DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Daddy please ka saurare ni, dan Allah Daddy.”

Ko gezau beyi ba, sai ma hade rai da ya sake yi yana wa John mugun kallo

“Me kake jira ne?”

Da sauri ya karasa janshi, ya fita dashi.

Tsaki Daddy ya ja ya tashi ya bar falon baki daya.

DAURIN GORO????????????????????

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????

2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863

GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????

09032345899

Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali????????????????????????????????????????????????????????
: DG

ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

    ©️Rano
                    (6)


Ina kwance ina ta kallon inno tana hada kan abubuwa da suke dakin, Nura ne ya shigo ya karba sannan ya fita dasu, kamani tayi ta lulluba min wani babban Mayafi muka fito, a hankali nake tafiya cikin wani yanayi mara dadi da ba zan iya tantancewa ba, har muka isa gaban motar da ban taba ganin irin ta ba, soja ne ya bude mana gidan baya muka shiga, ya rufe sannan muka dauke hanyar kauyen mu, kasancewar motar rufe take ruf da bakin gilashi hakan ya hana mutanen gari kallon mu, sai dai na lura duk in da muka bi sai an bimu da kallo. A kofar gida ya ajiye mu, Inno ta sake jan mayafin ta kare min fuska ta sosai ta fito dani, mata ne a tsaitsaye kowacce ta fito jin mota, da sauri Inno ta ja hannu na muka shige gida tana hararar su. Muna shiga matan gidan mu suka taso, kowa yana min sannu wadda ta kasance da biyu, daki Inno ta tura ni ta dawo wajen su tana amsa gaisuwar da suke min ta munafurci da gulma. Sun dan jima ina jiyo sautin karadin su, har suka watse, daga nan bacci ya dauke ni, ban sake sanin me yake faruwa ba.

A bangaren gidan Maigari kuwa ya aikata aka kirawo su Baba da Daddy. Inno najin hakan ta rufo ni a daki ta yafa mayafinta ta bisu, Baba be isa ya hanata ba sai dai babu yadda ya iya. Suna zuwa Daddy ma yana zuwa cikin shigar fararen kaya manya, cikin girmamawa suka gaisa gaba daya, Inno na makale a gefe tana jiran taji dalilin kiran.

“Abin da yasa na tara ku anan…”

Maigari ya soma

“Maganar da mukayi akan yaran nan, da kuma alfarmar da shi Alhaji ya nema ta a yi koma a kwana biyu, ina ganin abu daya da zamuyi wa yarmu shine aure, dan babu wani mutum a kaf kauyen nan da zai karbi auren ta, dan hakan ta taɓa faruwa a baya, a karshe saboda yadda yaran gari suka sako ita yarinyar a gaba yasa ta aikata abinda duk beyi mana dadi ba, shiyasa muka yanke hukuncin idan hakan ta sake faruwa, toh duk wanda aka tabbatar da ya aikata hakan xa’a aura masa yarinyar.”

“Gaskiya ne.” Duk suka amsa cikin gamsuwa.

“Toh yanzu Alhaji idan ka shirya, sai a gabatar da komai a nan.”

“A shirye nake ranka ya dade, duk abinda ake bukata sai a sanar dani.”

“Gaskiya ina da ja wallahi.” Maganar Inno ta katse su,

“Ina dah ja maigari, ya kamata ace a matsayi na na uwar yar nan anyi shawara dani, amma ace kawai a yanke hukuncin yi mata aure babu izini na, yarinyar da dududu nawa take, gaskiya ni ban yarda ba.”

Da tsananin mamaki suke kallon ta, babu uwa daya a kauyen nan kaf da irin hakan zata faru har ta tsaya jayayya, kamar bata san kalar wulakancin da yarinyar zata fuskanta ba?

“Menene dalilin ki, na kin abinda muka zo dashi?” Maigari ya wurgo mata tambayar

“Allah ya taimake ka, ni dai kawai bana so ne, ban yarda ayi mata aure yanzu ba, batun maganar mutane kuwa suyi tayi, zan san yadda zan ɓullo musu.”

“Kaji abinda maidakin ka tace Malam Ayubah, yar nan dai yarku ce, ku kuka haife ta, duk soyayyar da zamu nuna mata ba kamar wadda kuke yi mata ba, menene ra’ayin ka akai?”

“Ranka ya dade ni dai na amince da maganar auren, ina ganin hakan shine kawai sauki.”

Ya fada ba tare da ya kalli bangaren Inno ba, dan yasan idan ya yarda suka hada ido ba zata taba barin sa ya aikata zabin zuciyar sa ba.

“Sauran yan uwan yarinyar, shin kun amince ko kuwa?”

“Mun amince.”

“Masha Allah, toh ke sai kiyi hakuri, dama aure a hannun Iyayen maza yake.”

“Alhaji Bismillah.”

Matsowa Daddy ya sake yi ya zura hannu a aljihun sa ya ciro kudi, alama yayi wa da driver sa ya fito da sauran kayan dake booth ɗin, ganin haka yasa Inno fashewa da kuka ta yi saurin fadawa gidan mai gari. Bisa ga shaidu da wakilan kowanne bangare aka shiga gabatar da daurin auren da ya zamo tsanin farko na duk wata rayuwa da Aminatu zata taka a gaba.


Cikin dare ta kasa bacci, babu abinda take sai juyi, bata san yadda zatayi ba, idan har auren nan na nufin katanga da cikar burin ta, zata iya komai akai, duk da babu wanda yasan abinda ya faru sai mutane uku kachal a duniyar nan, amma ba zata bari damar ta ta karshe ta kwace mata ba, wanda auren nan yana nufin rugujewar komai. Har akayi asubah tana bitar abu daya, bata jira gari ya gama haske ba, ta tashi Aminatu ta bata kunu, ta ballo mata magungunan ta ta bata sannan ta dauki yar karamar purse din ta da mayafin ta, ta fice daga gidan. Tafiya me nisan gaske tsakanin kauyen nasu da wanda ke makwabtaka dasu, sanda ta isa gari yayi haske sosai, mutum daya jallin jal data san sirrin ta, sirrin da yake shirin zama tarihi idan har ta aminta da wannan auren, wajen ta tazo, dan samun mafita. Da sallama ta shiga gidan duk matan gidan suka kalle ta cike da mamakin wannan zuwan nata da sassafe haka, gaishe su tayi a tsaitsaye bata damu da irin kallon da suke mata ba ta fada dakin wadda tazo wajen ta.

“Akwai matsala kenan.” Ta fada tana kallon ta har ta ƙaraso ciki.

“Ita ce ta taso ni, ina cikin matsala wallahi harira, bansan ya zanyi ba.”

“Lallai ai naga alama, me ya faru hala? Ko dai wani abun ya samu yar mutane ne?”

“Kusan haka.” Ta cire mayafin ta ta zauna gefen gadon, sannan ta shiga bata labarin komai. Ajiyar zuciya Harira ta sauke bayan ta gama sauraron ta

“Kema dai Inno kinyi sakaci, bayan kinsan dalilinmu da kudurinmu a nan gaba, amma kikayi sakaci da yarinyar mutane har wannan abin ya faru da ita, kina ganin zasu yarda ne su kyale mu duk ranar da gaskiya ya fito? Bayan irin rikon da sukayi wa namu d’an.”

“Duk nayi dana sani wallahi, zuciya ce ta d’ebe ni, amma yanzu na gano kuskure na, ki taymaka nidai da shawarar yadda za’a yi da auren nan, idan yaran nan ya dauke ta suka bar kauyen nan kina ganin zai sake dawowa da ita ne?”

“Gaskiya dai, gashi kince an riga an daura auren.”

“An daura wallahi.”

“Toh mafita daya ce gaskiya idan zaki iya…”

“Zanyi koma menene idan akan d’ana ne.”

Murmushi harira tayi ta matso kusa da ita.


Kamar kayan wanki haka suka fito dashi, a kwana biyun da yayi duk yai baki ya rame sosai kamar ba shi ba, kauda kai Daddy yayi daga kallon sa, sun riga sun fito a shirye zasu tafi, Dada kawai za’a bari itama dan tace babu inda zata ne, gashi ba zai iya musu da ita ba. Su Ja’afar kuwa tuni suka tsufa a can sai dai Daddy ya ja musu kunne akan maganar, baya son kowa yaji har sai ya dawo da kansa zai sanar musu. Atm card ya ciro ya wurga masa, sai mukullayen gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button