DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Indai kana bin umarni na to mu koma”

wama ya sani ko maganin asiri ne ta bata,aini ko yanzu muka had’u da yarinyarnan in dai ba a gaban momma bane saina sake mata warning kawai zata halaka uwata da maganin k’auye yadda nake tsantsaninsu amma harta d’auki abu ta bawa uwata tasha.

“Magana nake maka Muhasin” ta katse masa tunanin.

Sadeey S Adam✍????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

Wagga shafi naki ne kyauta Mom Haidar????,ki daure ki karanta banso ki tafi strike shiyasa nasa dole Aliyu ya rangad’awa Janan saki uku????

25

inna lillahi wa inna ilaihi raji’un shine abinda ko wannensu ke fad’a.

Wata harara Umma ta zabga musu tare da fad’in “munafukan banza kawai salatin me kuke?”

Nura ne ya kalleta yace “meya faru da ita haka Umma?”

“Kai baka ga abinda tayi ba,da namiji ta dawo gidan nan fa”

Sum-Sum ya fice ya bar gidan dan yaga ran Umma ya b’aci sosai.

Asabe da Yabi suka durk’usa gabanta har lokacin kuka take a fili yanda take jin azabar ciwon na sake shigarta.

Ummi ba shiri ta shiga d’aki, tunda take bata tab’a tausayin Janan kamar yau ba.

” ‘Dagata mu tafi da ita gidanmu sai dai kome Haidar zaiyi yayi”

“A’a mu kaita chemist” Asabe tayi maganar.

“Ina mukaga wani chemist a k’auyen nan muje kawai gidan Malam Ayuba ya bata magani”

Haka kuwa sukayi suka d’agata tana kuka ta kasa ajje ko k’afar,har a lokacin jini zuba yake a k’afarta haka suka isa har gidan malamin.

Sai daya shafa mata man alayyadi a k’afar sannan yayi mata addu’oi kuma ya bata maganin da zata rik’a shafawa a gurin.

Suna fitowa daga gidan malamin cikin kuka tace “dan Allah ku kaini gidanmu”

“Ai bamu san gidanku ba Janan” Asabe tayi maganar.

Cikin kuka tace “zan nuna muku dan Allah ku muje bakin titi mu samu abin hawa”
*
Tun a k’ofar gate d’in su Yabi suka rik’a mamakin yadda Janan ta auri Aliyu bayan ta fito daga wannan tafkeken gida.

A babban falo babu kowa dan haka tace suje k’aramin falon.

Suna shiga suka tarar da Mameey da Fauziyya ne kad’ai a zaune a falon.

Da gudu fauziyya ta k’araso ta rungumeta suka fara sabon kuka.

Mameey tashi tayi ta k’araso gabanta ta rik’eta tana kallon k’afarta da har ta kumbura tayi jajir.

Gaisawa sukayi da su Asabe sannan tace su zauna.

Janan na zaune kusa da Mameey tana kuka tana fad’a mata irin azabar da ake gana mata a gidan Aliyu.

Duk kansu kuka suke hatta Asabe sai da ta koka,’yan aiki suka kawo masu ruwa da lemo.

A lokacin Fauziyya take kuka tana fad’a mata irin shari’ar da ake gudanarwa sannan Abba yace kar a fad’awa kowa har ita.

Kuka sosai Janan take gani take k’ila laifi tayiwa Allah yake jarabtarta da hakan amma wannan tsanar da Abba yayi mata tayi yawa.

Kallon Mameey tayi taga itama hawaye take,da sauri ta saka hannu tana goge mata “Mameey kiyi hak’uri karki k’ara tsinka min zuciya dan Allah” ta fad’a tana hawaye.

“Meya kawo Janan gidana?” Suka ji muryar Abba.

Da sauri Janan ta mik’e tsaye sai kuma ta zauna saboda zafin k’afarta tama manta da ciwon.

“Bance bana son ganinki tare damu ba,na yanke alak’armu dake na sallamaki a matsayin ‘yata dan haka ki bar gidan nan yanzu-yanzu”

“Yallab’ai baka da lafiya fa amma har ka jiyo muryar Janan ka fito”

“Saboda tayi min mummunan tabo shiyasa ko guri tazo sai naji jikina ba dad’i”

“Abba kayi hak’uri dan Allah, wallahi idan kana fad’in haka ji nake kamar ana sokamin wuk’a,Abba ka duba halin da nake ciki ka tausaya min”

Tari-tari yake yana fad’in “kina son kashe ni ko Janan?bana son ganinki ki daina zuwa wallahi idan na sake ganin k’afarki a gidan nan ban yafe miki ba,na haramta miki zuwa gidana”

Sunkuyawa yayi k’asa yana tari yana nunata da yatsa yana fad’in ta fita.

Kuka take tamkar zuciyarta zata tsinke haka ta bar gidan ita dasu Asabe da suka mata jagora.

     ***********

Yana zaune akan lafiyayyar kujerar ya zuba duka hannayensa ya rik’e hab’arsa.

Mommy sai fad’a take ta inda take shiga bata nan take fita ba,ya zuba ido kawai yana kallonta,ga tarin damuwa na damunsa ga fad’an Mommy ya rasa da wanne zaiji.

Maganar da tayi ne ya sashi saurin cire hannayen ya kalleta a d’an tsorace.

“Ko me zakayi saika kiramin Janan a Waya yau sai na k’ure k’aryarka,ka samu wata ka bata waya dan a tsarani ko?”

“Mommy wallahi ba k’arya nake miki ba?”

“Shiyasa nace ka kiramin ita a waya naji dalilin dayasa tace zata zo bata zo ba”

“Mommy bata k’asar an fita da ita waje bata da lafiya”

Hmmm “Jalal kenan ni zaka maida yarinya?to shima d’an uwan naka na bashi nan da wata d’aya ya dawo gida kuma ya samo mata acan inda yake karb’ar magani na gaji da ganinku a haka,ko so kuke sai na mutu banga jikokina ba”

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “Mommy please kiyi hak’uri zaki ga jikokin ki harda ‘ya’yansu insha Allah”

Hmmm “kamar da gaske”

“Dagaske nake Mommy ki kwantar da hankalinki”

“Okay ina dai jira ka kawo min Janan”

“Amma Mommy ya kamata a samo wata ‘Yar aikin dan gani nake kamar aiki yayiwa inna Abu yawa” ya kawar da maganar

“Ai ina tayata da wasu abubuwa,to me za’a kawo bayan duk kun gujeni kai ka tafi Kaduna shi ya tafi waje,Asaben ce abokiyar hira kawai”

“Mun kusa dawowa fa”

“Allah yasa”.

Ranar Mommy ta tsokano masa inda yake masa ciwo dan wuni yayi yana rik’e da agogon Janan yana tunanin ko yanzu a wane hali take?oho!.

     *********

A k’ofar gidan ta sake goge hawayen fuskarta ta kalli Asabe ” bazan shiga ba kasheni zasuyi”

“Babu abinda zasu yi miki mu shiga in kaiki”

Girgiza kai tayi tana fad’in “wlh kashe ni suke son yi”

“To ko gidanmu zata?” Yabi tayi maganar.
“Haba Yabi taya zataje gidanki bayan da mijinta,haba kinsan k’auyennan yanzu sai abin ya zama surutu”

Da k’yar suka lallab’ata ta shiga gidan.

Gidan shiru kamar babu kowa haka d’akin ma da sukaje ba kowa.

Akan katifar suka kwantar da ita sannan suka zauna suna hira saboda su mantar da ita damuwarta.

Sai la’asar lik’is suka bar gidan dan abinci ma Fura Asabe ta siyo suka dama kuma har a lokacin Aliyu bai shigo gidan ba.

Haka in zatayi alwalla kamar zatayi kuka saboda zafin ciwon in ta saka masa ruwa.

Ranar haka ta sake kwana ba tare da ta runtsa ba,ga k’afar sam ta hanata bacci Aliyu kuwa bai kwana a gidan ba dan bata ganshi ba.

Da Asuba a daddafe tayi sallah sai a lokacin bacci mai nauyi ya d’auketa.

Maganganun da taji ne ya saka ta bud’e idonta.

Ganin Aliyu tayi tare da wasu maza guda uku wanda tayi imani cewa ma’aikata ne.

Da sauri ta tashi taja mayafinta ta rufe jikinta.
Abin har ya kai Aliyu ya shigo mata d’aki da maza saboda baya kishinta.

“Yawwa ta tashi ma” Aliyu ya fad’a yana kallonta.

Kanta na k’asa dan bata san dalilin zuwan nasu ba,ji tayi ance mik’a mata takardu tare da fad’in “gashi kiyi signing”

“Signing akan me?” Tayi maganar cikin sanyin murya tana kallon Aliyun.

“A’a naga kina kallona ko baza kiyi bane?”

“Ai ban san ko na mene ba”

“Daga kotu muke,zakiyi signing sannan ki rubata Account number da Account name d’inki”

Kallon mamaki kawai ta bisu dashi,hannunta na shaking ta karb’i takardar ta rubuta tayi signing.

“Dukiyata ta dawo hannu na”
Ya fad’a yana dariya yana kallon ta.

kenan kud’in account d’inmu za’a bashi?,Dana san haka ne wallahi na wancan account d’in zan rubuta shine mai dubu 70 kacal a ciki. tayi maganar a zuciyarta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button