DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sorry na barki ke kadai.”
“Ba komi.” Ta ambata a hankali.
“Gobe idan Allah ya kaimu zamu fara Umrah, saboda next week zaki ga likitan ki, so get ready.”
Yace yana wucewa daki, kwanciya yayi ya huta, ita kuma ta kunna Tv tana kalla duk kewar gida ta taso mata.
Sai da aka kira sallah sannan ya fito, da alamu ma bacci yayi, alwala kawai yayi ya fita, hakan yasa ta tashi itama ta gabatar da sallar sannan ta dan sake cin abinci ta zauna tana cigaba da kallon.
Makale da waya a kunnen sa yana magana ya shigo, zare wayar yayi ya mika mata, yana cewa
“Ammi ce.”
Da sauri ta karba ta tashi tayi ciki ya bita da kallo yana murmushi, so yake sai yayi mata horon da zata kawo kanta gareshi, gashi duk ya soma gazawa amma haka zai daure dan yaga alamar wasan zaiyi dadi, mimmikewa yayi a saman kujerar har ta dawo ta mika masa wayar sa, chan gefe ta koma ta zauna tana satar kallon shi, ranshi fes yana ta danna wayar sa yanayin fuskar sa ya nuna yana jin dadin abinds yake, sosai ranta ya sosu ganin ya share ta, tashi tayi ta wuce daki tayi shirin kwanciya kawai dan ta ga abin nashi ba na kare bane.
Anan falon yayi kwanciyar sa, tun tana sa ran shigowar sa har ta hakura ta kwanta.
Washegari suka soma Umrah, hakan ya kara haifar da nisa tsakanin su, dukkan su sun shagala wajen Ibadah musamman Aminatu da take ganin dama ce da zata bautawa Allah sosai ta kuma yi masa godiya bisa sauya sauyan da ya samu rayuwar ta.
Sati guda sukayi suna Ibadah, a ranar da suka sauke Umrah da daddare tana zaune tana duba wayar ta, gama maganar su kenan da Iman da Hajiya Turai ta zauna tana tunanin rayuwa, shigowa yayi ta bishi da ido, ya wuce kai tsaye wajen kayan su ya dauki bathrobe ya daura, ta gefe take kallon duk abinda yake yi, toilet ya fad’a ya jima a ciki yana wanka, ta lura dama yana da dadewa a toilet, tashi tayi ta fiddo masa doguwar rigar sa da boxer ta ajiye a saman gadon tayi hanyar barin dakin daidai lokacin ya turo kofar toilet din ya fito.
“Bani karamin towel.”
Yace yana k’arasa wa gaban mirror, da baya ta dawo ta dauko ta mika masa kanta a ƙasa, kin karba yayi ya zuba mata ido, material ne a jikin ta silk anyi masa ɗinkin riga doguwa me fadi daga kasa, saman ta kuma ya tsuke, yawo ya shiga yi da idanun sa, dagowa tayi da nufin sake mika masa idanun ta suka shiga cikin nasa, rage musu karfi yayi saurin yi zuwa kanana masu bayyana asirin zuciyarsa, da towel ɗin da hannun ta ya hade ya riga yana dage mata gira
“Taimaka pls, tayani rage ruwan kaina.”
Zame hannun ta tayi, ta ja masa kujera ya zauna ta saka towel din tana share masa kai, lumshe ido kawai yake yana buɗe su tana lura dashi ta mudubin
“Na gama.” Tace tana mika masa, langabe kai yayi cikin shagwabe murya yace
“Ki karasa ladan ki, get me dress ba zan iya ba.”
“Sai kace Iman?” Tasa dariya
“Eh karki manta I’m the first and last born wajen Mummy da Daddy na, dole nayi shagwaba ai”
“Soon za’a haifo twins ai,ka daina feeling kanka, bayan haka ma ai Ja’afar ne dan gaban goshin Mummy not u.”
Matso da ita yayi ta zauna saman cinyar sa, a kunne ya rada mata
“Kece zaki haifa mana twins ai, Mummy ta tsufa sai mu bata kawai, ko mu bawa Ammi daya itama daya mu karbe Iman.”
Dariya tasa tana zamewa jin ya fara chanja salon, matse ta yayi gam ya hana ta motsi, kansa na saman kafadarta ya shiga aika mata da sakonnin sa, shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, ta gaza yin komai duk ya kanainaye ta, maganganu yake mata masu dad’i da sa kwanciyar hankali, sosai hakan yayi tasiri akanta. A hankali komai ya shiga chanjawa zuwa wani bigire me cike da farin ciki da kaunar juna, it was a memorable night a wajen dukkan su, hakan ya sake haifar da shakuwa mara misaltuwa a tsakanin masoyan biyu.
Da safe suka tashi so happy and energetic, tsokanar ta yake taki kulashi, kunya da nauyin sa take ji, kasan zuciyar ta cike yake da kaunar sa, kauna me sanyi, mutunci da karamcin sa gareta abu ne me matukar muhimmanci a wajen ta, he’s the perfect husband da duk wata mace zata yi muradin samu.
Tare suka shirya suka wuce asibitin, domin ganin likitan idon nata da ya basu appointment yau, hannun su sarke da juna suka shiga asibitin, da fara’a ya karbe su, babban mutum ne dan a ƙalla zai girmi su Daddy, tests ya saka aka fara yi mata, daga karshe ya dora ta akan strong magunguna da zasu taimakawa idon wajen karo karfin ganin, kwana uku tayi tana shan magungunan suka koma, akayi mata aikin idon, cikin nasara akayi aikin aka gama, cikin hukuncin Ubangiji sai ga idon ta ya dawo ras tana ganin komai tar ba kamar da take amfani da glass ba, farin cikin da suka shiga mara misaltuwa ne, haka sukayi ta kiran mutane suna sanar musu cike da farin ciki.
Daga nan Dubai suka wuce, anan suka mori amarcin su sosai, suka yi yawon wajejen shakatawa kafin su tattaro su dawo.
Yana zaune bayan yaje sun Alhaji Marwan, yaji dadin yadda ya karbe shi sosai, ya kuma yi masa godia bisa alkhairin da yayi wa Aminatu, sannan yayi masa tayin aiki a kamfanin sa dake Kano, yaji dadi ssoai kuma ya amsa tayin babu wani dogon tunani don aiki a kamfanin sa aiki ne me kyau da tsoka, gashi kuma permanent and pensionable ne.
Ji yayi yana bukatar yaje yayi shopping saboda gobe yake sa ran shiga Kano domin ya sanar wa Hajiya labarin, tashi yayi ya sauya shigar shi zuwa kananan kaya, ya fito. Kai tsaye supermarket din daya saba siyayya ya shiga, ya wuce direct inda yasan zai samu abubuwan da yake bukata.
A daidai lokacin wata hadaddiyar beb ta turo kayan data siya tana ta mitar bata musu lokaci da wadda suke tare tayi,ji tayi tayi karo da mutum ta dago a zaton ta ameerah ce, bude idon sa yayi sosai akan ta, chubby cute little girl da ita, she looks so young and naive.
“Sorry.” Yace mata a gajarce ya raba ta gefen ta ya wuce, da kallo ta bishi, zubin sa irin na first class guys din nan, masu nutsuwa da kamala, a take taji ta kamu, kamuwa me karfi, yayi mata ???? ba karya, tana tsaye har ameerah ta karaso dauke da wani lotion da ta tsaya nema,
“Sheshe na samo shi fa, sorry nasan kin gama shaka.” Ta kama kunnen ta tana dariya alamun ban hakuri
“Karki damu,jiran yayi amfani, muje.” Ta tura bsket ɗin tana yin gaba. Cike da mamakin ta bi bayan ta, ganin sudden change a wajen Raheenat sheshe, kada kai kawai tayi ta san koma menene zata sanar mata.
A wajen biyan kudin suka sake haduwa, satar kallon juna sukayi tayi har suka gama. Tare suka fito ya shiga motar sa suma suka shiga tasu, bin su ya dinga yi a hankali har suka isa gida, sai da yaga shigar su sannan ya fito ya karasa wajen maigadi ya tambaye shi akan ta,be boye mishi komai ba ya sanar dashi komai, kai tsaye ya nemi izinin ganin mahaifin ta, lokacin yana garden din sa yana hutawa maigadi ya sanar dashi, yace ya shigo dashi
Bayan sun gaisa ya fada mishi abinda yake tafe dashi, tare da neman izinin magana da yar shi, hakan yayi wa mahaifin nata dadi kwarai, dan ba’a taba masa haka ba, yawanci sai sun gama daidai wa da yaran sannan iyaye ke samun labari.
Hakan da Anas ɗin yayi shine koyarwa addinin musulunci, idan kaga yarinya kana so ka fara neman izinin iyayen ta. Tambayoyi yayi masa masu yawa, ya kuma fuskanci abubuwa game da Anas ɗin, yaron yayi masa sosai, zai kuma so ya hada shi da Raheenatu dama ita kadai ta rage duk ya aurar da yayyenta. Waya ya daga ya kira ta yace tazo garden ta same shi, hijabi ta ɗora a saman kayan ta fita, gaban ta taji yana faduwa tun da ta doshi wajen, kamar wadda kwai ya fashe wa haka ta karasa, tana ganin shi gaban ta ya fadi, tayi saurin durkusawa a wajen cikin rawar baki tace