DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Alhaji kar kayi mishi illah.”
Ya fada cikin tashin hankali ganin yadda idon yaron ya kakkafe

“Barni na kashe shi, ya cancanci haka, ko ma fiye da hakan, barni dan Allah, harbe shi zanyi kowa ya huta.” Ya sake riƙe shi sosai, bugu ya fara kai masa ta ko ina, tun Farouk na kokarin kwatar kansa har jikin sa ya saki ya shiga fitar da jini ta ko ina.

Lawan da sauran ne suka shiga tsakani, ganin haka yasa Garbati da Ilu sulale wa su bar dakin suna fita suka ci karo da sojoji, a darare suka gifta su suka bar asibitin da sauri.

Ba karamin duka yayi masa ba, da kyar suka kwace su, duk da haka sai daya hankad’a shi da karfi kansa ya fashe, Amal ce tayi saurin isa wajen sa tana kuka taa dago shi.

Haki kawai Daddy yake, kamar wanda ya shiga filin daga, cikin tsananin bacin rai ya nuna shi da hannu yana kallan su Maigari.

“Maigari, Malam da sauran wanda suke wajen nan, ku zama shaida, ga shi nan, duk hukuncin da kuka yanke akansa bani da ja, kuyi masa duk abinda kuka ga dama babu ruwana, karku duba girma na, arziki na ko khakhi na, kuyi masa hukuncin daya dace daidai dashi.”

Ya dora…

“Sai dai ina neman alfarmar kowanne hukunci za’a yanke ya zama cikin kwana biyu, dan zan koma in da na fito.”

Juyawa yayi ya nufi kofar fita da sauri yana jin ba’a taba bata mishi rai irin na yau ba. Daya bayan daya suke dinga zamewa suna barin dakin ya rage sai su Inno kawai. Tashi tayi ta dago shi tana kallon fuskar sa

“Baka aikata abinda ake zargin ka dashi ba, amma me yasa ka dauki laifi me girma ka dora akan ka?”

Ta tambaya tana karantar sa.

Mik’ewa yayi yana goge bakin sa yana kallonta

“Bansani ba, bansan dalili ba. Ina ganin hakan da nayi shine kawai mafita.”

Juyawa yayi ya bar dakin Yana rangaji, Amal ta bishi da sauri tana kiran sa.

Kuka na fashe dashi, Inno ta harare ni tana zama a gefe na

“Kukan uban me kike?”

“Inno kinga fa kuka yake, duk kuma jini a jikin sa, yana da kirki sosai.”

“Toh sai akayi uban me? Ke yanzu karamar ki dake kinsan wani yana kuka, baki ji maganar da mai gari yayi ba, idan na yarda akayi miki aure idan ranar da nake jira tazo nayi yaya kenan?”

“Na’am?” Na tambaya cikin rashin gane abinda take nufi

“Manta kawai, abu daya nake so dake, idan aka tambaye ki kice ba zaki auri kowa ba, babu inda zaki matsa daga nan sai ranar da Allah ya yanke miki wahalar nan.”

Gid’a mata kai nayi ina share hawayen dake faman kaikawo a fuskata kamar an kunna fanfo.

Tashi nayi ta taimaka min na wanke fuska ta, ina zama ya shigo fuskar sa anyi dressing ya dire kayan tea ba tare da yayi magana ba ya juya ya sake fita.


A hargitse ya shiga gidan, Dada na zaune a falo tana jira shigowar sa, ganin yanayin sa yasa tasan komai ya ɓaci, be zauna ba, ya shiga kwala wa su Ja’afar kira, sai daya tara su duka sannan ya hau fada, sosai yayi musu fada sannan yace duk su shirya kaya zasu bar garin a ranar. Duk suka amsa da toh sannan ya sallame su. Zama yayi cikin kujerar falon yana zare butiran din hannun sa.

“Dadah yaron nan ya amsa laifin sa, dan yau dama ka haife shi ne baka haifi halin sa ba.”

“Yanzu menene abin yi? Kana nufin shi baban nawa ya amsa laifin?”

“Ya amsa har ma sun yanke hukuncin bashi auren ta.”

Da sauri ta tashi

“Aure kuma? Dududu Baban nawa nawa yake? Karka manta alƙawarin da kayi wa Marigayi.”

“Toh ya za’a yi Dadah, tun da yasan ya bata wa yar karamar yarinya rayuwa ai gwara a aura masa ita kawai kowa ya huta, idan yaso sai ya hakura da karatun nasa su zauna anan ɗin tunda irin rayuwar da ya zaba ma kansa kenan.”

“Amma ka tabbata shi ya aikata?”

“Nima da ina ta tunanin hakan, amma daga baya daya amince da laifin nasa kinga ai babu maganar tantama, ya aikata din”

“Kai wannan abu beyi dadi ba, amma ita yarinyar fa? Bata fadi kowa ba?”

“Kin ganta dai Dadah, karama ce sosai dan ko Amal ta fita girma da cika ido, ga kuma kauyanci da rashin wayewa, bayan haka ba’a kai ga tambayar yarinyar ba ya amsa laifin sa, kinga ai babu bukatar kuma wani dogon bincike da dai be amsa bane.”

“Toh Allah ya sauwake, amma sam banji dadin abin nan ba, amma dai ƙaddara ce dan sam ba haka halin babana yake ba kai ma ka sani, bansan dai me ya faru ba, Allah ya kara kiyaye wa.”

“Amin ya ALLAH.”

“Bari na shiga ciki, in sha Allah da an gama komai jibi zamu wuce baki daya, su yaran suyi gaba yau, nima ina da ayyukan yi da yawa, dalilin admission din farouk din ne ya shigo dani garin wallahi.”


Tafiya yake a kasa bayan ya bawa driver umarnin ya maida Amal gida, be san ina yake saka ƙafarsa ba, ya dai san kawai yana tafiya ne akan kasa, sai dai kafatanin tunanin sa ya tafi ne akan abinda ya faru a yan awannin da basu wuce ashirin ba, gaba daya rayuwar sa ta chanja, ya rasa duk wani girma da kima a idon mahaifin sa, haka Allah yake ƙaddara wa bawa ƙaddarar sa, ba tare da ya shirya ma hakan ko yayi tunanin hakan zai taba kasancewa dashi ba.

Tsaiwar babur a gaban sa ce yasa ya dakata yana kallon na kai, Garbati ke da Ilu, cikin kazamar shiga irin ta yan Iskan kauye, sigari Garbati ya busa masa a fuska yana dariya.

“Ango ango.”

“Lafiya?”

” Ita ce ta kawo hakan, ka dai ga kadan daga aikin Garbati ko?”

“Bani da lokacin tsayawa magana daku, kamar yadda ban dauke ku a cikin jerin mutane masu hankali ba.”

Da haka ya rabe ta gefen su ya wuce, yana jin Garbati na kutuntuma masa ashar, be bi ta kai ba, burin sa kawai ya isa wajen da babu kowa.
   Kansa ya haɗa da gwuiwar sa, ba zan iya fadar yanayin da yake ciki ba, zuciyar sa ta yi nauyi, ta cunkushe kamar zata budo kirjin sa ta fito, so yake yayi kuka ko zai samu sauki, sai dai babu ko digon hawaye sai na zuci da ya ka faman yi. Da fari ya so ya tabbatar da gaskiyar sa, ko dan irinsu Garbati masu halin dabbobi, sai dai furucin auren da yaji ne ya rusa komai, ba zai iya barin yarinya karama Kamar Amal ta rayu da Garbati ba, rayuwa irin ta aure me cike da tarin matsaloli, dalilin hakan yasa yayi ma kansa mugun dauri, daurin da yake tunanin har karshen rayuwar sa zai cigaba da bibiyar sa.
    Ya jima sosai a wajen, ba zai iya lissafa adadin awowin daya bata ba, ya dai mike ne kawai da niyyar zuwa gidan ko me zai faru ya faru. Sai a lokacin ya lura da irin nisan tafiyar da yayi. Har ya karasa gidan be bar fargabar haduwa da Daddy ba, ya san shi sarai yasan abin da zai iya aikatawa akan shi, abun mafi tsoro a tattare dashi shine bakin sa, baya son wata kalma ta muzantawa ta fito daga bakin sa, ba zai iya daukar hakan ba sam.
   Tura gate din yayi yaji shi a bude, a nutse ya tura kansa cikin gidan bakin sa dauke da addua, jami’an tsaron dake zube birjik a gidan ya fara cin karo dasu, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, dauke kansa yayi ya haura kofar da zata sadaka da falon gidan. A dan tsorace ya tura kofar yana tarrradin abinda zai tarar, cikin tsawa aka dakatar dashi.

“Tsaya anan!” Da sauri ya tsaya yana maida hannayen sa baya kamar me shirin arcewa.

“John!” Daddy ya bud’e murya ya kwala kira, a guje ya shigo ya tsaya gaban sa.

“Lock him up.”

Ya fada yana nuna masa Farouk dake tsaye kamar an dasa shi, yasan dama hakan zata faru.

“Yes sir!” Ya amsa da sauri ya chakumi wuyan Farouk kamar kayan wanki. Tirjiya ya fara yi yana magiya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button