DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Hijabi babba ta ɗora a saman shigar ta,ta sauko ta tarar da Ja’afar, Kamal, Amal da Iman suna kwasar gara a saman dinning.
“Sai Anty!” Ja’afar yace yana dariya
“Anzo za’a cinye wa mijina abinci ko? Toh wallahi gwara a matso da bikin nan naku kowa ya kama gaban sa.”
“Haba wa, Madam ai ko munyi auren muna manne da gidan Ya Farouk, wannan dabge haka.”
Kamal yace yana kurbar kunun ayar da yayi sanyi sosai.
“Allah dai ya aurar damu nan kusa kawai alaji.”
Suka saka dariya baki daya, tattare warmers din da ta zuba wa ya Farouk nasa tayi ta kai sama, sannan ta dawo lokacin sun gama, sallama sukayi mata suka tafi har Iman din da ta zama ta Mummy dan sam taki basu ita har sun hakura.
Sallar magriba tayi, ta sake gyara fuskar ta ta feshe jikin ta da wasu turarrukan ta sauko ta zauna jiran zuwan sa. Ganin shirun yayi yawa yasa ta kunna Tv tana kallon shirin dadin Kowa na arewa 24, sosai ta shagala da kallon har bata ji bude gate din ba sai tsayuwar mota, kafin ta isa kofar har ya turo kofar ya shigo, da sauri ta isa gareshi, ya bude mata dukkan hannun su ta fada ciki, rumfa yayi mata ruf yana sake kankame ta.
“Welcome home chubby.”
“I missed you hayatyy.”
“Missed you more.” Tace tana zare kanta, peck tayi masa a kumatu taja hannun sa suka haye sama, a gefen gado ta zaunar dashi ta zare masa takalmin da safa ta ajiye su a wajen daya dace sannan ta dawo ta zauna a gefen sa tana masa murmushi me tsada tace
“Sannu da hanya.”
Mika yayi yana komawa baya kafin yace
“na gaji sosai wallahi.”
“Sannu, ai dole, bari kasha ruwa sai ka yi wanka zaka ji dadin jikin ka.”
Mik’ewa tayi ta kawo masa ruwa da kunun aya, ta zuba masa yasha sosai yana lumshe ido, ganin ya kusa shanye wa ne yasa ta matsar gefe ta rage masa kayan jikinsa sukayi bathroom, ita ta taimaka masa yayi wankan sannnan ta fito ta barshi ya karasa.
Bayan ya fito ya shirya cikin kaya marasa nauyi, alamun garin akwai hadari shiyasa zafin yayi yawa, sallah ya fara yi sannan ya hau kan food mat ta shiga serving dinshi.
Yana ci suna hira gwanin sha’awa, duk yawanci akan hirar inda yaje ne da kuma harkar NGO dinta. Yana gamawa ta tattare komai, ya jasu sukayi isha’a dan har an idar a masallaci lokacin an fara yayyafi kadan kadan.
A saman cinyar shi ta kwanta ya zura hannayen shi cikin gashin kanta dake fitar da wani annurin kanshi ya shiga ya mutsa shi a hankali cikin salo, hira suke gwanin sha’awar hannun su sarke da juna, a lokacin ta kawo masa maganar Amal, yace zai yi magana da Daddy, taji dadi sosai tayi addu’ar Allah ya bada sa’a, amin yace yayi kissing dinta a forehead kafin ya daga ta zuwa babbar fadar tashi data sha gyara da sabon lallausan zanin gado wanda ya dace da yanayin da masoya zasu kasance a ciki.
Da light and romantic kiss ya fara, a hankali xukatan masoyan biyu suka cika da muradin kasancewa da juna, a hankali cikin deep husky romantic voice d’insa ya kama kunne ta ya rada mata
“Ina son yanayin damina, ya kan haifar da wani yanayi me wuyar fassarawa, its all started bayan na fito daga gida, fitowar da ta zamar min abin alfahari, ƙaddara ce ta fito dani, ƙaddara me karfi da ba za’a iya ketare mata ba, abu na biyu haduwar gangar jikin mu waje guda, sanda ruwa yayi karfi a lokacin komai ya wakana, har Allah ya bamu rabon haihuwa ta sanadiyyar haka, ina ji a raina hakan zai sake kasancewa a daren yau, ina so naga wani babyn, wanda zai amsa sunan Farouk da Aminatu. Ina son ki har bansan iya yawan sa ba, I love You with all I am.”
“I love you beyond everything Ya Farouk, ka soni a lokacin da bani da abinda za’a soni, ka inganta min rayuwa ka nuna wa duniya nima zan iya, i love You chubby nah.”
“Shissh say no more, xamu yi rayuwa me inganci, tare zamuyi kuka, muyi dariya tare, I’m your best friend kema haka, we shared our sorrows and everything, for you are my eternal peace of mind, my everything, both of our hearts will be bound forever, together we will see tomorrow.”
“In Sha Allah my chu….”
Dariya yasa yana kokarin hade bakin su waje guda yace
“Soon zan fara exercise gaskiya, I want to be slim again, ta karfi da yaji an samun chubby.”
“No haka nake son ka.”
“Shikenan, Allah ya barmu tare Mrs Farouk Kabir Shagari, soon to be Captain Kabir Shagari.”
Kankame shi tayi sosai cikin jin dadi tace
“Allah ya tabbatar da Alkhairi.”
“Amin.”
Na amsa ina murmushi
Alhamdulillah ya ALLAH,ina godiya ga duk masoya ZAFAFA Biyar, na fili dana boye, Allah ya saka.da alkahiri.
Kuskuren da ke cikin littafin nan ina rokon Allah ya gafarta min. Allah ya bamu Sa’a ya biya wa kowa bukatar sa ta duniya yasa mu cika da imani.
Hafsat Rano ke cewa sai wani lokacin idan me dukka ya kaimu.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????
2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863
GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????
09032345899
Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali????????????????????????????????????????????????????????