?”
“Kayi hakuri ya Anas.”
“Me ya faru? Karki cemin ba zaki aure ni ba after all this time dana dauka ina jiran ki.”
“Ba laifi na bane, a yanzu dana san hukuncin da ke kaina kar mu saba wa Allah, ina da aure a kaina, kayi hakuri na cigaba da kallon ka a matsayin babban ya’ya na.”