DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Mik’ewa yayi da sauri, yayi mata wani irin kallo kafin ya juya kamar zai tashi sama ya fice daga falon.
  Dafe kanta tayi, tasan dama za’a yi haka,sai dai bata so suyi rabuwar rashin dadi dashi, amma tasan fushin sa, dole dama zaiyi abinda yafi haka, zata bashi lokaci har zuwa sanda zai huce.
   Tashi tayi ta koma ciki, tana duba wayar ta ko Farouk ya kira ta, amma babu kiran sa ko daya, gashi Ammi tace kar ta kuskurat ta kirashi, ita abin ma dariya yake bata, yadda Ammin ta dage sosai akan lallai sai ta ja ajinta.


Gagarumin taro akayi, duk yan uwan Ammi da kawayen ta matan kushoshin gwamnati sun halarta, gift kuwa Aminatu ta shashi, har sai data daina gane masu bata saboda yawansu.
   Kyautar sabuwar mota dalleliya Ammin tayi mata, Hajiya Turai kuma ta bata wani dankareren gold sarka da da kunne hade da bracelet me kyau. Kamal ma ba’a barshi a baya ba sabuwar waya yayi mata order ya bata,kukan farin ciki ta saka saboda yadda rayuwar ta ta chanja a cikin awanni kadan da a cikin awannin da tayi na rayuwar ta ba komai bane.
   Daddy kuwa ba’a maganar tasa kyautar dan ta musamman ce, kokarin kiran manyan Drs na kashashe daban daban yake akan matsalar idon ta dan yana so ayi mata aiki me kyau, be fada wa kowa ba, so yake sai komai ya kammala ya sanar musu, yawan shakatawa zasu tafi gaba daya gidajen biyu, daga nan sai Aminatun taga likita, suna dawowa sai a hau shirye shiryen gagarumin bikin da suke shirya mata irin na ya’yan gata.


Kwanan Farouk uku a Kaduna duk ya gundura, babu abinda yake son gani sai ita, gashi ko ya kira ta wayar da suke kadan ce zata ce Ammi na kira, dole yayi wa Mummy dabara ya lallaba ya taho bayan ya bar Iman din a chan duk kuwa da kashedin da Ammin da kanta ta karbi wayar tayi masa akan lallai idan zai dawo karya kuskura ya dawo babu Iman din, gashi Mummy ma ta kafe shi kam be san ya zai musu ba, abu daya yake ganin shine kawai Mummy tayi hakuri ta dawo gida, in yaso sai su dinga shifting idan tayi kwana biyu ana sai ta koma nan.
   Har ya iso Abuja be daina tunanin yadda zasu kwashe da Ammin ba, sai da yayi wanka ya huta sosai, ya duba Dadah da bata jin dadi tun abinda ya faru,sannan ya nufi gidan kanshi tsaye.
  
Ta window ta hango shigowar shi, tayi saurin tashi daka kwanciyar da take, ta fada toilet, wanka tayi a gurguje ta dauro towel ta fito, kai tsaye wajen mirror tayi ba tare da ta lura da shi ba, ta cikin mirror ta hange shi, gaban tane ya yanke ya fadi ganin mutum a zaune a kan gadon ya zura mata ido ba ko kiftawa, da sauri tayi hanyar toilet din cikin zafin nama ya rigata k’arasa wa ya chapke ta.

“Karki manta soja ne ni, ba zaki fini gudu ba.”

“Dan Aallah…”

“Shissh karma ki fara wallahi, ba a isa a hanani abinda Allah ya halatta min ba.”

“Ammi zata shigo fa.”

“And so? Shine daidai ma ai.” Yace yana zagaye hannun sa a saman fuskar ta, runtse idon ta tayi da sauri, ta rike hannun shi.

“Pleee… Please kayi hakuri.”

“Please kayi hakuri.” Ya kwaikwayi muryar ta yana dariya.

Hannu ta kai chest din sa ta dake shi, ya rike hannun yana ɗorawa a saman kirjin nasa

“Kiji yadda zuciya ta ke bugawa da sauri da sauri, I’m dying to be with you, please do something.”

Saurin zare hannun ta tayi, tana juyar da kanta. Zagayo wa yayi bangaren fuskar ta ta

“Bari naji yadda take take bugawa.”

Da sauri tasa hannu ta kare saman chest dinta, ta lura so yake sai ya kure ta dole, ga wata masifaffiyar kunyar sa da take ji, Allah yaso ta ma towel din da dan girman shi, duk da haka ana iya ganin fiye da rabin jikin nata.
  Baya ya ja ya harde hannu yana karewa ko ina na jikin ta kallo. He just can’t wait…: DG*
                       44

©Hafsat Rano

★★★★★★

Maganar Ammi ce ta iso musu tun kafin ta ƙaraso tana bada order, a diririce ya hau neman wajen da zai boye, duk rashin kunyar sa yana tsoron tazo ta ganshi a haka, dariya Aminatu ta shiga yi masa ba kakkautawa, be kula ta ba, yayi saurin samun corridor dake jikin wardrobe ya makale daidai lokacin ta shigo, tsaye tayi tana karewa dakin kallo kafin idanun ta su sauka akan kafafun sa dake bayyana a fili, basarwa tayi ta dubi Aminatun tana hararar ta

“Me kuma kika tsaya kamar wata soja, ko ba wanka kikayi ba?”

Da sauri ta juya ta shige toilet tana kunshe dariyar ta, rigar data cire ta maida ta saka,

“Me haka? Ba sune jikin ki ba dazu?”

“Auw sune.” Tace a diririce, wajen wardrobe din tayi ta bude ta dauki kayan ta koma toilet din. 
Sanda ta fito Ammin bata dakin, kallon inda yake a makale tayi ta kwashe da dariya yayi saurin fitowa, rankwashi ya kai mata ta goce tana dariya

“Maganin me satar hanya kenan.”
Tace tana masa gwalo,

“Yarinya bashi kika ci, xan dawo ne.”

Ya juya ya bar dakin, sai da ya fara tabbatar da babu kowa a falon sannan ya fice daga gidan da sauri yana murmushi.

***Hajiya Turai ce ta aiko aka kira ta, a chan ta tarar da Kamal ta zauna aka cigaba da hirar da ita duk da ba wani sake wa tayi dasu ba amma yadda suke jan ta a jiki yasa ta saki jikin ta itama, har Daddy ya dawo suna wajen,anan suka ci abincin dare gaba dayan su, cikin farin ciki, duk motsin da zatayi sai an samu wanda zai tambaye ta ko akwai wani abu da take bukata? Ta kanyi murmushi tace babu, dan ita a halin yanzu babu kuma abinda zata nema, sai fatan cikawa da duniya lafiya.

Sai data gama shirin kwanciya tsaf, tayi wa Ammin sallama ta haye saman sabon gadon ta, wanda ya kawatu da abubuwa na jin dadi da more rayuwa, cikin kwana biyu aka shirya mata dakin duk kuwa da sun san ba dadewa zatayi ba, babu ce kawai babu a dakin.
  Sama sama taji motsi kamar ana bude kofar, shiru tayi tana sake ji, tunanin ta ko Ammin ce, ta tashi tana kunna bedside lamp, idon ta ya sauka a cikin nasa ya zura hannayen sa cikin aljihun dogon wandon sa, fuskar sa na fitar ta bayyananan murmushi me sanyaya zuciyar wanda ake yi wa shi.

“Yaaa F…”

“Shissh!”

Ya dora hannun sa alamun tai shiru, juyawa yayi ya murza key ɗin dakin sannan ya dawo, ba jiran komai ya haura saman gadon ya kwanta akan bayan sa, ƙafafuwan sa da suke mike sosai ta kalla, ta maida kallon ta kan fuskar sa.

“Kashe wutar nan please bana kwana da haske.”

“Kwana? Anan zaka kwana?”

Ware idon sa yai, ya daga mata kai

“Akwai damuwa ne!?”

“Ammi fa…” Tace da sauri,

“Haram na aikata?”

Girgiza masa kai tayi,

“Oya kashe ki kwanta, gudnight.”

Ya juya bayan sa, yawu ta hadiye ta kashe wutar tana kwanciya a chan gefe, ƙasa ƙasa yace

” Karfi da yaji an maida mutum gauro.”

“Na’am?” Tace tana sake matsawa

“Babu.”

Shiru ya sake biyo baya, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa, yadda komai ya sauya daga abun da ba zaka taba tunani ba zuwa me wanzuwa a yanzu a wani bigire na daban, sauyawar akalar rayuwa zuwa wani abu daban abin birgewa da sa farin ciki. Lallai komai ya faru da bawa mukaddari ne, haduwar su da taimakon da yayi mata ya zama wani tsani na rayuwar ta, tsanin da zai yi wuya ta taka shi idan ba wannan dalilin ba.

Mirginawa yayi har ya isa gareta, ya raba hannun sa biyu ya toge dayan da kanta yace

“Bani labari.”

Ajiyar zuciya ta sauke kadan, ta gyara kwanciyar ta sosai, a hankali tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button