DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Fita sukayi ta zauna kawai tana zulumi tana tunanin ko meya faru a kotu yau?,ita dai gabanta fad’uwa yake.

       ********

Suna fitowa daga kotu Abba ya zube.

Da sauri suka rufar masa duka suna kuka,da k’yar suka sakashi a mota zuwa asibiti.

Kai tsaye emergency aka nufa dashi dan ya fita hayyacinsa tamkar ya mutu.

Cikin ikon Allah likitoci suka samo kanshi.

6 hours later

Yana kwance akan gadon idonsa na kallon silin,Mameey na zaune gefen gadon yayinda Fahad da Fauziyya ke tsaye a jikin gadon.

Har lokacin suna cikin damuwa Fauziyya kuwa kuka kawai take.

Kallonsu yayi cikin k’arfin hali yace “karku damu akwai Allah kuma yana kallon duk abinda ke faruwa kuma ya sani ban zalunci kowa ba amma an zalunceni,duka gidana da nashi an had’a an bashi saboda kawai ba’a ga inda aka binne dukiyarsu ba sai ace komai bamu an basu, sannan an dakatar dani daga aiki ba tare da hak’k’ina ba duk irin ruk’on aikina amma ace wai ban san aikina ba”

Tari ne ya sark’e masa,Fahad ya rik’oshi yana fad’in “Abba dan Allah ka cire komai a ranka”

Ya kalleshi lokacin tarin ya lafa yace “Fahad bazan iya cirewa ba,kaima na ja maka matsala a gurin aikinka sun k’wace mana komai hatta kud’in dake account d’in mu sun karb’a duk wani kadararmu sun karb’e wannan wace irin shari’a ce?wane irin bahagon hukuncine,da kayan sawa kad’ai aka barmu Fahad” kuka sosai Abba yake suma suna kuka.

Turo k’ofar da aka yi ne yasa duka suka kalli wajen.

A fusace Fahad ya taso yana fad’in “me kazo kayi mana anan?”

Murmushi yayi yana fad’in “kwantar da hankalinka ba zama ya kawo ni ba”

Zai k’ara magana Abba yayi saurin d’aga masa hannu alamar yayi shiru.

Taku biyu Aliyu yayi ya k’arasa jikin gadon “sannu ko” yayi dariya ‘yar kad’an sannan ya juya ya kalli Mameey.

“Kin gani ko haka Allah yake ikonsa,yau gani nine mai arzik’in,duk wani abinda kuke tak’ama dashi babu,kin san me?zuwa nayi na baku sadaka dan a samu a sayi magani kuma ‘yarki zan mayar da ita k’ask’antacciyar baiwa a gidana”

” ‘karya kake matsiyaci wallahi har yanzu bakayi arzik’in da zaka wulak’antamu ba” Fauziyya ta fad’a a fusace.

“Hahahahh keee! Har kin samu kanki kenan? ‘Yar iska mai bin maza”

Hannu ta d’aga zata wankeshi da mari yayi saurin rik’ewa “kul! Karki kuskura ki fara” ya wurgar da hannunta gefe sannan ya juya ya sake kallon Mameey ya fiddo bandir na dubu ya wurga mata yace “ayi kud’in magani”

Wani damk’a da Fahad ya kai masa ne yaja kaurewar fad’a tsakaninsu,da sauri Mameey ta fara k’ok’arin rabasu Aliyu ya kai mata duka a fuska ta dad’i,da gudu Fauziyya ta fita neman taimako,Abba ya tashi shima jiri ya d’ebeshi ya fad’i.

Da k’yar wasu likitoci suka shigo suka raba fad’an,Aka kama Mameey aka bata gado itama.

Abba kuwa aka Saka mashi oxygen saboda numfashinsa baya fita da kyau.

Aliyu na shigowa gida ya rufe Janan da duka,ta fito k’ofar gida da gudu ya biyota yana duka,mutane na rik’eshi yana fad’in a sakeshi ya illatata.

Mutanen gurin kuwa sukace a k’yaleshi ai matarsa ce,ita kuwa da gudu ta fad’a gidan Asabe,yana neman shigowa tayi saurin maida k’ofar ta rufe tare da zubewa k’asa.
Sai a lokacin taji zugi a k’afarta dan har ta manta da ciwon saboda wawan dukan da yayi mata,gannin jini a k’afarta ne yasa ta k’walla ihu a take ta sume a gurin,a haka Asabe tazo ta ganta.

    ******

Tana farfad’owa ta ganta a kwance kan gadon Asabe.

Asabe na mata fifita Zuhra na gefenta tayi tagumi.

“Inna Asabe kinga ta bud’e idanunta”

Kallon ta tayi tana hamdala,da sauri ta tashi ta kawo mata ruwa.

Bata ma karb’a ba illa kuka da take tayi dan ta gama tsinkewa da lamarin.

Ganin kukan yayi yawa ne yasa Zuhra ta fara magana rai a b’ace.
“Wai ke Janan hawayenki baya k’arewa ne?akan me zaki zauna Haidar yana neman kashe ki?”

Bata iya cewa komai ba sai kukanta daya k’aru.

Asabe tayi Ajiyar zuciya tace “ni wallahi na rasa rashin tausayi irin na mahaifiyarsa ita take zugashi”

“Wallahi na auri Aliyu ita bata isa ta saka ya dokeni na kasa ramawa a kanta ba,duk uwar mijin data kasa rik’e mutumci ta sai ka hau ka taka,ke Janan wallahi dole ki dokasu a kotu a raba aurenku ki huta”

Sai a lokacin ta fara magana tana fad’in “idan na kai Aliyu kotu ya sakeni ina zan koma?babana ya koreni in aka raba mana aure da Aliyu bani da inda zani”

“Baki da dangi ne?”

“Muna dasu amma kinsan dangi na yanzu ba wani zumunci ake ba babu wanda zai saurareni bamu had’uwa sai in har wata sabga ta had’a da kamar wuya yanzu in tunkaresu da matsala ta su karb’a”

“To gaskiya kije ayi miki tsakani dasu a kotu ina dalili,dubi yadda kika koma fa,wanda ya dad’e bai ganki ba bazai shaidaki ba”.

     **********

Ganin yadda yake neman sark’ewa yasa Mameey ta tashi da sauri zata fita kiran likita.

Hijabinta ya rik’e yace ” karki kira kowa”

“Meyasa?” Ta tambaya tana kuka.

“Saboda mutuwa zanyi” ya fad’a yana murmushi sannan ya saka hannu a aljihun wondonsa ya d’akko takarda ya mik’a mata.

“Ki bawa Janan wannan,ki fad’awa Fahad da Fauziyya na yafe musu suma su yafe min,sannan dan Allah karki raba kan ‘ya’yana duk runtsi duk wahala ki zauna dasu ki k’ara musu darasi akan zaman duniya”

“Yallab’ai dan Allah ka daina fad’ar haka,ita mutuwa ko wanda yake lafiya k’alau tana d’auka”

“Baki san irin azabar da nake ji ba ni kad’ai na san yadda nake ji”

Ranar dai haka Abba ya rik’a shan azaba bai ma san wake kansa ba,k’arfe 11 na dare Allah yayi masa rasuwa.
(wayyo Allah tashin hankali wanda ba’a sa masa rana,karkuso kuga yadda Mameey ta rik’a suma tamkar itama bazata rayu ba).

Kafin safiya dubban mutane sun jin labarin mutuwar Alh Hashim,wasu suna Allah wadarai da hukuncin da aka masa a kotu wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa wasu kuma suna cewa alhakin Aliyu ne.

A gidan mak’ocinsa aka yi masa sutura, wanda yake side d’insa, Alhaji Ibrahim yana aiki a wani babban kamfanin saida motoci mutum ne mai karamci,side d’aya ya warewa su Mameey suka zauna zaman makoki tunda gidansu an k’wace musu.

Kwana biyu da rasuwar Abba Mameey tace su tafi su bar garin bata son zama duk da ana ta zuwa ta’aziyya ta dai fad’awa matan gidan ta wakiltasu su karb’i ta’aziyyar Abba.

Babu yadda Alh Ibrahim baiyi ba akan su zauna amma tace a’a duk da dai bata jindad’i kuma bama ta san ina zasu nufa ba.

Haka suka had’a duk kayansu na amfani suka tari taxi da sassafe suka tafi suna mai yiwa iyalan Alh Ibrahim godiya akan karamci da suka musu,sannan ta bawa haj kaltume uwar gidan takardar da Abba ya bada tace idan Janan tazo a bata a kuma bata hak’uri akan abinda ya faru.

Duk wannan abin da ake daga Janan har Aliyu babu wanda ya san wainar da ake toyawa dan a kwanaki biyun babu inda ya fita.

Janan kuwa dama daga d’aki sai band’aki saboda k’afarta ba lafiya bakuma ta jindad’i a kwanaki biyun nan.

Ranar da Aliyu ya fita ganin gidan yana son ya tsara yadda zasu zauna a ranar yaga mutane a k’ofar gidan mak’ocin Abba,koda ya tambaya sai aka ce masa Alh Hashim ne ya rasu yau kwana uku kenan kuma iyalansa sun bar garin.

Bai samu damar shiga gidan ba saboda yadda yaga mutane na masa gani-gani,babu shiri ya dawo k’auyen gaba d’aya jikinsa ya mutu duk da yana ganin hak’k’insu ya kashe Abba ya bi Hafsa da baba.

A tsakar gida ya tarar da Umma tana ta fito da kaya tana sakawa a bakko.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button