DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ni nake da tabbas saboda an fad’a min Abba bazai muku aure ba sai kun gama masters sannan shi zai zab’a muku mijin dayaga ya dace daku,ni kuma umma tace in fito da mata nan da wata d’aya ayi bikina dan ta gaji da ganina haka babu aure, Janan na san babu yadda za’ayi Abba ya aura miki ni,bayan abinda ya faru gashi kuma ni direba ne,muna son junanmu amma dole mu hak’ura da juna”

Wani guntun hawayene ya zubo a fuskarta,tafi seconds goma kafin tace “bazamu tab’a rabuwa ba da yardar Allah please a ina zamu had’u muyi maganar?”

“A skul d’inku” ya bata amsa kai tsaye.

“Okay idan na shiga skul gobe zan kiraka”

“Allah ya kaimu”

“Ameen” ta fad’a a sanyaye.

Shi kuwa cikin murna ya ajje wayar dan ya san hak’onsa ya kusa cimma ruwa.

‘Dakin Fahad ta koma ta rok’eshi daya barta taga Fauziyya,da k’yar ya yarda ya bata key d’in d’akin sannan yace ta tabbatar ta dawo dashi.

Jikinta a sanyaye ta bud’e d’akin cikin sallama ta shiga.

Fauziyyar na kan sallaya bayanta jingine da gado.

Jiyowa tayi ta kalleta tayi murmushi “sai yau zakizo ganina ko?”

Yadda Janan taji muryar Fauziyya ta canza sai tayi matuk’ar bata tausayi.

Zama tayi kusa da ita tace “kinsan Abba yace kada a bari kowa yazo wurinki”

Kamo hannunta tayi ta rik’e wasu zafafan hawaye suka zubo a fuskarta “Janan na san Abba yana fushi dani,watak’ilma yanzu ya tsaneni ko kuma yana dana Sanin haihuwata”

Da sauri ta rufe mata baki tare da fad’in “haba dai ki daina fad’in haka kina nan a zuciyar Abba kamar yadda kike da” ta k’arasa maganar tana hawaye

“Hmmm Janan kenan na san halin Abba kuma na san tabbas yana fushi dani amma ki rok’ar min gafara gurin Mameey da Aliyu,ina ganin kamar gawata ce zata fita a d’akin nan”

“Ya salam!dan Allah ki daina furucin nan Yaya Fauzah komai fa zai wuce”

“Na sani Janan amma ina jin ciwon abinda na aikata duk da Allah ya kub’utar dani Aliyu yana da hali mai kyau amma da wani ne na san da tuni mutuncina ya zube kuma duk laifin Abba ne da Sharrin k’awa,Janan k’awa tana da mugun had’ari”

“Wacece ta baki shawarar nan?”

“Zubaida ce,amma kin san da laifin Abba”

“Abba d’an boko ne addu’a kawai zamu cigaba dayi,ita kuma Zubaida wallahi sai ta gane kurenta wato shiyasa ta dameni da kira tana tambayar ina kike”

“Ni dai fata na kowa ya yafe min zan yi k’ok’arin gyara laifina”

“Allah ya yafe mana baki d’aya”

“Ameen,yanzu ina Aliyun?”

“Kinsan Abba ya koreshi ko albashin watan nan bai ba shi ba”

“Kanga matsalar ko Janan,amma ya kamata ace ya bashi hak’k’insa”

“Abba yana da zafi sai dai muce Allah ya sassauta masa zamuyi iya bakin k’ok’arin mu dan ganin mun fitar dake daga wannan k’angin”

“Janan kenan,ni wallahi bana son fita saboda kunyar had’a ido da Mameey”

“Mameey ta san baki da laifi duk aikin shaid’an ne wannan”

“Hmmm”

“Zan tafi kada a gane ina nan,idan na samu chance zan sake zuwa”

“Shikenan Janan nagode”

“To saida safe”
“Allah ya kaimu”
“Ameen”

Jan k’ofar tayi ta rufe,ta maidawa Fahad key d’in sannan ta tafi d’akinta da Zumud’in gobe tayi su had’u da Aliyu.

Sadeey S Adam

Sadeey S Adam✍????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

21

Da sallama ta shigo gidan ta gaida Umma sannan tace “Ni kuwa amarya na nan?”

Ummi ta kalleta tace “wace Amarya kuma”

“Amaryar gidan nan mana”

“Ai bamu da Amarya mu”

“To Janan nake nufi”

“Tana d’akinta” Ummin ta fad’a tana tab’e baki.

Asabe ta wuce zuwa d’akin Janan.

“Umma kiga wani tsegumi wurin Asabe?”

“To ke ina ruwanki”

“Uhmmm”

Asabe na shiga taga Janan d’in ta tattare guri d’aya sai nishi take,k’arasawa tayi kan tabarmar ta zauna tare da d’ago Janan.

Bata abincin tayi idonta a rufe ta girgiza kai tare da fad’in “na k’oshi”

“A’a ki daure”

Da k’yar ta samu Janan d’in ta fara cin abincin,cokali uku tayi sai amai,Asabe ce ta bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ta wanke gurin.

“Ki k’arasa cin abinci Janan”

“A’a na k’oshi kaina ciwo yake”

“Rashin cin abincin da kikayi tun safe shine ya jawo miki hakan,ki daure ki k’arasa ci,sai inje in d’akko miki magani na san in kika sha cikin k’ank’anin lokaci zaki samu sauk’i insha Allahu”

Haka Janan ta daure taci abincin ba dan yana mata dad’i ba sai dan yunwar da takeji kawai.

Asabe ta koma gidanta ta jik’owa Janan magani ta kawo mata,runtse ido kawai tayi tasha.

Aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi ya d’auketa,Asabe ta gyara mata komai sannan ta fita.

Tana farkawa taji wata muguwar kasala,ga uban zuffa duk ta had’e mata jiki,kallon agogon hannunta tayi taga biyar da rabi ma ta wuce.

Tashi tayi ta zuba ruwa a bokiti ta nufi band’aki tayi wanka,duk dai a tsantsance take rayuwar gidan da k’auyen ba irin tata ba.

Sai da ta dawo d’akin ta lura babu akwatunanta sai wani guda d’aya wanda bata san meya kawo shi ba kuma bata san na waye ba.

A hankali ta taka har gurin,ta janyo ta bud’e,atamfofi ta gani ta fara d’agasu duk kansu robber ne(lagona) d’inkakku guda 5 sai Vaseline da kwalli da farar powder a gefe,sai kuma hijabai milk and black da wani takalmi irin na narkakkiyar robber wanda ake sayar dasu 500-800 shima black ne.

Abin ya matuk’ar bata mamaki dan tana d’aga kayan ta gansu tamkar an gwada ta.

“Nawa ne?hmm to ina lefen da Mameey tayi min?”

Murmushi kawai tayi lokacin data tabbatar Aliyu ne ya d’auke akwatunan ko shakka babu ta san shine.

Mai ta shafa sannan ta d’akko d’aya daga cikin atamfofin ta saka,riga da zani ne kina ganin d’inkin kin san a k’auyen aka yi shi.

Sai ta koma kamar irin wayayyiyar k’auyen nan.

Ita kanta data kalli kanta sai da tayi dariya tace “oh dubeni tamkar ‘yar k’auye,lallai soyayya kenan Allah ka karkato da hankalin mijina gareni kasa ya soni fiye da yadda nake sonshi ya kuma yafewa Abba laifin da yace yayi masa.

Haka Janan ta cigaba da fuskantar matsaloli da ban da ban daga gurin su Aliyu amma tana jure komai duka da zagi har sun zame mata jiki,akwatunanta kuwa cewa yayi ya sayar da wasu sauran kuwa Zuhra zai kaiwa lefe.

Kullum babu ranar da bazai doketa ba saboda girki ita babu abinda ta iya a irin girkinsu in ba shinkafa da taliya ba su kam tsuro mata da abu suke Wanda Sam bata sansu ba,haka zatayi yak’i ciyuwa shi kuma ya jibgeta.

Yau ta kasance Monday satinta d’aya a gidan Aliyu bata ma san wainar da ake toyawa ba a gidansu.

Tashi tayi kawai da son taje skul yau,dan haka ta shirya da wuri ta tambayeshi yace
“ban hanaki ba amma ko gwandala ta bazan baki ba kuma bance ki biya gidan kowa ba,daga makaranta ki dawo gida idan naji kin biya wani gurin ranki sai yayi mummunan b’aci”

“An gama” ta fad’a tana murmushi dan abubuwan sun zame mata jiki.

Har zata fita taji Umma tace “ina zaki je?”

Juyowa tayi ta kalleta tace “Zanje makaranta”

“Wa kike son ya miki girki?waye bawanki?”

“Zan dawo da wuri Umma”

“Babu inda zaki je”

“Umma k’yaleta taja munafurci ne ke damunta” suka juya duka suka kalli Aliyu.

“Oh kaine ka mara mata baya akan ta tafi”

“Umma ki barta kawai ai ta sani nace kartaje ko ina daga can ta dawo nan”

“Kaima ai bakayi karatu ba dan haka itama baza tayi ba”

Da k’yar Umma ta yarda Janan ta tafi,ita Janan ma har mamaki take da Aliyu ya barta.

  **********

Tun daga nesa lubna ta tsaya tana k’are mata kallo”

Tab’o Raihan tayi tace “kinga wata can tana tafiya kamar zata fad’i kuma wallahi kamar Janan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button