DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Janan duk da na san bakya jin magana amma ban d’auki abinda kika yi a komai ba sai k’addara kuma babu yadda muka iya da hukuncin Allah.

Janan ina mutuk’ar son ki ban tab’a jin sonki ya ragu a raina ba,ku uku Allah ya bani dan haka nafi son Ku fiye da komai a rayuwata,duk ranar da nayi muku wani abu kukaji haushi a ranar bana runtsawa saboda yadda nake jinku a raina yafi k’arfin wasa amma ina dannewa ne saboda in muku tarbiyya mai kyau bana son na sangartaku.

ko da kikaga ina korarki idan kinzo gida dan in hukuntaki akan laifin da kika yi ne,daga ke har Mameeyn naki na san baku tab’a hango abinda na hango muku ba,ba wai ina k’yamar talaka ba a’a ina gudun irin cin mutumci nasu da zarar ka mayar dasu inuwa,bance ko wane talaka haka yake ba,ban kuma ce daga yanzu Ku rik’a k’yamar talaka ba,a’a ina son kuyi bincike sosai akan duk abinda kuka saka a gaba.

Sannan ina son sanar dake cewar Salman bai mutu ba,nace miki ya mutu ne saboda in fitar dake daga damuwar da kika shiga kuma in mantar dake shi,tabbas Salman mutumin kirki ne Janan, dan ko dana rabaku dashi bai tab’a min koda kuwa kallon banza ba har ya bar garinnan,na hanaki aurenshi ne saboda baya da asali Janan amma ki Sani Aliyu yayi min babbar illa,sannan ni ban san inda dukiyarshi take a gidana ba saboda ban san inda aka sare bishiyar da yake fad’a ba,gadonku yana hannunsa idan har ya cinye muku Allah bazai barshi ba,sannan ki k’ara sanar masa ina nan ina jiran ranar da zamu tsaya ni dashi a mana hisabi dan ban yafe masa ba.

Ina son ki nemi gidan wani Malam Lado a cikin katsina yake a wata unguwar filin samji yake kice masa yayi miki kwatancen gidan wani wanda ake kira da Alto sarkin gini a cikin garin Nijar ban san wane gari bane,in kikaje mutumin ko bai biyoki ba zai fad’a miki inda bishiyar da suka sare take don shine da yaransa sukayi aikin gidan duka,ban fad’awa kowa ba koda a kotu domin na san shari’ar ha’inci aka yi ban fad’awa kosu Fahad ba ke na zab’a na kuma fad’a miki kije ki farauto muku ‘yancinku ki amso muku dukiyarku Janan kena wakilta dan haka tafiya ta kamaki da zarar kinga sak’on nan karki zauna.

daga k’arshe ina muku fatan Alkhairi a sauran rayuwarku,ina fatan zaku cigaba da rayuwa cikin jindad’i da amincin Allah, na yafe miki duniya da lahira nima ki yafe min ‘yata.

Kuka har sark’e mata ya rik’a yi,tanayi ta magana tana fad’in “baka min komai ba Abba na yafe maka Abba”

Kasancewar gidan babbane suma basu jiyo kukanta har tayi ta gama ta kwanta lamo tanayin kukan zuci.

Shigowar Alh Ibrahim ce yasa ta d’ago kanta tana hawaye.

” ‘yata kukan ya isa haka,mahaifinki kowa ya shaida shi mutumin kirki ne,har aka kaishi makwancinsa mutane suna kukan rashin adali,yana kwance cikin jindad’i amma ke kina d’aga masa hankali,kina son ya rik’a jin azaba da rad’ad’in kukan da kike masa”
Ta girgiza kai tana goge hawayen wani na k’ara zubowa.

“Abu d’aya zaki masa wanda zaiji dad’i ya kuma san ya haihu shine addu’a karkiyi wasa da yi masa addu’a kinji” ta d’aga kai alamar to.

Haka ya cigaba da mata nasiha cikin rarrashi.

      ********

Da sallama ta tura k’ofar d’akin ta shiga.
“Dama Umma tace kina nan kina kuka” Raihan ta fad’a lokacin da ta k’araso jikin gadon ta zauna.

Wasu sabbin hawaye ne suka fito daga fuskar Lubna ta saka hannu ta goge sannan ta fara magana.
“Dole duk ranar dana tuno Janan nayi kuma,ke! na san Janan bazata tab’a gogewa a zuciyata ba”

“Hakane Lubna wallahi ni kaina ina jin Janan a cikin jinina lokacin guda na shak’u da ita yanzu haka Ummina fad’a take min akan meyasa ban kawota suka cigaba da zama a gidanmu tunda Akwai extra rooms”

Lubna na hawaye tace “nifa saboda Janan daddy ya hanani fita ko ina dan kar inje gidansu,wallahi ina dana sanin barin Janan tayi soyayya da Aliyu,Ashe ba alkhairi bane shiyasa har mukayi fad’a da ita a kanshi,tunda yarinta muke tare da Janan tare mukayi primary, secondary skul sannan muna tare a high institution ma amma ace rana d’aya na barta ta barni,saboda Janan bata da lafiya nak’i cigaba da karatu har sai data warke muka fara poly tare amma ace yau an rabamu mahaifina ya mana tsakani da ita” kuka sosai take Raihan ta rumgumeta tana rarrashi.

Turo k’ofar da aka yi ne yasa Raihan ta juya tace “kinga Umma kukan take”

“Aini har na gaji da kukan Lubna ki rarrasheta dai ke k’ila taji maganarki”
Fita tayi taja musu k’ofar.

“Lubna dan Allah ki bar kukan nan”

“Dole inyi kuka Raihan,Abba ya rasu ban je musu gaisuwa ba gashi ance sun bar garin ya zanyi”

Hmmm “hak’uri mana Allah ya Sani ba da gangan mukayi ba,nima ban san rasuwar Abba ba sai jiya kuma yau ina zuwa na tarar wai Aliyu ne a gidan,dana fito na tambayi wani a waje sai yace sun bar garin kuma bai san inda suka koma ba”

“Kinji fa,gaskiya Aliyu azzalumine Raihan wallahi sai yanzu na k’ara dana sanin k’in fad’awa Jalal da mukayi na san da yayi wani taimako”

“Hakane gaskiya bamu kyauta ba,jiya ma munyi waya dashi ya tambayeni tana zuwa skul nace masa eh ni ban san ta ina zan fara masa bayani ba,amma yace min sai upper week zai shigo Kaduna”

“Idan ya shigo kawai mu sanar dashi dan k’aryar ba inda zata kaimu”

“Yawwa credentials d’in Janan komai da komai yana hannunki ko?”

“Eh”

“Ki bani in na shiga skul gobe zanje in mata deferring dan bana son ta rasa karatunta”

“Amma Raihan meyasa bazaki bari muga yadda Allah zaiyi ba ko zata dawo”

Hmmm “Lubna mun kusa fara exam yaushe kike tunanin zata iya covering bayan tana cikin damuwa koda ta dawo d’in ma kawai ki bani wannan itace hanya mafi sauk’i”

Tashi tayi a sanyaye ta d’akko mata ta bata,sukayi sallama ta tafi.

       ********

Yana kwance yana juyi akan makeken gadon Abba wanda a yanzu ya zama mallakinsa.

Hankalinsa gaba d’aya a tashe yake,yau satinsa biyu kenan bai saka Janan a idonsa ba,bai tab’a tunanin ta shiga ransa ba sai yanzu da bata gabanshi, da kuwa gani yake kawai ya tsaneta baya son ganinta amma yanzu babu abinda yake son gani sama da ita.

Yaje gidan Alh Ibrahim har sau biyu amma ko farfajiyar gidan maigadi ya hanashi shiga bare ya samu ganin Janan.

Shi unguwarma ta ishesa babu wanda yake mu’amala dashi kowa ya tsaneshi,ko a masallaci mutane basa musabaha dashi.

Kodan ansan shi ada Direban gidan ne shiyasa suke masa gani-gani.

ni kuwa komai zai faru ba zan bar gidan gadonmu ba saboda anan na girma,in basuyi mu’amala dani ba wasu zasuyi. ya fad’a a zuciyarsa.

Ummi ce ta turo k’ofar cikin sallama ta shigo ta zauna.

“Lafiya?” Ya fad’a yana kallon ta.

“Yaushe zan koma makaranta kuma Umma tace zaka koya mana mota tunda akwai motoci”

“Bazan koya miki ba yarinya tun kafin ki waye har kinsan k’arya” ya fad’a rai a b’ace.

Tashi tayi tana turje-turje ta fita.

Sai gata sun dawo da Umma.
“To mara kunya naji sak’onka”

Tashi yayi zaune yace “Umma wane k’aryar taje ta fad’a miki”

“Maganar koya mota dole ne a koya mata itama”

“Umma…..”

“Rufamin baki kabi Umarnina kawai”

Knocking suka ji ana tayi dan haka duka sukayo waje dan sunsan babu wanda zai nemesu to waye haka?.

Yana bud’e k’ofar idonsa ya dira akan nata,gabanshi har fad’uwa yayi yadda yaga idanun nata kamar sun juye.

“Ohh kece kika dawo” Umma ta fad’a tana k’ok’arin fitowa.

Bata ma kalleta ba kawai tace “ba dawo wa nayi ba nazo karb’ar takardata ne”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button