DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

***Waje daya Ammi ta hade mata komai, duk abinda zata bukata ta haɗa shi a cikin jakar.
Tana kwance tayi rigingine Ammin ta leko ta kira ta, falon Daddy suka je, yana zaune daga shi sai doguwar jallabiya fara yana kallon news, remote ya dauka ya rage volume din yana duban su cikin kulawa.
“Maraba da Uwata.”
Sunne kanta tayi ta zame ta zauna a kasa tace
“Daddy ina kwana?”
“Lafiya lou mamana, ya sabon waje.”
“Alhamdulillah.”
“Toh Masha Allah, mamana abubuwa da yawa sun faru, wanda dukkan mu babu wanda ya ke da ikon hana faruwar su tunda Allah ya riga ya tsara, toh Alhamdulillah duk da haka mun gode wa Allah, dan bamu san abin da hakan ke nufi be, ina fatan komai da ya faru ya zama tarihi a wajen ki, sannan ina horon ki da ki zama me hakuri da juriya a duk yanayin rayuwar da kika riski kanki.”
“Ki riƙe addinin ki, ki riƙe mutuncin ki, ki zama uwa ta gari ga yayanki, ki girmama mijin ki,ki kiyaye dokokin Allah, ina fatan ki shiga sabuwar rayuwar ki cikin amincin da yardar Allah, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka.”
Kuka ta saka, yau ita ce a gaban mahaifin ta yake mata faɗa irin wanda iyaye ya kamata suyi wa dan su, abun da ta rasa a rayuwar ta kenan, lallai babu abinda zata ce sai godiya ga Allah, shi ya ƙaddara mata komai.
“Menene na kuka kuma? Kinji sokonta Ammi.”
Murmushi Ammin tayi dan itama zuciyar ta ta karaya, ta kuma gane dalilin kukan nata.
“Auw kema kukan zakiyi? Toh bari na gyara zama na sha kallon uwa da ‘ya suna kuka.”
Dariya ya basu gaba daya, hakan yayi masa dad’i ainun, sai ya mike yana cewa
“Bari kiga mamana, akwai sakon ki da ya kamata na baki.”
Ya shige daki, jim kadan ya fito rike da manyan files ya aje gefen sa, ya hau bude su daya bayan ɗaya, sai daya gama dubawa sannan ya mike mata
“Gashi uwata, wannan shine kyautar ki, abubuwa da kika rasa a baya ina fatan zai isa ya rufe komai.”
Hannun ta na kakkarwa ta karba ta bude, jiri ne ya soma dibar ta ganin tarin abubuwan da files ɗin suka kunsa, da sauri ta dago ya sakar mata murmushi cike da gamsar wa yace
“Karki yi tantama dama chan naki ne.
DG
*Fourty End *
“Nagode Allah ya saka da Alkhairi.”.
Tace Muryar ta na sarkewa. Murmushi yayi cikin jin dadi yace
“Allah yayi miki albarka.”
“Amin.” Suka amsa baki daya.
Daga nan gidan su Farouk ta shiga wajen Daddy, yayi mata nasiha sosai ya kuma bata kyautar kudi masu tsoka, daga nan sukayi sallama da Mummy ma, ita yar madaidaiciyar leda ta bata me kyau tace zata kira ta a waya, godia tayi ta wuce shashen Dadah, anan ta shantake ganin Ja’afar ya kuma ta kwasar ta da hira tun tana basarwa har ta saki jiki dashi, Amal na gefe bata sa musu baki sai dai tayi murmushi kawai ,Aminatu na lura da ita, tayi laushi sosai kamar ba ita ba, hakan yayi mata dadi, ko da ma chan tasan vata da matsala, kawai anyi amfani da ita ne da kuma yarintar ta.
Da kyar ta bar shashen Dadah ta wuce gida rike da Iman da ke ta faman bata labarin abubuwan da suka faru wanda ma bata tambaye ta ba, ganin surutun na neman wuce gona da iri yasa ta dakatar da ita.
A tsanake ta hau shiryawa tun da Ammi tace mata jirgin karfe biyu zasu hau, tana yi tana tunanin Farouk, bata san zai iya fushi da ita har haka ba, ita sam bata ma ga abin fushin ba, haka ta k’arasa tana ayyana yadda zasu kwashe dashi tunda dai tare zasuyi tafiyar.
Juyawa tayi ta sake kallon kanta a mudubi, shigar ta cikin ɗinkin lace white and red riga da zani yayi matukar yin kyau da dacewa da yanayin jikin ta, mayafi ta ɗora a saman red bayan ta daura dankwalin, tayi kyau ainun kamar ka sace ta, turo kofar akayi ta dakata da abinda take, Kamal ne hannun sa makale cikin dogon wandon sa, murmushi tayi ta zauna saman stool din gaban mirror tana duban sa har ya ƙaraso.
“Sis, kingan ki kuwa? Wannan ai sai ki rikita Ya Farouk din.”
“Toh sarkin tsokana.” Ta saka dariya
“Allah dagaske nake, kin fito a amaryar ki, ga angon chan a falo sai kizo muje wajen Old Woman kinsan tun dazu take zuba wa hanya ido, yau kafar ta matsa mata shisa bata fito ba.”
“Allah sarki Hajiya, muje toh.” Tace tana zura takalmin ta.
Idon ta akan sa suka fito, ya shirya tsaf cikin shigar manyan kaya da suka dace da tsari da yanayin sa, kamshin turaren sa ya gauraye ko ina na falon, idon sa akan Tv har suka gifta shi be kalle su ba, hakan ya kara sata a wani yanayi mara dadi, haka ta daure suka dangana da bangaren Hajiyan, sukayi mata sallama har da kwallar ta sannan ta fito.
A tunanin ta zata tadda shi a falon, suna shigowa ta ga wayam babu shi, sai ta zame ta zauna a saman kujerar da ya tashi, ta soma tsorata da fushin nasa, amma babu komai zata san yadda zata bullo masa dan ba zata jura ba.
Da suka tashi tafiya kowa ya fito, har gaban motar iyayen suka rako su, kowa yana musu fatan alkhairi, kasa duban kowa tayi zuciyar ta ta karye, kuka ta soma kasa ƙasa ba tare da ta bar kowa ya gane ba. Sai da driver ya kunna motar sannan ya ƙaraso wajen, yayi sallama da kowa ya fada bayan motar, sanyayan turaren sa ya cika kofar hancin ta, a dan kaikaice ya kalle ta, yayi murmushin mugunta ya maida kansa window yana duban hanya, har suka isa airport ɗin babu wanda yayi wa wani magana, shi ya fara fita ya sauke kayan su, sannan ya buɗe mata kofar yana duban chan wani waje, a kasalance ta fito tana kokarin sai ta kalle shi amma sam ya hana ta hakan, jan kayan nasu ya shiga yi ta bi bayan sa tana sake sake.
Har aka gama duk arrangements din da za’a yi bata kara ganin sa ba, sau daya ta hange shi chan suna magana da wani agent, zuwa chan jirgi ya sauka suka dunguma zuwa ciki, She’s feeling nervous saboda lokacin ta na farko kenan data tako cikin airport, jiri take ji ga wani mugun tsoro daya cika mata zuciya, daurewa tayi ta cigaba da bin sa a baya, har suka dangana da cikin jirgin zuwa lokacin tsoron ta ya dada karuwa.
Bayan sunyi settling aka yi a announcing kowa ya saka belt jirgi zai tashi, hannun ta ne ya hau rawa, yana lura da ita, tana kokarin sawa taji hannun sa saman nata, ta dago da sauri, sunkuyowa yayi daidai fuskar ta, yayi mata kallo ɗaya ya maida kansa kasa, ya daura mata belt din, sannan ya saka nasa, ya zauna sosai ya kwantar da kanta saman kafadarsa kusan rabin jikin ta na saman nashi a hankali ya furta
“Stay still matsoraciya.”
Tsit tayi kamar ruwa ya cinye ta, tayi lamo tana jin tsoron na barin ta a hankali, she feels so comfortable a yadda yayi mata, har bata san sanda jirgin ya daidai ta a sararin samaniya ba. Shi kansa ya kasa tantance yanayin da zuciya da gangar jikin sa suke ciki, be ki su zauna a haka ba.
“Ya Farouk.” Ya tsinkayi muryar ta kamar me rada a saman kunne sa, lumshe ido yayi ya buɗe ya zuba mata su
“Uhum?” Yace ya kasa buɗe bakin sa saboda yadda yake ji
“Ina zamu je?”
“Siyar dake zan, Allah sa ma zakiyi tsada.”
Shiru tayi bata kuma cewa komai ba, har zuwa sanda suka isa, hannun ta ya kama suka fito, yanayi da tsarin filin jirgin kadai ya isa ka gane ka bar Nigeria kasar mu ta gado, fararen Larabawan da suka yi wa airport ɗin ado yasa ta gane kasar da suke, bakin ta ya gaza boye farin cikin da take ciki, yau itace a birnin na Makka da take hasashe da burin zuwa, a hankali ta soma takawa a ƙasar me tsarki, tana biye dashi kamar ragumi da akala, taxi ya samar musu har zuwa masaukin da zasu sauka wanda ya riga yayi booking din sa tun kafin zuwan su kasar.
Da kallon manya manyan gine-ginen da suka kawata garin ta shagala, har bata san sun iso ba sai dayayi magana, a kunya ce ta sauko tana kara kallon ko ina cikin tsananin mamaki.
Girman hotel din kaɗai abin kallo ne, ya tsaru ta ko ina, komai tsaf tsaf kamar ka kwanta a kasa, wani a cikin ma’aikatan ne yayi musu jagoranci zuwa masaukin nasu, wanda ya kasance aljannar duniya, falo ne babba sai bed room me dauke da madaidaicin gado.
Sallah suka fara gabatarwa daga nan sukayi order abinci suka ci. Farouk ne ya fara wanka ya sauya kayan sa ya fita, hakan ya bata damar watsa ruwan ita ma, ta bi lafiyar gado tana jiran dawowar sa.
Ya jima sosai kafin ya shigo dauke da manyan ledoji, kayan da zasu bukata na dan zaman da zasuyi ya samo, da sauri ta tashi ta karbi kayan, tana yi masa sannu da zuwa.