DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ya akai? ka kawo mai motar da zamu tafin?”

“Umma a bari sai gobe kinga yanzu yamma ta kusa”

“To a wane dalili kasan tafiyar ba yau ba kasa muke ta had’a kaya tun safe,to wallahi baka isa ba”

“Umma naga bama su kwashe komai ba,kayan d’aki da sauransu”

“Tunda kaga sun bari ai namu ne an hutar da kai siyan wasu”

Ganin ranta ya b’aci sosai yasa yace “to Ku shirya bayan sallar magriba zamu tafi”

“Allah ya kaimu” ta fad’a tana cigaba da had’a kayan.

Shi kuma ya wuce kewayensa.

A zaune ya tarar da ita tayi uban tagumi da duka hannunta biyu.

Tunda ya aureta bata tab’a bashi tausayi kamar yau ba,yana so ya fad’a mata rasuwar Abba amma ya kasa saboda da ciwo ace mahaifinta an kaishi har kuma kwana uku bata ganshi ba bataji labarin rasuwarsa ba.
the same abinda ya faru dani ya fad’a a zuciyarsa.

“Ki shirya zamu bar garin nan mu koma Kaduna yau”

Gabanta yayi mummunan fad’uwa idonta ya ciko da hawaye tace “kana nufin gidanmu?ina su Abba suka koma?”

“Ba cewa nayi kimin tambaya ba umarni ne na baki” ya fad’a a dake,dan ji yake kamar yayi mata kuka.

Sauri yayi ya fita ya bar mata d’akin.

Ana yin sallah kuwa ya shigo yace su fito ,haka ta janyo trolley d’inta tana d’angasa k’afarta, fad’uwar gabanta ya tsananta.

A k’ofar gida ta had’u da Asabe “saura ki yada zumunci Amarya”

“Insha Allah zan rik’a ziyartarki bazan tab’a mantawa dake a rayuwata ba”

“Ki yawaita addu’a duk inda kike kuma a duk inda kika tsinci kanki karki manta addu’a”

“Insha Allah”

Wasu magunguna ta mik’o mata k’ulli biyu tace “wannan mai maik’on kina shafawa a ciwon,shi kuma na garin maganin na duk wani ciwo ne,ki kula da kanki,Allah ya kiyaye hanya ya kuma tsare ki”

“Ameen nagode sosai” ta fad’a ta d’aure maganin a zanenta

“Karki damu” Asabe ta fad’a cikin damuwa.

Duk abinda sukeyi Aliyu yana tsaye jikin motar yana kallon ta.

Su Umma da Ummi na fitowa tayi saurin zuwa ta shiga motar suka tafi.

A motar ma babu abinda Umma keyi sai habaici da zagin Janan tamkar wata sa’arta,ita kuwa tayi shiru tama rasa me yake mata dad’i.

Tun daga nesa ta hango canopy taji gabanta yayi mummunan fad’uwa duk da ba a k’ofar gidansu bane.

A zuciyarta tace to ko mamansu bilkisu ta rasu ne dama ba cikakkiyar lafiyane da ita ba.

Suna tsayawa a k’ofar gate d’in gidan ta kasa fitowa,wai gidansu ne ya zama mallakin Aliyu,gani take tamkar a mafarki.

“To ki fito mana ‘yar dad’i mota” Ummi tayi maganar tana yatsina fuska.

Jikinta a sanyaye ta fito tana k’ara kallon rumfunan da aka kafa a k’ofar gidan Alh Ibrahim.

Hasken lights d’in daya cika layin ne yasa Baita ya hangota, da sauri ya taso ya taho,lokacin ana sauke kayansu a mota.

Yana zuwa gabanta ya fashe da kuka.

Ita duk a tunaninta ko korar Abba daga gidan ne ya sakashi kuka dan haka tace “Baita pls ka bar kukan nan”

Cikin kuka yace “Janan wallahi ban san Abba ya rasu ba sai yau d’innan bamuyi adalci ba amma kuma ba laifinmu bane office aka ce dole sai mun koma”

Tunda ya fara maganar Janan ta saki baki tana kallonshi bata ma fahimtar me yake fad’a sosai.

Aliyu sadda kai k’asa kawai yayi yayinda Umma da Ummi ke mamaki.

“Wa…..wan…wane Abba?” Ta fad’a bakinta na karkarwa.

Jin haka ne ya sakashi yin shiru dan tunda yaji haka ya san bata san mutuwar ba.

Wuyan rigarsa ta shak’a tace “Abbana?wallahi k’arya kake yana raye bai mutu ba”

Dariya tayi irin ta zautattun nan sannan ta sake shi ta b’ata rai,sai kuma ta ruga da gudu ta fad’a gidan Alh Ibrahim d’in ta manta ma da ciwon k’afarta.

Sadeey S Adam✍????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

‘Kawata Amarya Khadija,a gaskiya abinda kika zo min dashi yau bazan iya musulta farin cikin danaji ba,har na cire ran zan samu saboda yadda nasha nema na rasa,ashe abin yana ranki har sai da kika samomin,zazzafar k’auna ce wannan,na yarda ke mai k’auna ta ce,fatana Allah ya saka miki da gidan aljanna ya biya miki dukkanin buk’atunki ya k’ara dank’on k’auna tsakaninki da maigidanki,ya k’ara dank’on zumunci tsakaninmu.
Nagode matuk'a

26

A babban falon gidan ta tsaya tana zazzare ido tana kallon mutanen dake zaune.

A hankali ta fara ganin ko ina yana juya mata,cikin kuka ta furta “Mameey kina ina?ki fito ki fad’a min gaskiya Abba na san bai mutu ba” sai kuma ta rik’e gashinta ta sulale k’asa.

Salati aka hau yi,haj Mariya tayi saurin zuwa suka kamata aka yi d’akin bilkisu da ita.

Few minutes ago

Idanunta ta bud’e gaba d’aya tana kallon mutanen dake kanta.

Wani k’ara data k’walla sai daya gigitasu dukansu.

Ta mik’e tana neman ta ruga sukayi saurin rik’e ta,wani fizgewa da tayi Alh Ibrahim shi kad’ai ya iya rik’eta gam,aka kira likita yayi mata allurar bacci.

Idonta k’yar akan likitan har bacci ya d’auketa.

Kallon Alh Ibrahim yayi yace “tana neman rasa tunaninta fa ya kamata ana kwantar mata hankali”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,ya Allah ka bamu ikon ceto rayuwar yarinyar nan”

“Ameen” haj Mariya ta fad’a cikin damuwa.

Sallama sukayi da doctor ya rubuta wasu magungunan da zata samu relief sai kuma na ciwon k’afar tata,sannan yace zaizo washe gari ya cire mata bandajin goshin nata.

     *******

“Wai meke damunka Aliyu?naga duk kabi ka shiga damuwa akan waccan banzar yarinyar”

Ajiyar zuciya yayi yace “Umma wallahi ina mamakin rasuwar mahaifin Janan”

Mtsssw taja tsaki cikin b’acin rai tace “to ko shine Alh Rabe iya abinda zakayi kenan,mutumin daya kashe maka mahaifi da mata har ka ji tausayinsa,ai yanzu lokaci ne daya kamata ace muna farin ciki”

Shi dai bai ce komai ba illa kanshi kawai daya dafe “ina son dama kazo ka nunnuna mana abubuwan da bamu Sani ba,sannan kana sane da cewar wani satin za’a d’aura aurenku da Zuhra ko?”

Baice komai ba kawai tashi yayi yana fad’in “muje na nuna muku” ta lura dashi sarai akan damuwar daya sakama kanshi amma sai ta shareshi kawai.

     *******

Janan sai da tayi sati guda tana hauka-hauka sannan Allah ya bata sauk’in abin.

Yanzu ma tana zaune kamar ko yaushe tana ta kuka ,Bilkisu na gefenta tana bata hak’uri.

Haj Mariya ce tayi sallama ta shigo “Janan kukan ne har yanzu”

Zama tayi kusa da ita ta dafa kafad’arta tace “Janan Abbanki addu’a yake buk’ata ba kuka ba,ki Sani wannan kukan da kike yi kina saka masa rad’ad’i ne”

Cikin kuka tace “ina kukan takaicine,nabi son zuciya nayi abinda mahaifina baya so Ashe ajalinsa na janyo masa,ina dana sanin k’in bin maganarsa da nayi gashi har ya rasu bai bud’i baki yace Janan na yafe miki ba,sannan su Mameey sun tafi ban san ina suka shiga ba,taya bazan yi kuka ba,ku barni inyi dan Allah”

“Kiyi hak’uri Janan haka Allah ya k’addara”

“Ban san k’addarar mutuwar Abba da rashin su Mam……….” Da sauri Bilkisu ta rufe mata baki tana fad’in “kina addu’a Janan”

Jiki a sanyaye haj Mariya ta mik’a mata takardar tace “gashi inji Mameey tace Abba ne yace a baki”

Karb’ar takardar tayi ta kwanta ta cigaba da kuka,su kuma suka tashi suka fita dan ta samu damar karantawa a nutse.

Sai da tayi kuka sosai ta samu nutsuwa sannan ta ware takardar ta fara karantawa.

Zuwa gareki ‘Yata Jannah.
Na san bazaki riski wannan takarda ba har sai na koma ga Allah, lokacin da zaki karanta na san zaki karantane kina mai zubda hawaye tare da nadamar k’untata min da kika yi na auren wanda ba zab’ina ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button