DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Napep ta tara ta shiga ya kaita har k’ofar gidan Aliyu,bata ga kowa a k’ofar gidan ba hakan ne ya bata damar fad’awa gidan Asabe.

A hankali tayi sallama dan kar su Umma su jita.
“Ah ah Amarya ce a gidan namu shigo bismilla”

Duk da tasha kuka ta k’oshi amma hakan bai hanata b’oye damuwarta ba wajen k’irk’iro murmushi,d’akin suka shiga bayan sun gaisa ta kawo mata ruwa.

Cikin jindad’i tace “nagode” Jakarta ta bud’e ta fiddo dubu biyu ta mik’a mata.

Karb’a tayi tana fad’in “me za’ayi dasu?”

“Kyauta ce na baki”

Baki bud’e Asabe tace “Jaka goma fa?ina zan kaisu? a’a wallahi sunyi yawa Amarya”

“Kin cancanci fiye da haka,wallahi naso ace ma siyayya na miki amma ban samu damar haka ba,kinga tun da aka kawoni nake ajje da dubu hud’u banyi komai dasu ba sai yau ne ma na kashe 500 nayi kud’in mota ki ajje kyayi wani abu dasu karki damu”

“To nagode Allah ya Saka da alkhairi,amma idan babu damuwa zan tambayeki dan Allah”

“Karki damu indai na san amsa zan fad’a miki”

“Kowa ya ganki ya san ke ‘Yar manya ce dan Allah shin auren soyayya kukayi da Aliyu?”

“Tabbas auren soyayya mukayi”

Shiru tayi kafin tace “amma idan haka ne meyasa yake dukanki koda yaushe?sannan kowa a k’auyen nan yana son Aliyu tun sanda yazo garin nan saboda kirki,hak’uri da kawaici irin nasa amma akwai wata magana da naji d’azu wadda ta d’aure min kai”

Murmushi Janan tayi tace “karki damu bara na shiga gida dan ina dawowa nan nayo” tayi haka ne dan ta kawar da maganar.

Tashi tayi da sauri ta fito,Asabe ta biyota tana sake mata godiya.
***
Kwance ta ganshi kan katifa yana Waya,kallon daya bita dashi ne yasa tasha jinin jikinta.

Cire hijabin tayi tana k’ok’arin ajje jaka taji ya wullo mata wata tambaya “daga ina kike?”
Juyowa tayi ta kalleshi tace “kamarya?amma ai Kasan na tafi makaranta ko?”

“Sai kika biya gidan wa daga nan?”

“Ni babu inda na biya”

Cikin tsawa yace “kada ki yarda kiyi wasa da hankalina Janan”

Shiru tayi ba tare da tace komai ba,ganin yana neman ya rufeta da fad’a ne ta juya zata fita taji ya finciko ta.

Sai daya fara zabzabga mata mari sannan yayi ball da ita ta fad’i k’asa.
“Bance karki je gidanku ba?”

Kukan da ta fara ne yasa Umma da Ummi saurin shigowa kewayen dan bama su san ta dawo ba.

“Iyeee munafukar Ashe kin dawo?”

“Sai yanzu taga damar dawowa ba basarakiya”

“Umma gidansu taje dana ce karta biya ko ina”

“Ai ga irinta nan wayace ka barta taje makarantar ai sai da nace kar tayi tunda kaima bakayi ba”

“Wallahi bazata k’ara fita daga k’auyen nan ba sai ranar dana bata takardar sallama”

Umma tayi dariya tace “ai ranar tazo daga k’arshen satin nan ne in Allah ya kaimu,ai so nake a kasa ganeta amma har yanzu naga da sauranki,dalla tashi ki samo mana ruwa kuma minti biyar na baki ki dawo”

Kuka kawai take zuciyarta cike da fargaba.

“Bazaki tashi ba sai na sake miki sabon duka?” Aliyu ya fad’a.

Da sauri ta tashi jikinta na b’ari ta d’auki gyalenta dake kan tabarmar ta yafa ta fita tsakar gidan.

Fanteka ta d’auka ta fita tana goge hawaye.

Zuciyarta kawai ta raya mata ta tafi rafi ta fad’a ta mutu kowa ma ya huta da takaicinta dan gani take ita ta jefa iyayenta da kanta a wannan ibtila’in.

Tafiya kawai take zuciyarta a cunkushe da damuwa.

Tsaye take bakin rafin babu kowa kasancewar rana tayi yawa,zama tayi a gefen rafin ta zuba k’afafun a cikin ruwan tana ta addu’o’in neman gafarar Allah kafin ta fad’a kawai taji an dafa kafad’arta.

A tsorace ta juyo ta kalleshi.

“Hey” ya fad’a lokacin da yake zare bak’in glass d’in dake fuskarsa.

“Sannu” ta fad’a a tsorace.

“Nazo wuce wa na hangoki a nan,pls ko zaki iya min wani taimako?”

“Na me?”

“Calm down ba cutar ki zanyi ba naga duk kin tsorata”

Bata ce komai ba illa tsoron kawai da yake bata.

“Mom d’ina ce babu lafiya so tana son fitowa tayi amai kafin ta fito har tayi a mota so shine nake so in babu damuwa kid’an taimaka min tun da naga ke macece”

“Babu damuwa” ta fad’a a sanyaye shi kuma ya bita da kallo yana mamakin yadda ‘yan k’auye ke irin wannan wahalalliyar rayuwar dan ko dressing basu iya ba.
a zuciyarsa yake fad’a yayinda ya kafa mata ido tana d’ebo ruwa a fantekar.

“Muje ko” ta masa magana bayan ta d’ebo ruwan,gaba yayi tana binsa a baya a zuciyarta tace.

abinda zan aikata haramun ne Allah yana sona da rahama shiyasa ya turo bawanshi ya hanani fad’awa ga halaka.

Yadda taga Maman nashi a galabaice ta tausaya mata dan haka bayan ta wanke mata jiki da inda ta b’ata da amai kawai ta d’auki gorar ruwan da ta gani a gefe ta kunce zaninta,guntun maganin da Asabe ta bata ne ta zuba a ciki ta jijjiga sannan tace “Idan kika sha wannan da yardar Allah zaki samu sauk’i”

Ta kafa mata gorar tana sha kawai taji anyi baya da ita.

Da sauri ya karb’i gorar ya d’aga hannu ya kifa mata mari.

“Daga cewa ki taimaka mana sai ki bata wannan k’azantar taku,Ku matsalarku ‘yan k’auye Jahilci ya muku yawa babu wayewa ko kad’an a tare daku”

Kallonshi kawai take lokacin da wani hawayen ke k’ara tsiyaya a idanunta.

“Sai an zageku ku hau kuka sai kace Ku kukafi kowa hawaye,dalla matsa”
Ya fad’a yana kwantar da mamanshi sannan ya shiga motar ya jata da k’arfi.

Motar ta bi da ido wani sabbin hawayen na zuba a idonta.

Tafi taji daga bayanta a hankali ta juya hannunta rik’e da kuncinta.

“Shiyasa na biyoki dan inga me kike aikatawa nan ne gurin d’ibar ruwan ko?”

Girgiza kai tayi tana kuka tace “Aliyu wallahi taimakonsa yace nayi ma……..” A d’ayan kuncin ya sake marinta sannan yasa k’afa ya tad’iyeta yana fad’in “ni zaki ha’inta?k’arya kike wallahi kuma ki dawo gidan zaki sameni”

Bai kula ba da halin da take ciki ya barta anan kwance gefen titi cikin jini.

      **********

A b’angaren wannan matar kuwa sai yamma lik’is ta bud’e idonta daga baccin data samu.

Kasala kawai taji amma ciwon k’irjin da bugun zuciyar da yake damunta babu ko kad’an.

Babban abinda yafi bata mamaki shine yadda suke ta kashe kud’i daga wannan asibitin zuwa wancan amma tamkar ana k’ara mata azabar ciwo ne,sai gashi lokaci guda duk wani ciwo da take ji babu shi.

Kallon d’an nata take da yake driving tace “Muhasin mu koma wannan k’auyen”

Sai da ya juyo ya kalleta sannan ya cigaba da driving yana fad’in “momma kece kike magana haka?”

“K’warai kuwa kuma yarinyar daka mara maganin data bani shine silar warkewa ta, dan haka mu koma ka nemi yafiyarta sannan mu mata godiya”

“Momma mun kusa katsina fa,taya zamu koma wannan k’auyen sannan mu dawo mu sake d’aukar hanyar yola bayan tafiyar da mukasha tun daga Abuja pls momma kiyi hak’uri” ya fad’a,dan shi a tunaninsa maganin da tasha a Abuja ne yayi tasiri dan sam bai yarda da maganin hausa ba.

“Muhasin ina magana kana musawa?kada kaima kace kabi hanyar da ‘yan uwanka suka bi karkace kaima ka fara gajiya dani”

Parking yayi sannan ya juyo ya kalleta a tsanake yace “momma taya zan gaji dake bayan ke kika kawoni duniya,bana fatan kome na zama a rayuwa ace waini na gaji dake Allah kiyaye”

“To indai ba haka bane ina son mu koma ka bata hak’uri”

“Wallahi ko mun koma ba lallai mu ganta ba,a bakin ruwa na ganta fa taje d’iba kuma ban san ko sunanta ba ta ina zan ganta tunda babu gida a wajen?”

“Amma ai a k’auyen kusa da nan take ko?”

“Momma babu tabbas amma na san ko mun koma bazamu ganta ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button