DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Gobe zamu je Shagari.”

“Daddy ya fada min.”

“Owk zaka je? I’m feeling nervous.”

“Yes zanje, dole na zama by your side ai, yadda zanji daɗin karya wuyan duk wanda yayi miki kallon da ban gamsu dashi ba.”

Murmushi tayi

“Can you do that?”

“Kina mamaki? Zan iya abinda yafi haka ma ai.”

“Ummm.”

“Allah dai ya kaimu goben.'”

Yace yana sake matsowa jikin ta sosai, hira suka cigaba me dad’i, gaba-daya abinda ya faru a tafiyar sa, da abinda ya faru sai da suka sanar wa juna, wani suyi dariya wani kuma babu dad’i, ba tare da sanin su ba ashe dare yayi sosai, ganin idan suka biye wa hirar zasu kai asubah yasa suka hakura suka kwanta, duk da haka sai da ya tabbatar da ya aika mata sakonnin sa masu tsayawa a zuciya, duk da sakonnin kanana ne ba’a kai ga babban sakon ba,amma hakan yayi tasiri k’warai wajen sake dasa kyakkyawar alaka tsakanin su.
    Kiran asubah ne ya tashe shi, yayi saurin tashi ya gyara mata kwanciya, saboda yasan tana fashin sallah, shiyasa be tashe ta ba ya fice bayan ya tabbatar da babu kowa daya ganshi.


Karfe sha daya suka bar Abuja, suka isa Kano cikin yan mintuna da yake a jirgi suka tafi, suna isa suka dauki hanyar Katsina, daga Kamal har Aminatu babu wanda yake magana a cikin su, jifa jifa Farouk ke sako shi a cikin hirar tasu, bashi da kuzarin amsa musu sai dai yayi murmushi kawai.
  Hankalin Ammi ya tafi ne ga kallon hanya, tana fatan su isa lafiya ta samu damar ganin Inno, matar da bata san a wanne bigire zata ajiye alakar su ba, sai dai tana jin ciwo da haushin irin rikon da tayi wa Aminatu, duk kuwa da tasan ba komai Aminatun ta faɗa mata ba. Idan ta tuna wacece a wajen Kamal sai taji tana kokonton irin hukuncin daya dace da ita, ko banza ance uwa uwa ce ba zata so abinda zai bata wa Kamal din ba.
   Haka dai ta cigaba da tunanin abinda take ganin shine, amma bata iya jin zata saurara mata dole ne zata nuna mata kuskuren ta ko dan gaba.
   Shigar bayan azahar sukayi wa garin, kai tsaye gidan suka nufa hakan ya kara tsananta bugun zuciyar Aminatu da take ji kamar zata huda kirjin ta, ta fito, tsoron abinda zata tarar ne dankare a zuciyar ta, bayan tafiyar ta tasan dole abubuwa sun sauya, sai dai ba zata iya daukar rashin wani a cikin mutanen da tayi rayuwa dasu ba ko da kuwa Inno ce.
  
A kasalance ta fito daga motar, rantsattsen lace ne a jikin ta wanda yasha ɗinkin k’warriyar telar nan pink couture, kallo daya ya isa ya gamsar da kai matakin da ta taka ko kuma take shirin takawa a yanzu.
   A sanda Ammi ta bata kayan ita kanta sai data jinjina, dan tasan ba karamin kaya bane, duk sai taji ta kasa sawa tana tantamar wai itace? Sai da Ammin ta sake dawowa sannan ta matsa mata ta saka.
    A waje su dukka suka tsaya, kowa ya zuba mata ido kafin Ammi tace

“Ki shiga muna waje.”

Rau-rau tayi da idon ta, ta soma takawa a hankali, duk takun da zatayi sai zuciya da gangar jikin ta sun amsa, idon ta ta wurga gefe, matan dake makwabtaka dasu tuni sun fara lekowa jin tsaiwar mota, sai dai daga kallon da suke mata basu gane wacece ba, kada kanta tayi ta kutsa cikin zauren gidan nasu, yana da tsantsar talauci sunyi wa zauren k’awanya, inda zaka yi tunanin an dauki shekaru masu tsawo ba’a bi ta cikin zauren ba.
  Bakin ta dauke da sallama ta shiga, Karime da tazo ganin gida ta saki tsintsiyar dake hannun ta, idan har ba gizo idanun ta ke mata ba, tabbas Aminatu ce.

“Amin…” Bata karasa ba tayi saurin isa ta rungume ta, kukan da take boye wa ya taso mata gaba daya

“Inna, Inna fito ga Aminatu.”

Tace a gigice, da mugun gudu Inno ta fito, sai tayi turus ganin Aminatun cikin shiga ta alfarma, tsoro ne ya kamata, ta tsaya jikin kofa ta kasa karasowa.
  Kallon yadda ta koma Aminatu keyi, idan za’a gaya mata Inno zata zama haka zata iya musawa, babu fiye da rabin jikin ta, ta rame ainun, daga gani tana cikin mawuyacin hali. Da sauri Karime ta dauko tabarma, ta shimfida.
Takowa tayi ta zauna tana kallon dakin Baba, sai ta mike ta isa dakin ta tura kyauren daya gama lalacewa ta shiga, yana kwance akan tsohuwar katitar sa data kara lalacewa, duk yayi baki ya rame abun tausayi, a gaban sa ta durkusa tana sakin kuka me tsuma rai, kukan da take ya farkar dashi daga baccin wahalar da yake, a cikin mawuyacin hali ya kira sunan ta, da ace ma ba a kusa dashi take ba, babu yadda za’a yi taji Hannun shi ta kama ta rike cikin nata, ta cigaba da kuka. Da kyar ta saita kanta tace

“Sannu Baba! Ya jikin?”

“Alhamdulillah.”

Shigowa Yalwati ta yi dan tabbatar da abinda aka gaya mata, turus tayi ganin da gaske Aminatun ce

“AMINATU kece?ikon Allah.”

“Nice, mun same ku lafiya? Ya jikin Baba?”

“Lafia lou, tare kuke da mutanen dake waje?”

Da sauri ta tashi

“Bari nace su shigo,tare muke.”

Tayi waje da sauri, Inno na tsaye in da ta barta, matsawa tayi gaban ta, ta tsuguna har kasa

“Ina wuni Inna?”

“Tsawon lokacin nan kina ina ? Shine kika ki waiwayo wa? Sai yanzu.”

“Kiyi hakuri, tare muke da baƙi bari nace su shigo.”

Tayi saurin ficewa, suna tsaya tace su shigo, ta juya suka bi bayan ta Ammi jikinta ya gama sanyi dan bata zaci lalacewar ta kai haka ba.
Sallamar su kadai tasa cikin Inno kadawa, bata jira ta gama tantance su ba ta zari buta da sauri tayi banɗaki, zama sukayi akan tabarmar Yalwati ta zo suka gaisa kafin ta tashi ta kawo musu ruwa tana satar kallon Kamal.
Jimawa tayi sosai a ciki, da kyar ta fito, sakin butar tayi ta fadi, ta kwala kiran

“Yalwati, Yalwati! Zo kiga wallahi dana ne, shine yazo ranar zo ki gani karya ƙara tafiya.”

“Na ganshi yaya, ki nutsu ku gaisa.”

Tsugunnawa tayi a gefe duk jikin ta sai rawa yake kamar mazari. Cikin dakiya Aminatu tace

“Inna wannan itace mahaifiya ta.”

Zumbur ta mike ta hau waige waigen inda zata buya dakatar da ita Ammi tayi

“Ki tsaya muyi magana ta fahimta tun da ni dake a yanzu mun hadu akan abu guda, cuta dai kun riga kun cuceni, babu abinda zance muku sai dai na barku da ALLAH.”

“Babu abinda ya rage na boye boye,komai ya bayyana, Aminatu ta hadu da iyayenta na asali, cikin mutunci.

Ko ban fada ba kinsan a yauzu ta wuce kallon banza balle a daga mata murya. Ina fatan hakan ya zama izina gare ki dama duk wani me irin wannan tunanin, Kamal da Aminatu dukkannin su yayana ne, ni nan na shayar da shi saboda haka baki da hurumin sake shiga rayuwar mu.”

Dagowa tayi da sauri, ta sauke idon ta akan Kamal din, yayi mata nisan da za’a iya misalta shi da tsakanin sama da kasa, ita dama tasan ko da Hajiyan bata ce haka ba, abu mawuyaci ne ya dawo gareta, share hawayen dake faman yawo a fuskar ta tai tace

“Hakika nayi kuskuren da zai cigaba da bibiyata har sanda zan koma ga mahalicci na, ban chanchanci daya daga cikin su ba, na zame masa uwa, ina rokon da ki yafe min, ki dubi halin da muke ciki ko da shi kadai aka barni ya ishe ni ishara.”

“Bani zaki roka ba, Aminatu kika cuta, kika batawa rayuwa, idan nace zan daureki akan laifin da kika aikata mata bana jin igiya zatayi saura.”

“Aminatu ki yafe min dan Allah!”

“Na yafe miki inna, na jima da yafe miki.”

“Idan har ita ta yafe, ni da Daddy ba zamu yafe ba.”

Ya fada rai bace

“Kamal?”

“Babu ruwanki Aminatu, wannan ba maganar ki bace.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button