DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ina nufin ka sake ni Aliyu” ta fad’a idanunta a cikin nasa.

“Kinzo a dai-dai gab’ar daya dace,dama saki ai ko baki nema ba zai miki shi dan haka na baka damar ka sake ta saki uku a take anan”

Ya kasa d’auke idonsa akan Janan sannan ya kasa magana.

“Ka saketa nace”

“Umma bazan iya ba,idan na saki Janan ina ganin babu adalci a lamarin”

“K’arya kake Aliyu” Janan ta fad’a tana nuna shi da yatsa tana k’ara fad’in “dole ka sake ni wallahi kai baka isa kayi min illa ba kuma in cigaba da zama da kai,har yaushe kasan adalci ai baka da adalci kai azzalumi ne” ta k’arasa maganar tana kuka.

Umma ta kalleshi cike da mamaki tace “ince ka saketa amma kana ce min bazaka iya ba”

“Kiyi hak’uri Umma bazan iya sakinta ba”

Sakin baki Ummi tayi tana mamakin yayan nata,Umma kuwa k’ara fad’i take wallahi sai ya saki Janan yana fad’in bazai iya ba.

Cikin matsanancin kuka tace “kayi shari’a da mahaifina kaci galaba to ka sani a wannan karon ni zanci galaba zamu tsaya gaban alk’ali da kai dole ne ka sake ni, ka jira sammaci daga kotu”

Da sauri ta juya ta tafi tana cigaba da kukan tare da k’udiri da yawa a kanta.

Sadeey S Adam✍????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

Fatima Muhammad Ali,sak’onki ya iso gareni da farko dai ina amsa gaisuwarki kuma nagode sosai nima ina sonki da yawa nagode da fatan alkhairi da kika min,kuma nima ina miki fatan alkhairi a duk inda kike????

‘yan group na TASKAR SANAZ dana MRS OMAR da sauran groups dake bibiyar novel d’ina nagode sosai????

29

Muhasin haka ya koma yola ya d’ebowa Momma kayan sakawa,sannan ya siyowa Janan kaya ita ma.

Ya koma yola shi, sai dai duk k’arshen sati yana zuwa kaduna duba su yana mutuk’ar tausayin Janan d’in.

    ******

Hawayen daya kasa mak’alewa ne ya samu damar sauka a kuncinsa.

Kallon Raihan yayi ya girgiza kai sannan ya tashi yana neman tafiya tayi saurin cewa “dan Allah Jalal ka tsaya kaji”

“Me zan ji bayan abinda na gama ji yanzu”

“Amma ya kama ta ka saurare ni”

“Lokaci na k’ure min Raihan nafi so naje na kai cigiyar su a kafafan yad’a labarai tun kafin suyi nisa”

“Dan Allah kada ka Ka kai tunda ba b’ata sukayi ba”

“Ni a gurina sun b’ata ne”

“Bazasu ji dad’i ba ina ganin kamar tozarci ne”

Zama yayi yace “to ya kike so nayi?”

“Hak’uri da kuma addu’a”

“Amma meyasa kika min haka Raihan?meyasa tun abin yana d’anye baku fad’amin ba sai da bakin alk’alami ya bushe”

Shiru tayi kawai itama zuciyarta na k’una.

“Ina son Janan kuma na fara sonta had’uwata ta farko da ita,har Janan tayi Aure ban tab’a jin sonta ya ragu a zuciyata ba,na danne kawai saboda na san tayi min nisa,amma meyasa zaku k’i sanar dani halin da take ciki bayan kunsan ita d’in jinin jikina ce”

“So kuma?” Ta fad’a lokacin da ta kasa b’oye damuwarta.

“Eh so da kika sani”

Wani irin kishin Janan taji duk da bata kusa da ita.

Allah ya k’ara nisantar da Janan yasa karta ji sha’awar dawowa Kaduna ta fad’a a zuciyarta yayinda ta rik’a jin haushin kanta da tayi mata differing.

“Ki min alk’awari Raihan” ta tsinkayi maganarsa kamar daga sama.

“Ina jin ka”

“Dan Allah ina son ki tayani addu’a Allah ya dawo min da Janan a cikin kwanakin nan”

“Insha Allah”

“Nagode! Yanzu zanje gidan su Lubna”

“Zan raka ka”

“A’a kiyi zamanki ba kince lecture zaku shiga ba”

Shiru tayi shi kuma yayi tafiyarsa.
*
Suna zaune a falon gidansu Lubna.

Ta sunkuyaar da kanta kawai tana kuka dan da taji maganar Janan sai tayi hawaye.

“Ki daina kukan ya isa haka”

‘Dago kai tayi ta kalleshi tace “wallahi tun sanda na ganka da Janan na san kunyi mugun dacewa amma yadda Janan ta d’auki son Aliyu ta lik’awa zuciyarta shiyasa kawai na kasa furtawa,mun maka laifi amma kayi hak’uri”

“Bakomai fatana Allah ya dawo mana dasu lafiya”

“Ameen” ta amsa tana goge hawayen fuskarta.

      ********

Bayan wata guda

Suna tsaye jikin mota,Muhasin na gefe tare da doctor yana masa bayani akan magungunan da za’a saya.

Jikinta duk yayi sanyi saboda sam bata k’aunar k’ara had’uwa da Aliyu.

Momma ta gane hakan,dan haka ta janyo hannunta tace “karki damu Janan ki rik’a kwantar da hankalinki kinji”

Kai kawai ta d’aga,Muhasin ya dawo ya shiga motar suka tafi.

Sai da suka fara zuwa k’aton chemists suka siya magungunan sannan momma tace Janan tayi musu kwatancen gidan.

Har k’ofar gidan sukaje a bud’e ma k’ofar take dan haka suka kutsa kai suka shiga.

A k’ofar Babban falo sukayi knocking, sun d’an juma kafin a bud’e k’ofar.

Ummi ce ta fito tana kallon su a shek’e.

Kamar bazata matsa ba sai kuma kawai ta matsa tace “Ku shigo”

Bayan sun zazzauna ita kuma Ummi ta haye sama.

Sai jin muryar Umma sukayi tana fad’in “uban me ta dawo yi gidannan?”

Duk Kansu suka kalli gurin.
Tana gaba Aliyu da Ummi na biye da ita.

“Tashi ki fita matsiyaciya” ta fara fuzgar Janan.
Momma tayi saurin cewa “baiwar Allah dakata mana”

Juyowa tayi tana fad’in “ke kuma a suwa”

“Dakata iya haka kada ki yarda kici mutuncin uwata ba tare da kinsan matsayinmu ba”

Sai kuma tayi shiru,shi kuma ya kalli Aliyu ya cigaba da fad’in “dama munzo mu sanar da kai matarka na d’auke da cikinka ba wani abu muke buk’ata ba kawai ina son kasan akwai jininka ko nan gaba”

“Karya kuke wallahi, mu zakuyi wa d’anmu sharri”

Ta juya ta kalli Aliyu tace “ko gaskiya ne?”

Jikinsa a sanyaye ya girgiza kai.
“Naga kayi sanyi?” Umma ta k’ara tuhumarshi.

idan ban k’aryata hakan ba tabbas komai zai iya faruwa.

Cikin d’aga murya yace “a gidan ubanwa zaki d’ebo cikin shege ki lik’a min”

Janan da tun lokacin da aka fara maganar ta sunkuyar da kanta tana kuka sai a lokacin ta d’agoshi ta kalli Aliyu
“Kaji tsoron Allah ka fad’i gaskiya karka shegantamin d’a Aliyu dan Allah ka fitar dani daga zargi”

“Dalla rufamin baki tanan kika b’ullo kuma?to wallahi ranki zaiyi mummunan b’aci idan har kika cigaba da kiran shegen cikinki a matsayin nawa danni ban tab’a had’a shimfid’a dake ba”

Muhasin ya kalleshi yace “ka yarda muje kotu kuyi li’ani?”

“Muyi mana wayake tsoro” ya mayar cikin b’acin rai.

Momma kuwa sai doka salati take tana hawaye.

Janan ta mik’e tsaye cikin kuka tace “ba sai anyi ba saboda bani da tabbas amma ni na san cikinka ne,amma ka sani ko wata rana kada ka nemi d’anka, ka k’addara baka da d’a dani”

“Dama ai babu,dalla ki fita bana son ganinki”

Da sauri ta wuce ta fita,Momma ta sake kallonsu kawai ta fashe da kuka tace “Allah ya saka miki Janan”

Muhasin kuwa kasa cewa komai yayi saboda yadda zuciyarsa ke tafasa komai zai Iya faruwa.

A farfajiyar gidan jiri ya d’auki Janan ta zube.

Masoya sai kun yi min hak’uri dan kwana biyun nan ina busy, kuyi manage da wannan

Sadeey S Adam

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17

Leave a Reply

Back to top button