DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU
by
SaNaz deeyah????

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Godiya ta tabbata ga Allah mad’aukakin sarki mai kowa mai komai daya bani ikon sake rubuta littafi a karo na 12,tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad(S.A.W).

Wagga labari dana zo maku dashi k’irk’irarren labari ne(fiction)ban rubuta shi dan cin zarafin wani ko wata ba,na rubutashi ne kawai dan na nishad’antar da duk wani masoyina

Littafin nan na sadaukar dashi gaba d’aya gareku.
MRS XERKS & SAFNAH LUV
kunfi k’arfin komai a gurina kunyi a rayuwa,ko sadaukarwar da nayi maku na novel d’ina bai isa ace ya biyaku abinda kuka min a rayuwa ba,ya Allah ya had’a fuskokinmu da alkhairi kafin mubar duniya,Allah yasa ina da rabon ganinku a rayuwata.

SAFNAH kin b’uya tunda kika haifa mana baby muka daina jinki Allah ubangiji yasa dai lafiya????

01

Yau ma kamar kullum suna zaune su biyar suna karyawa a dining area…

Janan ce ta kalli Abba tace “Abba ni kam dama ka barmu muna driving da kanmu wallahi zamu iya”

Kallonta yayi fuskarshi d’auke da murmushi yace “kiyi hak’uri Janan nafi son driver yana kaiku daga baya idan karatunku yayi nisa zan iya baku mota,ita fauziyya ma da take l2 bata yi magana ba sai ke da kike yin diploma”

“Amma Abba…..”

“Kimin shiru Janan,na gama yanke hukunci driver na jiranku a waje Idan kun gama “
Tashi yayi ya haye upstairs ya barsu.

Ran Janan a b’ace ta kalli Mameey tace “dan Allah mameey ki saka baki a maganar nan Abba ya fahimce mu,we ar matured enough ba sai ana had’a mu da driver ba”

“Dalla rufa mana baki malama,ta ina kika zama matured? a hakan?”

“Haba Yaya fahad nayi tunanin ma zaka lallab’a Abba”

“Baza’a lallab’a shi ba,sai k’arya kawai,kinfi son kina Murza kan mota kina nuna ke ‘yar wani ce?to baki isa ba,Dan ma Abba baice zai had’a ki da security ba”

Wani d’an guntun hawaye ta goge tare da fad’in “shikenan”
Tashi tayi kawai ta fice.

Mameey ta bita da ido tare da fad’in “Allah rage miki wannan zafin ran Janan”
“Zan gyara tane ki barni da ita mameey” Fahad ya fad’a rai a b’ace

Fauziyya kam babu abinda ta iya cewa dan ranta ya b’aci sosai.

       ******

“Janan fito mu tafi”
Fauziyya tayi maganar tana tsaye daga bakin k’ofa.

Janan dake tsaye jikin mirrow ta gyara d’orin d’an kwalinta ta d’au jaka”

A farfajiyar gidan ta tsaya tana kallon securities d’in,can ta hango direban tsaye jikin mota”

“Mts Ali direba ba,wallahi baka isa ba”

“Janan muyi hak’uri kawai”

“Aunty wallahi bana son naji kunya na muzanta a cikin friends”

“To ya ya muka iya?”

“Zanyi maganinsa”
Kawai tayi gaba.

Suna isa ya bud’e musu k’ofa,tsaki tayi tare da cewa “aikin banza kawai”

Ya San dashi take amma kawai ya shareta.

Sun fara tafiya a cikin mota kawai ta daka masa tsawa “dakata Malam”
Yayi saurin yin parking.

“Bani key”

Juyowa yayi ya kalleta cike da mamaki dan hatta Fauziyya sai da tayi mamakin maganar.

“Ka bani mana ka tsaya kana kallona kamar maye,wama ya sani ko mayen ne”

Mik’a mata yayi sannan ya bud’e motar ya fita,itama fitowar tayi tana masa kallon wulak’anci,”mtsw matsiyaci kawai”

Shiga tayi ta tada motar tare da watsa masa ‘ura”

“Janan kar Abba yayi fad’a”
“Karki damu Yaya fauzah na d’auki duk fad’an da dai in wulak’anta”
“To Allah ya kyauta”
“Ameen”

Sai da ta fara dire fauziyya a skul sannan ta wuce tasu.

       ********

Yana tsaye jikin mainar gidansu idonshi gaba d’aya sun kad’a sunyi jajir,duk kanin jijiyar dake fuskarshi ta fito ta bayyana,ranshi gaba d’aya a b’ace yake.

Ummi ta goge hawayen idonta tace “Yaya idan babu dama kawai a hak’ura dan bana son rasa ka kamar yadda na rasa Aunty hafsa da baba”

Umma ta kalleta ta daka mata tsawa “ki rufa min baki Ummi,me kike nufi?mu barsu suci bulus,wallahi bazai tab’a yuwuwa ba dole Aliyu ya k’watar mana ‘yancinmu,yanzu gashi nan karatunki ya tsaya tun daga aji hudu na sakandire bazai yuwu ba”

“yaya…”

“Yi shiru Ummi” ya katseta sannan ya cigaba da fad’in “zanyi iya bakin k’ok’arina dan ganin na karb’o mana ‘yancinmu”

Kai ya saka ya fice daga gidan ranshi a b’ace.

   ************

Gidansu Zuhra ya wuce dan yasan nan ne kad’ai idan yaje hankalinsa zai kwanta dan ko babu komai Zuhra ta San darajar d’an Adam tana da girmama mutane.

Zuhra fara ce kyakkyawa,tana da diri sosai doguwa ce amma ba can ba,tana da tarbiyya sannan akwaita da ilmin addini kuma mahaddaciyar qur’ani ce sai dai batayi karatun boko ba iya karta firamare skul

Aliyu na isa k’ofar gidan yasa aka kirawota.

Bata wani jima ba ta fito fuskarta d’auke da murmushi,ganin yanayinsa ne yasa itama ta daina murmushin ta k’araso inda yake
“Waya tab’a min angona?”

Kallonta kawai yake ba tare da wani sauyi ba.

“Pls ka fad’a min damuwarka”
“Kece damuwa ta”
Ya bata amsa tare da zama a dutsen da suka saba hira akai.

Zama tayi kusa dashi tare da fad’in “dan Allah ka fad’a min damuwarka wlh hankalina ya tashi”

“Zuhra na tsani Janan wlh bana ko k’aunar ganinta dama ba sonsu nake ba amma ta k’ara sa min tsanarta ji nake kamar na kasheta ita da mahaifinta da duk wani masoyinsu”

“Me?kisa fa angona”
Ta fad’a a razane tare da kallonsa,shima kallonta yake yana k’ara jin zafin a ransa.

“Wacece Janan?”

Tambayar da tayi masa ne ya sashi dawowa hayyacinsa dan bai ma San yayi wannan furucin ba.

Rasa amsar da zai bata yayi gashi ta kafa masa idanu tana jiran amsa.

“Kayi shiru”

“Wata yarinya ce tana neman raina min hankali,wai har yanzu su baffa basu gama yanke lokacin bikinmu ba?na gaji da ganinki a titi”

Cike da jin kunya tace “da amfanin gona ya fito za’ayi bikinmu kasan bikin ‘yar fari sai da Babban shiri”

Murmushi yayi sannan yace “Allah ya kaimu lokacin”
“Ameen Angona”

Haka suka zauna suna ta hira tare da tsara rayuwarsu.

       ********

Tun da maigadi ya bud’e gate ta hango Abba da Ali a tsaye.

Gabanta ya fad’i ta kalli Fauziyya tace “Aunty Fauzah wancan munafukin ya kai k’ararmu wajen Abba”

“Hmm ni kam ba ruwana wlh ke kika karb’i key dama sai da nace karki karb’a “

“Karki wani damua na d’au laifin”

Suna yin parking ta suka fito dukkansu fuskarsu d’auke da rashin gaskiya.

Suna isa Janan tace “sannu da gida Abba”

Mari ya d’auketa dashi sannan yace “bani key”
a tsawace

Mik’a masa key d’in tayi hannunta rik’e da kuncinta.

“Abba pls kayi hak’uri”

“Rufa min baki kema”
Ya sake kallon Janan yace “na soke miki driving ko kina so ko baki so Aliyu ne zai rik’a kaiki ko ina kuma ita Fauziyya zan bata mota ke kuma ke kad’ai zai rik’a kaiwa tunda baki da kunya,ke daga yau na mayar da Ali DIREBAN GIDANnan”

Kallonshi kawai take fuskarta d’auke da k’walla.

“Ku bar min gurin nan”

Da sauri fauziyya taja hannun janan suka shiga ciki.

Alk’alamin Sadeey
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by
SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

03

Lubna ce ta k’araso fuskarta d’auke da murmushi tace “ai na dad’e da sanin cewa direbanki kike so hakan ne yasa kika daina min magana na tsawon sati tun lokacin da kikaji nace zanyi soyayya dashi,Besty ma yace zaizo yaji dalilin dayasa kika daina kulani”

Ran Janan ya b’aci sosai da har baza tayi mata magana ba amma jin zafin abin yasa tace “ke kika ja na daina miki magana domin talaka da mai kud’i matsayinsu d’aya a gurin Allah,Wanda yafi wani shine wanda yafi tsoron Allah”

“Hmmm to ai saiki aureshi tunda kina tausayinsa”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button