DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Shima baice komai ba,haka yaja motar cike da mamakinta ganin abin yake tamkar a mafarki.

Yana yin parking tayi saurin d’aukar jakarta ta fita.
Ya bita da kallo,cije leb’e yayi yana murmushi yace “kin d’ebo ruwan dazai k’ona ki”.

Janan kuwa tana zuwa falo taci karo da mameey,k’arasawa tayi kan kujerar ta zauna ta rufe fuskarta da mayafi tana shashshek’ar kuka.

” Waya tab’oki ko keda Raihan d’in ne?”

Kai ta girgiza alamar a’a.

“To mene?kin shigo kina kuka ai sai ki saka in tsorata nayi tunanin ko wani abu ne ya faru”

Cigaba tayi da kukan kamar ana tunzura ta.
Mameey tayi banza ta k’yaleta saboda ta mata yin duniya tak’i fad’ar abinda ke damunta,daga k’arshe ma tashi tayi ta bar mata falon.

A b’angaren Ali kuma yana yin parking ya bawa maigadin key ya tafi.
Har ya isa gidansu yana tunanin abubuwan da suka fito daga bakin Janan yana jin maganar tamkar ba gaskiya ba.

A tsakar gida ya tarar da Ummi na wanki umma kuma tana gaban murhu tana fifita wuta.

“Yaya barka da zuwa”
“Yawwa Ummi sannu da aiki”
Gurin umma ya k’arasa ya durk’usa ya gaida ta ta amsa cike da fara’a.

Shiru yayi baice komai ba har saida tace “lafiya Aliyu?”
Kai ya sosa yayi murmushi sannan yace “babu komai umma”

“Karka b’oye min komai Aliyu ka fad’an gaskiya”

Labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da Janan ya fad’a mata.

“Alhamdulillah ya Allah nagode maka daka karb’i addu’ata na dad’e ina jiran wannan rana”
Ta fad’a tana goge hawaye.

Ummi dake wanki ta k’araso gurin tace “Yaya yanzu ya za’ayi”
“Sai abinda umma tace”

‘Dago kai tayi idonta yayi jajir tace “ka amince mata,ka cusa mata kanka yadda babu wani mahaluk’i da zai iya rabaku daga zarar ka aureta a sannan ne zamu fara d’aukar fansa,karkayi wasa Aliyu inaso ace cikin wata uku anyi bikinku”

Sai dayaji gabanshi ya fad’i dan duk duniya yafi tsanar Janan da babanta fiye da danginta kuma yanzu ace wai yayi soyayya da ita har da aure.
“Ko bazaka iya bin umarni na bane?”
Umma ta katseshi.
“A’a ina tunanin yadda Zuhra da iyayenta zasu kalleni”

“Karka damu zuhra itace matarka ta dindindin in har ina raye,ita waccan ai da mun karb’i hak’k’inmu zamu kad’ata”

A haka dai ta tsara masa komai duk wani abinda ya dace yayi.

      ***********

Tana kwance tana chatting Fauzah ta shigo.
Bata yi yunk’urin tashi ba bayan ta amsa mata sallama kawai ta cigaba da chatting d’inta.

“Ko na miki laifi ne naga baki fara’a nazo wajenki”

“Bakomai naga kema tunda aka baki mota kike shareni”

Murmushi tayi tare da fad’in “wallahi ba haka bane kiyi hak’uri k’anwata”

Murmushi tayi tare da cewa “ya wuce”

“Zuwa nayi neman alfarma”

“Tame?”
Ta fad’a tare da ajje wayar.

“Drivern ki nake son ki aramin zai kaini gidan biki”

“To ke mezai hana kiyi driving da kanki?”

“Na gaji da driving sis”

“Wani na nema ke kina kin gaji”

“Ni dai ki aramin shi pls”

“Sai kace wani kaya kije kiyi masa magana mana”

“A’a nafi son ki masa magana da kanki saboda bani son ya raina ni”

“Nima haka”
Janan ta bata amsa.

“Aike drivern ki ne janan”

“Nifa na tsani guy d’in nan haushinsa nakeji wallahi dan saboda shi yau nak’i zuwa skul”

“Taimaka min ni dai pls”

Ranta bayaso haka ta tashi ta fita farfajiyar gidan.

A can kan bencin maigadi ta hangoshi shi kad’ai yana latsa wayarshi k’irar NOKIA X(RK) wadda tasha ado da kyaure(lol).

K’arasawa tayi bata ko yi sallama ba tace zaka kai Yaya Fauzah unguwa yanzu.

Tayi sauri ta juya zata tafi kawai taji yace “kinyi kyau”

Da sauri ta juyo dan ta tabbatar da ita d’in yake,tana juyowa suka had’a ido taga yana murmushi.

“Dama ke kyakkyawa ce kuma kwalliyar da kikayi ya sake fito da kyawunki ko sarauniyar kyau dole ta Sara miki,kyanta dake za’aje wannan unguwar saboda zanso ace har muje mu dawo ina kallon wannan kyakkyawar fuskar”

Jikinta gaba d’aya a sanye yake,ji take kamar a mafarki ne Aliyu yake fad’a mata haka.

Ta gabanta yazo zai wuce yace “kicewa yayarmu ina jiranta bara na d’akko motar”

Tafi seconds 30 a gurin kafin ta waiga sai take ganin kamar securities d’in gidan duk ita suke kallo,Murmushi ta d’anyi sannan ta ja k’afarta da tagama yin sanyi ta koma ciki,a tsaye ta tarar da Fauzah a falo.

“Lafiya naga kin dad’e kuma kin dawo a sanyaye”

murmushi tayi tace “Yace yana jiranki”
“Okay”
“Yaya Fauzah in shirya mu tafi tare?”
“Gaskiya sauri nake bazan Iya jiranki ba”
“Mayafi kawai zan d’auka”
“A’a ki bari maje wani lokacin gidansu zubaida zanje zamuyi wata magana ne”
“Amma da kika ce gidan biki”
“Na fasa gidansu zuby zani akwai maganar da zamuyi”
“Okay a dawo lafiya”

Fauziyya na barin gurin ta bi k’ofar da kallo.

Ashe akwai ranar da zata zo inji ina son Aliyu?direba na ko dai asiri aka min?wannan wane irin sone na lokaci guda haka?
Murmushi tayi tare da fad’in “lubna batayi k’arya ba.

Alk’alamin Sadeey
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

06

Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa,tayi rolling ta d’an k’aramin veil,idanunta d’auke da farin glass hannunta rik’e da wani d’an k’aramin novel.

A tak’aice tayi kyau matuk’a.
Tun daya hangota ransa ya b’aci,a zuciyarsa ya furta

wannan kyawun naki nan bada dad’ewa ba zai zama muni sai nayi watsi da duk wani farin cikin zuri’arku

smiling yayi itama ta mayar masa dan yanzu idan ta ganshi ji take tamkar an tsundumata a aljanna”

Tana k’arasawa gabansa ta saki murmushi wanda har ya bayyana hak’oranta.

“Barka da zuwa sarauniyar kyawawa”

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta ta bud’e baki zatayi magana taji muryar Fauzah a bayansu.

“Ku tsaya ku saukeni a skul”
Duk Kansu suka jiyo suka kalleta.

A hankali ta k’arasa jikinta sanye da wata fitted gown nylon wadda tabi jikinta.

Janan kawai kallonta take rai a b’ace.

Bata sake masu magana ba kawai ta bud’e seat d’in gaba ta zauna.

Janan ta bud’e k’ofar baya ta shiga ta zauna.

Yana driving a nutse yayinda duk kanninsu suke latsa wayarsu.

“Kayi kyau sosai Aliyu” kamar daga sama sukaji maganar.

Duk kansu suka kalleta,ta maze tamkar bata ma San sunayi ba,ta sake fad’in “ko dan dama ai kai kyakkyawane”

Shiru yayi baice komai ba,Janan ji tayi zuciyarta na tafasa tamkar an watsa mata garwashi a ciki.

“Malam kayi sauri ka saukeni karna makara”
Shi kanshi yayi mamakin yadda ta masa magana a tsawace.

Nan ma bai tanka ba ya san ranta ne ya b’aci saboda furucin Fauzah.

Suna zuwa bakin gate tace ya tsaya.
A fusace ta sauka ranta a b’ace.

   ***********

Ya kirata yafi a k’irga batayi picking wayarshi ba,da ta gaji ma kawai ta kashe wayar.

“Waye haka ya dameki har kike kashe Waya?”

“Aliyu ne bayan ya b’atan rai kuma yake kirana komai zai ce min oho”

“Aliyu kuma,wanne kenan?”
“Wanne kika Sani?”

“Ni ban san kina da wani Aliyu ba bayan direbanki”

“To shi nake nufi”
“Ta fad’a tana kallon gefe da ban”

“Karfa maganar lubna ta zama gaskiya”
“Tama zama”
“Kamarya?”
“Kamar yadda nake soyayya dashi har muna shirin yin aure”
“Direbanki”
“Ya isa haka Raihan karki saka raina ya b’aci”
“Haba Janan wlh nayi tunanin duk wasa kike amma ina ke ina direba”

“Mu tsaya a nan dan wlh raina ya gama b’aci,na kawo Salman ance baya da asali shi kuma Aliyu ai kinsan asalinsa ko?”

Jakarta ta d’auka ta bar gurin,Raihan ta bita da kallon mamaki.

Tafiya take gaba d’aya ranta a b’ace ta nutsa sosai cikin makarantar inda take ma ba mutane sosai hanyar clinic ne,kawai taji ta gabza karo da mutum,wasu stars ta gani na azaba,ta d’ago dan ta bawa mutumin hak’uri kawai taji ruwan mari har uku kafin ma ta shaida ko waye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button