DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Oga xamu shiga ciki ne?”

“No ka tsaya anan.”

Yace yana fitowa, da kafa ya isa gate din ya tura, da Iman ya fara cin karo tana wasa a harabar gidan kan sabon keken ta. Murmushi yayi ganin ya samu weak point din gimbiyar tasa. Kai tsaye falon ya nufa, yayi knocking yana maida hannayen sa baya.
   Ta gama tattare duk ayyukan da ta yi kenan taji ana knocking, fasa shiga ciki tayi,ta nufi kofar a tunanin ta ko Iman ce ta gama wasan, turus tayi ganin shi taja ta tsaya ba tare da ta ce komai ba

“Ba zaa ce na shigo ba?”

Sai ta matsa masa,tana jingina da bango, har ya kai ya zauna bata motsa ba, sai daya sake magana sannan ta karaso ta zauna a darare.
   Hakuri ya soma bata,cikin kankan da kai ya kuma yi mata alkawarin ya chanja xai dinga xurfafa bincike kafin ya zartar da hukunci.
   Da fari taso kin bashi fuska, amma daga karshe sai ta sakko,dama chan tana son shi, kawai yadda ya rufe Ido ya wulakanta ta ne ya kasa barin zuciyar ta.
    Be baro gidan ba sai dare bayan yayi dinner cikin farin ciki da annashuwa, anan sukayi maganar komawar ta, tace ya bata lokaci, kin yarda yayi yace mata sati daya kawai ya isa tun da yanxu su ba yara bane. Dole ta amince akan babu yadda ta iya.

Dadah ya fara sanarwa yana isa, sosai tayi murna dan dama babban burin ta kenan.
  A daren ya sanar da MD, ji yake kamar lokacin xasu fara aure. Sati daya kuwa na cika aka daura auren Alhaji Kabir da Hajiya Abidah a karo na biyu. Babu wata bidia da akayi ta tare a sabo kuma tsohon gidan auren ta.


Gadan gadan aka shiga kotu bayan hankalin su ya kwanta, babu bukatar dogon zama da bincike tun da dukkan su sun amsa laifin su, adam yayi laushi sosai ya kuma gane ramin kura ba wajen bakin yaro bane, iyakar horo da wahalarwa ya shata a hannun yan sandan da ba wani isheshen imani ne da wasun su ba musamman akan mai laifi, hakan ya sashi gane kuren sa ya shiga magiya da ban hakurin da bashi da amfani.
   Aminatu duk ta damu shi yasa ta tsaya kai da fata wajen ganin Inno ta samu sassauci, kamar yadda aka gindaya wa kowannen su iya adadin shekarun da zai yi gidan kaso ko tarar kudi, kai tsaye ta hau shirye shiryen biyan kudin da aka gindaya wa Innon ba tare da sanin kowa ba.

Sati biyu

****Bangaren Farouk da Aminatu wasan buya kawai ake, sam Ammi ta hana shi ganin ta,hadaddiyar me gyaran jiki aka kawo take mata. Wani irin kyau da sheki take,santsi da kyawun fatar ta ma abin kallo ne. Ita kanta sai ta zauna tayi ta kallon kanta a mudubi, komai ya chanja a dan kankanin lokaci, haka rayuwa take dama.
   Gidan ya soma cika sosai, da yan uwa da abokan arziki. Karime da Hanne sun zo tun kwana biyu, hakan yayi mata dadi sosai, da farko sunki sakin jikin su ganin girma da haduwar gidan basu taba ganin irin shi ba ko da a mafarki ne, a hankali suka saki jikin su aka shiga hidimar bikin dasu.
  Walima kayatacciya aka yi a harabar gidan, in da aka gayyato wata babbar malama tayi fadakarwa akan zamantakewar aure.
   Washegari akayi mother’s eve, in da aka hada manyan matan kusoshi da masu fda aji na kasar nan.

A gajiye take sosai, sai dai ba zata iya ketare kiran Dadah ba, dole ta sauya kayan ta xuwa marasa nauyi ta ja hannun Karime.
    Gidan babu hayaniya sosai hakan ya basu damar isa kai tsaye bangaren Dadah. Amal ce ta amsa sallamar su, cikin sakin fuska tace

“Amarya.”

Mamaki ne ya kama Aminatun ta , zatayi magana Dadah ta fito, hannun ta, ta kama suka shige bed room. Nasiha sosai tayi mata akan rayuwa sannan ta bata kyautar sarka da yan kunne masu azabar kyau. Taji dadin kyautar, soyayyar da take mata daban ce, tun bata san kanta ba, tun tana abar kyama ta nuna mata soyayya. Bata da bakin da zata gode mata,sai dai tayi mata adduar gamawa da duniya lafiya.
   Part din mummy suka shiga, sanyayyen kamshi ne ke tashi, komai tsaf, mummy ba karamar yar gayu bace, shisa komai na falon sai da aka chanja shi, ya tafi daidai da zamani.
  
“Amarya.” Tace tana murmushi, karon farko data fara sakar mata fuska.

“Barka da dare Mummy.”

“Barka dai Aminatu, ya hidima?”

“Alhamdullah.”

“Masha Allah, ashe tafiya xakuyi? Sai jiya nake samun labari.”

Shiru Aminatu tayi ba tare da ta gane me take nufi ba. Tashi Ammin tayi ta shiga kitchen.

Harde hannun sa yayi a kofar yana kare mata kallo, jin kamar ana kallon ta yasa ta dago, da sauri Iman ta kwace daga rikon da yayi mata tayo wajen ta.

“Ummi na.”

Shafa kanta tayi tana murmushi.

“Iman, kin manta dani ko?'”

“Eh… Ina wajen Mummy, tan bani kayan dad’i.”

Murmushi tayi

“Lallai kinji daɗin ki.”

“Ummi baki gaishe da Daddy na ba.” Tace tana nuna mata shi da yake tsaye

“Zan gaishe shi ai anjima.” Tace tana basarwa

Fitowa Mummy tayi rike da tray sheke dq snacks. Kallon Farouk tayi

“Son tsaiwar me?”

Sosa Kansa yayi

“Fita ma zan yi Mummy.”

Ya juya sai ya makale a waje

“Zamu tafi Mummy.”

“Toh shikenan sai kun shigo sallama kenan?”

Murmushi tayi suka fita, da sauri yabi su, takun tafiyar sa sukaji a bayan su, Karime ta tsaya ya ƙaraso tana rike da hannun Iman, gaisawa sukayi idon sa akan Aminatun kafin suyi wata magana.

“Kuje wajen Ammi kinji dota?” Ya shafa kan ta

“Tohm Daddy.”

Tace sukayi saurin wuce Aminatu. Da sassarfa ya k’arasa gareta, yasa hannu ya jata, be tsaya ko ina ba sai a bangaren su, tura ta yayi ciki ya maida kofar ya rufe, ya jingina da jiki yana dariya kasa kasa

“Kin gama guje gujen kenan?”

“A ah.” Tace tana dariya

Matsowa yayi ya manna ta jikin sa, murya kasa ƙasa yace

“U look very beautiful, the soft skin, the perfume and everything are very nice!”

Dukan chest dinshi tayi ganin yadda yake yawo da hancin sa ko ina yana lumshe ido.

“Naughty boy.” Tace tana dariya.

“Kira ne koma mene, i just can’t hold it anymore, haba babu tausayi ne? Kalle ni fa duk na zama maraya.”

“Yafi ai.” Tace tana ture shi

“Please ki taymaka min I’m dying.”

“Ka yi hakuri Please.”

“Shikenan.” Ya janye jikin sa yana matsawa gefe alamun yaji haushi

“Akwai dama yarinyar da muka hadu a Nottingham, Dr Teema gabas, kuma ta nuna interest dinta akaina sosai, tunda baki sona zan neme ta, dama ina da contact d’inta.”

A razane ta kalle shi, zatayi magana ya juya ya shige daki da sauri,p tsaye tayi saroro cikin rashin sanin abin yi, tana tsaye Ja’afar ya shigo, a kunyan yace ta amsa gaisuwar sa, tana ganin yadda yake blushing tasan akwai wata a kasa, sai ta juya kawai ta bar part din zuciyar ta babu dad’i.

Tun da ta koma take gwada kiran sa amma wayar a kashe, dole ta hakura suka cigaba da hira dasu Karime.
  Ko da tazo kwanciya ma sai data kara kira amma a kashe, duk babu dad’i, sai ta dinga hasaso budurwar da yace, tasan tabbas me aji ce ta karshen karshe, kishi ne ya taru ya cika mata zuciya har ta kasa baccin ma.

***Sai data makara sosai, sanda ta tashi har su Karime sun gama shirin komawa, duk sai ta sake jin babu dad’i. Sukuku ta dinga yin komai har zuwa sanda zasu tafi, da kyar suka rabu bayan Ammi ta haɗa su da sha tara na arziki tun daga kan dangin sutura zuwa kudi. Sunji dadi sosai, har mota Kamal ya rakasu sannan ya kara musu da nashi. Tasha aka kai su suka tafi cikin kewar Aminatu da sabuwar rayuwar ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button