DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Gani Baba.”

“Yawwa auta ta, ga bakon ki nan ki kaishi wajen zaman chan sai kuyi magana ko.”

A kunyace ta amsa hakan ya kara dilmiyar da Anas cikin kogin son ta. Shi dinma kunyar yaji ya tashi da kyar yabi bayan ta, kanshi tsaye ya gabatar mata da kansa da abinda ya kawo shi, sosai ta jinjina karfin halinn sa, sai dai hakan ya kara birgeta, nauyin sa ya hanata cewa komai, sai kawai ya karbi number ta yayi mata sallama ya tafi.
  
Sanda Hajiya ta samu labarin har da taka rawar farin ciki, ga aiki me kyau ga mata, amfanin Alkhairi kenan, baya faduwa kasa banza.


Bayan shekara daya da rabi

Cikin hukuncin Allah bowayi gagara misali, abubuwa da yawa sun faru, rayuwa ta chanja komai ya cigaba da wakana da wanzuwa kamar yadda yake, sauye-sauyen da aka samu basu sa karaya ko kosawa ba, zaman lafiya kowanne bangare suke cikin so da kaunar juna, Dadah da Mummy komai ya wuce, ba zaka taba tunanin akwai wani abu daya taba faruwa tsakanin su ba, yadda take mutunta ta a da har yaso yafi haka.
   Bangaren masu laifi kuwa kowa ya girbi abinda ya shuka, a zaman gidan yarin ne Adam yayi fada da wani kasurgumin dan bashi, cikin dare kuwa ya biyo shi ya luma mishi wuka a ciki inda ya kashe shi har lahira ya kuma haka rami ya binne shi a wajen, sai da aka tsananta bincike sannan aka gano. Duk da labarin be ma kowa dadi ba, amma sun tabbata hakan shine abinda Allah ya tsara, shiyasa a rayuwa komai kayi me kyau, kuma karka biyewa rudin duniya da zuciya domin zasu kaika su baro ka. Ko babu tsufa akwai mutuwa!

Bangaren Inno tayi nadama sosai inda Aminatu da Kamal suka tsaya mata sosai suka chanja mata komai na gida da rayuwar ta sannan Aminatu ta bata jari me tsoka ta cigaba da juyawa, kasancewar ta mace me zafin nema, nan da nan ta kara bunkasa ta cigaba da juya kudin tana cire riba, duk yadda Kamal ya so share ta ya kasa,dole ya saki jiki ya ke shiga duk wani al’amuran ta,dolen sa ce shiyasa ma da auren Karime ya tashi shine akan komai, yayi uwa yayi uba ta tare a gidan sabon mijinta me kirki da yakana, ba laifi yayi karatun sa na boko dana arabi, matar sa daya suna zaune lafiya da Karimen tunda dama chan bata da matsala. Jarin itama Aminatun ta bata take yan kulle kullen ta a tsakar gida tana siyarwa.

Da bikin ya Anas ya tashi da amaryar sa Rahee da suka dade da daidaita junansu har gida ya kawo wa Aminatu ita ta wuni, ta kuma gayyace ta bikin.
   Da ya dawo daukar ta sai ya kira hajiyan sa ya aika da wayar sukayi magana da Aminatu ta bata hakuri sosai ta kuma gayyace ta bikin da za’a hada dana Ramlah, Aminatu taji dadi sosai ta kuma yi mata alkawarin zuwa idan lokacin yayi, anan sukayi exchanging number da Raheenatun da alƙawarin zata zo koyon hadaddun dishes don ita ɗin k’wararriyar chef ce.


Cikin shigar doguwar riga baka me adon pitch ta sauko, babu kowa a kasan ko ina tsaf an gyara shi, Kitchen ta nufa kai tsaye ta tarar da Baba Altine na aiki, a jikin babban freezer dake ajiye gefe guda a Kitchen din ta tsaya tana dora jakar ta a sama gami da files ɗin da  zata buƙata.

“An fito? Ina kwana?!” Baba Altine tace tana goge hannun ta da madaidaicin towel

“Barka da safiya Baba, kin ga naso makara akwai cases da yawa da ya kamata nayi clearing yau, gashi me gayya me aiki yace yana hanya yau, amma zanyi kokarin ganin na dawo da wuri.”

“Ah kice yau wajen Hajiya zan gudu maigida zai dawo.”

Dariya ta saka bayan ta gama jera abinda zata bukata akan dan karamin tray ta dauka ta wuce falo, a gaggauce ta karya tayi mata sallama ta fito, a baya ta watsa kayan hannun ta ta fada motar ta kirar Camry ja me gadi ya wangale mata gate.
   Sai data daidaita a titi sannan ta daga wayar ta dake faman reto ta sa a handfree

“Maman Iman, hala har kin fita.”

“Wallahi Anty Rahee, kinga amma da wuri zan dawo, snacks din ya zama ready ne?”

“Eh ya zama, nama yiwa oga magana ko zai biya ya aje, kinsan shi sai yace wai ba hanyar zai ba.”

“Ya Anas hoo! shikenan ki ajiye anjima Kamal ko Ja’afar wani zai zo sai ya karba. Nagode.”

Zata ajiye wayar kira ya kuma shigowa, dagawa tayi tana shan kwanar office din nata,

“Sis, kin fita ko?”.

“Na fita Amal, anything?”

“Ok zanzo gidan nida Iman, akwai maganar da nake so nayi miki ne.”

“Shikenan sai na dawo.”

Ta aje wayar, tana kashe motar, da sauri messenger ta ya iso wajen yana bude bayan motar

“Sannu da zuwa Hajiya.”

“Sannu Ila, ina fatan an yi duk abinda ya dace ko?”

“Anyi dukka, wasu mutane biyu ma da yar yarinya karama tun dazu suna zaune sunce wai wajen ki suka zo.”

“Ok.” Tace tayi hanyar office din, suna zaune rike da yarinyar suna hango ta suka tashi, da fara’a ta tarbe su, ta bude office din suka shiga ciki, ajiye komai tayi a muhallin sa kafin ta zauna ta ji me ya kawo su, duk da dama tatsuniyar gizo bata wuce koki, maganar dai daya ce kullum fyade wa kananun yara, zare glass din idon ta tayi,ta goge saman goshin ta tana duban yarinyar da dududu bata wuce 7years ba, she was raped by her own family member,kamar uncle ma yake a wajen ta..
   Rubuce rubuce tayi sannan ta kira Dr Rumaisa ta tura su domin ta duba ta sosai ta kuma bata report na damage din da aka mata before tayi proceeding further.
    Shekara guda kenan da kafa kungiyar tata me suna FAR-AM INITIATIVE (HELPING THE NEEDY AND FIGHTING AGAINST RAPE, VIOLENCE AND OTHER MARITAL ISSUES)
Alhamdulillah babu abinda zata ce sai godiyar Allah, sosai kungiyar ta samu karɓuwa ta kowanne lungu da sako na kasar nan, hakan kuma idan baku manta ba shine burin Aminatu, dan haka komai na tafiya cikin tsari, duk wanda ya kawo kukan sa wajen su suna kokarin share masa hawaye, da kanta take tsaya wa mata d a yara a kotu, ta kwato musu hakkin su ba tare da sisin su ba.

Wajen azahar ta samu barin office din, ta riga tayi wa Kamal text message na abinda take bukata na taron babban bakon nata.
   Sai zata fara watsa ruwa domin ana rana, sannan ta sauko kasan, lokacin Amal tazo, abinci taci suna dan taba hira akan wanda zai auri Amal din turad, Kitchen suka wuce saboda lokaci na ja, anan suka ci-gaba da maganar wadda Amal din kece tayi wa Farouk magana akai dan bata so damar ta sake kwace mata, so take itama tayi aure gashi har an saka bikin Kamal da Ja’afar shisa itama take so a hada da ita dan ta soma gajiya da zaman.
   Cikin kwarewa Aminatun ta shiga sarrafa hadaddiyar jollop rice me veggies, gefe guda kuma tana gasa kaza a gudar ta, sai hadin coleslow da yaji kayan hadi sosai. Kunun aya me rai da lafiya ta haɗa masa bayan ts rage aikin ta saka a freezer, (don’t mind me yunwa nake ji yasin ????????????????) duk da aikin yayi sauri saboda taimakon Baba Altine da Amal amma basu samu gamawa ba sai la’asar lis, sama ta haye da ya zama out of boundary daga ita sai chubby dinta ke rayuwa a ciki, komai yana kasa saboda haka babu wanda yake hawar mata domin fadar ta wuce ajin kowa.
  Kayan da zata saka ta ciro a wardrobe ta kunna hadadden turaren kayan data yi order a wajen Yerwa(Na Mss Xoxo) ta saka a kasan kabbasa ta shiga turara su, hatta undies da shegun nighties din da zata saka sai da komai ya dau kamshi, ajiye su tayi a saman bed ta wuce toilet domin gyara kanta, sai data fara rage pubic hair sannan ta wanke kanta da hadaddun mayukan wanke kai masu masifar kamshi, sannan ta yi wanka, ta bata kusan mintuna arba’in kafin ta fito ta jona handdryer ta hau busar da kan nata. Tana gamawa tayi oiling nasa da mayuka masu dadin kamshi sannan ta raba shi biyu tayi parking kowanne da ribbon daban.
A tsanake ta shirya kanta cikin wata ubansun half gown pink daga wajen kirjin anyi tattara da wani silk din zare, hakan ya fidda shape din wajen, sosai tayi kyau kamar yar tsana, parking din ya kara taimakawa ta fito kamar baby doll.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button