DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Raihan ta tashi da sauri tace “wallahi itace” duk kansu suka k’arasa gurinta da sauri.

“Ke meye hakan?” Raihan ta tambayeta.

“Kamarya?”

“Naje gidanki sau biyu baki nan wayarki kuma bata shiga”

Murmushi tayi tace “ai mun canza gida mun koma can kangire

“ina ne kuma haka?”

“Garin su Aliyu mana”

“Wannan d’an iskan?” Lubna ta fad’a tana tab’e baki.

“Mijina ne d’an iskan?”

“Haba lubna bai kamata kice haka ba” Raihan tayi maganar,tare da jan hannun Janan
“zo muje plantation akwai maganar da zamuyi”

Su ukun suka tafi,lubna da Janan suka zauna Raihan ta tsaya a tsaye ta hard’e hannu ta kalli Janan tace “duk wanda ya sanki a baya ya ganki yanzu yasan kina cikin wahala”

Zama tayi gefenta ta cigaba da fad’in “Janan kin ganki kuwa ?hijabin dake jikinki ma bai b’oye ramarki ba,kayan jikinki tamkar na masu furar bakin asibiti wanda wanki d’aya zaka musu su koma tsumma,takalmin k’afarki tamkar bathroom silifas d’inki haba Janan auren talaka hauka ne?at least ai ya kamata ki banbanta dasu ina uban kayan da Mameey ta had’a miki”

“Ya sai dasu saboda bashi da kud’i kuma nima ban hana ba kuma nina bashi da kaina”

“K’arya kike Janan ko ince k’ayar yake?akwai dalili dai dubi yadda kika zama fuskarki duk k’uraje da cizon sauro wanda da ba haka kike ba,ada fatarki smooth ce,sannan ga kuncinki nan sahun yatsu biyar bai b’ace ba,ko zaki b’oyewa kowa damuwarki bai kamata ki b’oye min ba saboda tare muka taso dake tun muna yara Janan”

Sai a lokacin yanayinta ya canza idonta duk ya cicciko ta kalli lubna tace “karku min tambayar titsiye dan Allah ni dai kawai ku tayani da addu’a Allah ya kawo min sassauci amma tabbas ina shan wahala kullum sai naci duka a gidan Aliyu”

“Mafita d’aya shine kice ya baki takardarki tun da babu dole”

“Haba lubna ki fad’i alkhairi ko kiyi shiru” Raihan ta fad’a.

“Ai gaskiya ce”

“Ina sonshi shiyasa nake jure duk wata wahala” ta fad’a lokacin da hawaye ya sauka a idonta.

“Kina da cikinsa ne?” Lubna ta sake tambaya.

“Babu abinda ya tab’a shiga tsakaninmu”

“To ni zanje in ci masa mutumci in kuma karb’ar miki takardar saki”

Mik’ewa tayi tsaye tace “karki soma lubna”

“Amma zaki iya cewa kinfi son Aliyu akan Abba?”

“Karki had’a iyaye da miji dan babu had’i”

“To in kuwa hakane kin iya banzar soyayya dan babu yadda za’ai ki cigaba da zama da Aliyu”

“Lubna kiyi shiru haka mana” Raihan ta fad’a a tsawace

“Dole in fad’a mata gaskiya”

“Shikenan”

Kallon Janan tayi tace “to Aliyu ya kai Abba kotu suna shari’a dan ranar laraba ma za’a cigaba da shari’ar”

“Me akan me?” Janan tana maganar tana kuka.

“Akan wata banzar hujjarsa,labarin yana da tsawo Janan sai mun zauna dan ko yaushe ina zuwa ina kuma jin shari’ar gaskiya Aliyu baya da mutumci”

Da sauri Janan ta juya,Raihan tayi saurin rik’ota.

“Ina zaki?”

“Gida” ta bata amsa sannan ta fuzge hannunta ta cigaba da tafiya da sauri.

Suka biyo ta a baya.

Ta inda Yarima yake zaune shi da friends d’insa ta wuce,da sauri ya tashi yasha gabanta.

“Amarya lafiya?yaushe kika shigo?me akayi miki?”
Hawayen fuskarta ta goge tana kallonsa tace “bakomai”

A lokacin su Raihan suka k’araso,ya tambayesu suka ce suma basu sani ba.

Yayi k’ok’arin binta Raihan tayi saurin wayencewa ta tsaya dashi ita kuwa Lubna ta bita.

Napep suka tara har k’ofar gidan.

Babu alamar security ko d’aya a gidan hakan ne ya tabbatar mata akwai matsala.

Tayi knocking maigadi ya fito,kallonta yayi sannan yace ”a’a Janan ce a gidan?”

“Eh ina su baita”

“Suna daga ciki” ya fad’a,taji dad’in hakan tana shiga kuwa ta gansu a farfajiyar gidan.

Da sauri kuwa baita ya taso yazo gurinta “Hajiya Janan sannu”
“Yawwa baita”
“Ciki zaki shiga?”
Tambayar ta bata mamaki ta kalleshi tace “da matsala ne?”

“Eh yace in dai kika zo karmu bari ki shigo”

“Cab wallahi dole in shiga inga halin da Abba yake ciki”

Da sauri ta wuce Lubna na biye da ita.

A falo taga ‘yan gidan gaba d’aya.

“Karki sake ki k’araso nan”
Abba ya fad’a tare da mik’ewa tsaye.

Su Fauziyya da Mameey da Fahad ma duk suka mik’e.

” Abba karka yi min haka dan Allah kayi hak’uri”

“Idan baki bar min gida ba zan tsine miki Janan dama kina cikin fushina har yanzu”

Fauziyya ta taho da sauri gurinta Abba ya tsayar da ita cikin tsawa “idan kika je gurinta sai dai ki bita kema bazaki sake rab’ata ba”

Duk kansu kuka suke,idan ka d’auke Fahad da Abba suma dai kana ganinsu kasan suna cikin damuwa matuk’a.

“Bana k’aunar k’ara ganinki har k’arshen rayuwata Janan,kece sanadi kin take umarni na idan har na mutu to tabbas ke kika kasheni Janan domin ke kika yayo mana bala’in yaron nan baya ganin darajar ni mahaifinki ne ke kuma matarshi amma haka yake zagina nida mahaifiyarki ko kunya babu kin cuceni Janan”

Kukan ta ya fito fili ta fara fad’in “na shiga uku ni Janan Abba ka yafe min in har baka yafe min ba na san wuta zan shiga,Abba na cuci kaina na cuceku dan Allah kuyi hak’uri Mameey”

Duk tabi ta rud’e sosai,rik’e ta Lubna tayi itama tana basu hak’uri tana kuka.

Abba na k’ara cewa “babu yafiya tsakanina dake sai dai hisabi Janan,ki fita kawai bana son ganinki”

Da wannan kalaman suka fito daga gidan duk Kansu suna kuka har Lubna.

Gidansu Lubna suka nufa ta zauna tana ta bata hak’uri ita da ummansu amma kuka take k’ara yi.

Idonta yayi Jajir ta kalli Lubna tace “in har ni ‘yar halak ce na bar auren Aliyu,na tsane shi bana son ko k’ara ganinshi Allah ya saka min zalunta ta da yayi,ko me Abba yayi wa. Aliyu bamu cancanci haka daga gareshi ba”

Hmmm “ba zuga ki nake ba Janan amma da kinji irin furucin da yayi wa Mameey a zama na k’arshe da saikin fi tsanarsa wallahi”

Ta goge hawayen idonta tace “ki fad’amin labarin Aliyu dan Allah ki fad’a min me Abba yayi masa?”

“Ki kad’ai kunnenki ki nutsu zan baki labarin Aliyu da kuma irin laifin da aka masa kamar yadda ya fad’a a kotu”

Shekarun baya da suka wuce….
(Labarin Aliyu)

Ku biyo ni kuji????

Sadeey S Adam✍????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

23

Daddy suka gani tsaye jikin k’ofa ransa a b’ace tamkar bai tab’ayin fara’a ba.

“Meya kawo ta gidannan?”

“Daddy Janan ce fa”

“Tun kafin kiyi wayo na san Janan dan haka ki tattara ta ta bar min gida yanzun nan sannan na datse alak’arki da ita kamar yadda na datse tawa data mahaifinta dan bazamu zauna da azzalumai ba”

“Daddy kayi hak’uri dan Allah,Abba yace ta bar masa gida kaima in ka koreta ina zataje?”

“Gidan uwaki” ya cilla mata dak’uwa ransa a b’ace ya cigaba da fad’in “ubanta ya koreta sai nine zan rik’e ta?tun kafin raina ya gama b’aci ki nuna mata hanya ta fita ta bar min gida”

Hawaye sharkaf a idon Janan haka ta tashi jikinta sai rawa yake ta rab’a ta jikin k’ofar ta wuce,da sauri Lubna ta saka mayafi zata bita daddy ya tsawatar mata yace ta zauna.

A falo Janan ta tarar da Umman Lubna a tsaye.
Kafad’arta ta dafa tace “Janan kiyi hak’uri kinji ki d’auki k’addara a duk yadda tazo miki Allah ya shige miki gaba”

Da k’yar ta iya cewa “ameen” ta wuce kawai.

Cikin kuka Lubna ke fad’in “Daddy tun tasowa ta nake tare da Janan baka tab’a rabamu ba sai yau rana d’aya zaka rabani da ita,daddy na san dani ce a halin da Janan ke ciki wallahi bazata tab’a min haka ba”

“Ki rufamin baki kafin in miki duka a gidan nan,ni bazaki fi k’arfina ba wallahi ni ba sakaran uba bane sakarai kawai” Jan k’ofar yayi ya fita ita kuma ta cigaba da kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button