DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Tashi yayi ta fita, suka bi bayan shi da kallo, babu wanda yayi magana. Wajen Farouk ya koma yana ta waya, jingina yayi da motar wani abu me daci ya tsaya mishi a makogaro. Tsayuwar motar yan sandan yasa Farouk aje wayar da yake, tuni unguwar ta soma cika jin karar jiniya, Harira, sister Asibi ne a bayan motar kowacce an saka mata handcuf. Durgowa police din yayi, ya tsaya gaban su
“Wacece dyr?” Yace yana kallon shi
Shiru Farouk yayi ganin KAMAL ɗin a tsaye, ganin haka yasa Kamal din yace
“Bismillah, muje na nuna muku ita, dama munyi yawa da Daddy akan haka.”
Gaba yayi suka bi bayan shi, yana shiga ya nuna Inno
“Gata nan arrest her.”
A zabure Aminatu ta tashi tsaye tana wa Kamal kallon mamaki,
“Menene haka?” Tace rai bace tana duban sa.
“Ku tafi da ita officer.” Yace yana dauke kansa.
A gaban sa Aminatu ta tsaya tana masa duba irin na wanda be san abinda yake ba, cikin bacin rai tace
“Me kake shirin yi?”
“Babu ruwan ki.”
Kuyi hakuri da short page na aje wayar oga Affan ya dauka yanzu screen din ya tabu da kyar na iya rubutun inayi yana gogewa wlhia: DG
45
©️Hafsat rano
★★★★
“Officer ku tafi da ita “
“Hajiya you are under arrest “
ya saka mata handcuf, jujjuya kanta kawai take cikin tsananin tashin hankali, a gaba suka sata Kamal na bin bayan su, kukan da take yana shiga cikin kunnuwan sa yana masa amsa kuwa, tsayawa yayi daga nesa yana duban motar, da gudu Karime tayi inda yake tsaye ta durkusa ƙasa tana kama kafuwan sa
“Dan Allah karka yi mata hukunci data aikata…Mahaifiyar ka ce ka taimaka bata da lafiya.”
Dauke kansa yayi dacin da yake ji na sake taso masa, ko tantama babu ita ɗin kanwar sa ce, sai dai bashi da hurumin hana hukuma aikin ta, na hukunta duk mai laifi.
Ciki ta koma da gudu tana kiran Aminatu, tare suka fito yana ganin su ya yi saurin buɗe mota ya shige dan ba zai iya jure ganin su ba. Duban Farouk tayi, magana suk’ da daya daga cikin yan sandan, kenan duk sun san da plan din kamasun shisa ma ko a ciki Ammi taki cewa komai duk kuwa da magiyar da tayi ta mata.
Karasowa akayi Garbati da Ila aka watsa su ciki suma, jan hannun Karime tayi suka koma ciki tana kuka, suna jin sanda motar ta daga ta bar unguwar, yara da manya aka samu abin magana.
Daki suka shiga, ta hau rarrashin Karimen da maganganu masu dadi, sosai take jin zafin Farouk da Kamal har ma da Ammin shisa da suka ce ta taso a tafi taki, tace zata tawo.
Babu wanda ya matsa mata tunda dama a garin zasu kwana. Suka tattara suka tafi suka kyale ta. Da tashin hankali Nura ya shigo gidan labari ya kai masa, lokacin jikin Baba ya kara rikice wa saboda abinda ya faru, mota ya tafi ya kirawo suka kwashe shi zuwa asibiti.
Duk abinda za’a bukata Aminatu ce ta biya, kudade ba kadan ba saboda ba karamin asibiti bane, ganin za’a iya bukatar wasu kudin gashi bata dashi yasa ta kira Kamal, lokacin yana zaune duk abin duniya ya dameshi
“Kudi nake bukata muna asibiti da Baba.”
Tace kai tsaye,
“Ina ne asibitin? zanzo.”
“Ok.” Tace tana kashe wayar
Cikin kankanin lokaci ya isa asibitin, a barandar ya hange ta tana tsaye ta zuba wa gate din ido, karasowa yayi ta nuna masa wajen biyan kudin bata ce mai komai ba, zuwa yayi ya biya abinda ake bukata ya dawo in da take, da hannu ta nuna masa dakin da Baban yake ta koma wajen da Karime ke xaune.
A darare ya bude dakin da aka kwantar da Baban ya kura masa ido, idon sa ne ya cicciko da kwalla ganin mutumin da ya kasance mahaifi a gareshi cikin tsananin wahalar talauci da tsananin ciwo.
Har gaban gadon ya taka ya na kare masa kallo, bacci yake me wahalarwa numfashin sa na fita da kyar ta cikin oxygen.
Dukkan su ba’a yi musu adalci ba sam duba da yadda abubuwan suka kasance.
Lallai Aminatu nada karfin zuciya idan wata ce ba xata kalle su ba balle har ta tausaya musu, sai gashi har fushi take dasu akan abinda ya xama dole.
Sai da Ammi ta kirasu sannan suka bar asibitin, har lokacin Aminatun na fushi dasu.
Washegari suka sake dawowa asibitin, ta bawa Nura kudin da Kamal ya bata sannan ta bawa karime wani abu tace ta rike a wajen ta ko zata bukaci wani abu sannan suka tafi.
Taso kwarai su kara kwana amma Ammi taki. Dole suka hakura suka tafi.
Kwanan su biyu da komawa rai yayi halinsa, mutuwar Baban ta girgiza both Aminatu da Kamal, be san mahaifin shi ba, magana ta fatar baki bata taɓa hada su sai gashi Allah ya karbi ransa a lokacin da yake da burin sanin sa.
Dole suka tattaro suka sake dawowa garin na Shagari amma wannan karon su biyu, sai Farouk da Ja’afar da suka biyo bayan su sukayi taaziyya.
Da zasu tafi kwarai Karime ta bawa Aminatu tausayi, ashe mijin ta ya rasu har tayi takaba, inda dangin mijin suka karbe dansu akan taki ta auri kanin mijin nata. Hakan ya kara wa Aminatu tausayin ta ba tare da shawara da kowa ba tasa ta haɗa kaya ta bisu saboda tana bukatar hutu sosai.
Bata ki ba, ta amsa tayin ta dan dama zaman yayi mata zafi gashi babu Inno tun da har yanzu ba’a shigar da case ɗin nasu kotu ba.
Zuwan Karime Abujan ya kasa ta dan saki jikin ta, tayi mamakin girma da Yalwar gidan da ya kasance mallakin su Aminatun, ta kuma kara karaya da lamarin shari’ar ganin ba kananan mutane innar ta tabo ba.
Duk yadda taso ta shige wa Kamal ya bata damar da zata yi masa maganar Inno yaƙi.
Safa da marwa Ya Anas ke tayi a tsakiyar falon ya gaza cewa komai. A kufule Hajiya tace’
“Wai Anas menene haka? Ka sani a gaba ka gaza cewa komai, me ya faru?”
“Hajiya Aminatu ce.”
Tabe baki tayi
“Dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce kok’i, wai har yanzu ba zaka hakura ba?”
“Hajiya hakuri ya zama dole ai, Aminatu tayi min nisa sosai, bayan haka kuma da mijin ta.”
Tashi tayi rai bace tace
“Dama rashin jin magana ne irin na dan yau, abinda na dade ina hasaso maka kenan, wahalar banza.”
“Hajiya bama wannan ba, ko da ace babu wani, zanji tsoron shiga saboda mahaifin ta ba karamin mutum bane, kina ji ana maganar Alhaji Marwan dikko?”
“Eh! Inaji, me ya faru?”
“Shine mahaifin ta.”
Da sauri ta dafe kirji
“Kana nufin uba mahaifi?”
“Eh Hajiya.”
“Na shige su ni Bintu, kasan kuwa me kake cewa?”
“Wallahi Hajiya.”
“*Hukumullah, kaji ikon Allah ko? Kai masha Allahu, amma ya akayi haka?.”
“Yadda kika ji haka yake Hajiya, ni kaina abin ya dauren kai.”
“Alhamdulillah, Allah na gode ma da babu wani abu dana taba mata, shiyasa aka ce karka wulakanta mutum wallahi.”
Murmushi yayi kawai,yana duban Hajiyan, sai ya kada kansa kawai ya bar falon, har yaje kofa tace
“Allah yasa tana da kanwa kaga sai ka shiga kawai ko dan hallacin da kayi wa yar su xasu baka, su kuma daga ka kaima ka samu wani abun.”
Sarai yaji, bece komai ba kawai ya karass barin dakin yana mamakin chanjawar Hajiyar,kudi masu gidan rana kenan.
★★★★
Cikin shirin farar shadda kal, ya dora hular jaddara, sosai ya fito a cikakken bakatsine me cike da kamala da haiba.
A gurguje ya shiga bangaren Dadah,ya gaishe ta ya sanaar da ita abinda yake shirin yi, addua tayi masa da fatan alkhairi.
Bayan mota ya fada, ya zauna sosai yana hasaso yadda xasu kwashe da ita, sai dai duk runtsi ba xai sake barin ta ba.
Sanda suka isa kadunan be ma sani ba yyi xurfi a tunani, sai da motar ta tsaya a kofar gidan sannan ya dago yana karewa unguwar kallo.