DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Karku damu zan taho”
Lubna tayi maganar.

Ali kam sakin jiki yayi yana hira da lubna dan ya San Janan tana jin haushin hakan.

Suna zaune bayan Janan ta gama yiwa Raihan narrating duk abinda ya faru.

Murmushi Raihan tayi sannan tace “yana da kyau ki bashi hak’uri saboda kema bazaki so a zagi naki ba,ban San yaushe kika koyi wulak’anci ba Janan da ba haka kike ba”

“Wallahi yanzun ma ba haka nake ba,kawai dai na tsaneshi saboda yayi min sanadin hanani driving”

“Ba dad’i amma kiyi hak’uri kuma ki bashi hak’uri tunda har kikaga yayi kuka tabbas baiji dad’i ba”

“Amma kuma bana son ya rainani”
“Bazai rainaki ba durk’usawa wada ba gajiyawa bane Janan”
“Shikenan nagode da shawararki insha Allah dayazo d’aukana zan bashi hak’uri”

Tun k’arfe biyu take tsaye tana jiranshi shiru babu alamun shi.

Waya ta d’aga zata kira kawai taji kiran Fahad ya shigo.
Da sauri ta d’aga tana fad’in “wai ina sakaran direban nan bayan nace masa k’arfe d’aya zan gama lecture gashi har biyu ta wuce”

Daga d’ayan b’angaren Fahad yace “marainin wayon naki bayanan saiki fad’an Inda kike zanzo na d’auke ki”

Gabanta yayi mummunan fad’uwa ba dai da gaske ya ajje driving d’in ba
“Kin min shiru ko bakiji ne”
“Ina k’ofar library” ta fad’a a sanyaye.

“Ya dai lafiya?”
Lubna ta fad’an tana kallonta.

“Wai bayanan Yaya Fahad ne zaizo d’aukana”

“Oh my god,shikenan yau bazan ganshi ba,naso na sake ganin kyakykyawar fuskarshi gaskiya ban tab’a ganin kyakykyawan namiji kamar Aliyu ba,ina son shi matuk’a”

“What?so fa?”
“Eh”
“Wane so bayan akwai engaged a kanki da Besty ko kin manta?” Janan ta fad’a cikin b’acin rai

“Na sani”
“Kin daina son Bestyn?”
“Kamar ya bayan har an mana baiko”
“To su biyu zaki aura ne?”
“Ya kike min tambaya kamar ‘yar jarida?”
“Dole na miki saboda kin bani mamaki wallahi”

Dariya tayi tace “kin San dai bazan tab’a auren direba ba barema direbanki,kawai ina son soyayya dashi ne saboda in fita kunyar friends dama ace yana da kud’i zan iya barin muktar na aureshi amma in rasa wazan aura sai direba”

“Amma kuma zakiyi soyayya dashi”

“Eh direba baya da wani value ai”

Cike da mamaki Janan ke kallonta dan batayi tunanin haka daga bakin lubna ba.

“Baya da value fa kika ce?shi ba mutum bane ko ba Allah ne ya hallicce shi ba?”

“Shi mutum ne amma talaka baya da daraja a waj…………”

“Dakata lubna” Janan tayi saurin katseta.

“Na tsani a wulak’anta d’an Adam”

“Ai ba wulak’anta shi nayi ba,ina son shi amma bada aure ba”

“Kina son yaudarar zuciyarshi,lubna karki cutar da d’an Adam baki San lokacin da zai miki rana ba”

“Amma kuma ke kike wulak’anta shi?”

“Laifi yayi min amma ni ban tsaneshi ba kuma banji dad’in abinda kikai ba”

“Oho dai nikam sai anjima” da sauri ta bar gurin.

Tana tsaye tana tunani har Yaya fahad ya k’araso,da sauri taje ta bud’e gaban mota ta shiga dan ta San halinsa da fad’a.

Suna cikin tafiya ta kasa daurewa tace “Yaya kamar ma daga office kake?”
“Eh”
“Ina drivern yake”
“Oho ni dai kawai mameey tace in biyo in taho dake”

Bata ji dad’i ba dan har ta fara zargin kanta amma ba damar ta fad’a ma fahad.

Har suka isa gida yana ta surutu amma amsar da take bashi bata wuce um ko um um.

Suna zuwa gida ta shige bedrum ba tare da tayima kowa magana ba.

Tana kwance kan gado kusan minti talatin tana tunanin Ali meyasa ma tayi masa haka.

Tashi tayi zaune ta d’an ja tsoki tare da fad’in akan me zan damu kaina?idan ya rasa aikin shi yayiwa Kansa

Cire kayanta tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta shirya ta fito falo..

“Mameey Aunty Fauzah bata dawo ba?”

“Eh sai six”
“Okay bara naje gun Abba muyi hira”
Bata jira amsar mameey ba ta wuce side d’in daddy.

Sati guda babu Ali ba labarinsa dan kullum Fahad ko Fauzah ne ke kaita skul tana son tambayar ko lafiya amma ta kasa tunda babu Wanda yayi mata zancensa ko Fauzah da take tunanin zata fad’a mata wani abu game da rashin zuwansa.

Yau kam bayan sun fito daga lecture ta kalli Raihan tace “yau sati guda Ali baya zuwa tun ranar Dana fad’a miki na zageshi”

“To ke meya dameki?”

“Dole in damu Raihan,wallahi kusan kullum da abin nake kwana a raina”

“Son shi har yayi girma haka a zuciyarki”

Da sauri suka juya dan ganin mai maganar.

Alk’alamin Sadeey
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

04

“Meye abin b’oye shi ai idan kana son abu kana nuna shi ga kowa ne”

Ran janan a b’ace tace “lubna meyasa kike min irin wannan?”

Murmushi tayi sannan tace “oh sorry na zo zan takura miki ko?ina ji ina gani kina neman yi min k’wacen Aliyu ai ba k’arya nayi ba kina sonshi”

A hargitse ta shak’o wuyanta tace “ina son shi sai me?”

“Sakarmin wuya ko in tara miki jama’a”

Ganin duk mutane sun tsaya suna kallonsu ya sa ta sake ta tare da fad’in “ba haramun bane soyayya dashi?to zanyi soyayya dashi kuma zan aure shi”

Tsaki taja tayi saurin wucewa ta bar gurin saboda kar tayi kuka gashi mutane sun fara ihu da hayaniya.

Saida ta tsaya a gurin da babu mutane sosai sannan tasha kukanta ta k’oshi sannan ta goge hawayenta ta nufi department d’insu.

Ranar bata yiwa kowa magana ba har suka kammala lectures, Raihan tayi-tayi ta fad’a mata abinda ke damunta amma tak’i fad’a,itama lubna bata yi mata magana ba bare su kaure da fad’a.

Babu wanda tayi wa magana a cikinsu haka ta kama hanya ta tafi.
A bakin main gate ta tsaya ta kirashi bai dad’e ba sai gashi yazo.

Kamar yadda ya saba haka ya fito da da sauri ya bud’e mata k’ofar baya.

Kallonshi kawai tayi ta matsa ta bud’e murfin seat d’in gaba ta shiga ta zauna.

Yafi minti 1 a tsaye bai shigo ba ita kuma tayi banza ta k’yaleshi dan tasan mamaki yake.

Sai daya gama tsayuwarsa sannan ya shigo ya zauna.

“Dan Allah kiyi hak’uri ki koma baya”

Kallon tsiwa tayi masa tace “daga yanzu nan zan rik’a zama”

Hannunsa ya d’ora kan sitiyari ya saki ajiyar zuciya yace “nan ba hurumin ki bane,baki dace da nan ba,karki manta ni direbanki………….”

“Shhhhhh” tayi saurin katse shi,tare da yin wannin sassanyan murmushi “Kai ba direba na bane,saboda ina son duniya ta sani ina sonka kuma zan aureka,kaga sai aji dad’in kaini gidan radio ace na auri direba na,ina son dan Allah ka amince dani bazan tab’a cutarka ba”

Cire key d’in motar yayi tare da mik’a mata.
“Me kake nufi da hakan?”
“Ina nufin ki karb’a ki ja motar zan wuce gida dan naga abinda kike buk’ata kenan”

“Kamar ya?Aliyu karka bani kunya pls”

“Dakata Janan,kada ki maida ni k’aramin yaro kada kiga dan ina direbanki ki nemi wulak’antani,dan Allah ki fita ki koma baya,bazan iya soyayya dake ba dan bakya tsarin matan da nake so”

Bata san lokacin da hawaye ya fara zuba a idonta ba.

“Aliyu tunda nake a rayuwata ban tab’a cewa ina son wani d’a namiji ba,hasalima idan akace ana sona bana amincewa so d’aya na tab’a soyayya kuma ta wahalar dani banyi tunanin zan sake ba amma hakan har ya zama laifi kana kallon tsabar idona kana wulak’anta ni”

“Ko zaki sake bada Aliyu ba,bana sonki kuma bazanyi soyayya dake ba ki daina ma wannan maganar ina ke ina direba,kin manta irin maganganun da kike fad’a a kaina ne”

“Wallahi baka isa ba ko kana so ko baka so dole kayi soyayya dani,gwanda ma kaso”

Da sauri ta bud’e murfin motar ta fita ta koma seat d’in baya ta kwanta tana hawaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button