DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL
Ta dad’e idonta rufe kafin ta bud’e shi ta dirar dashi kan kyakykyawan saurayin.
“Hannu ta d’aga zata rama taji an rik’e ta tare da hankad’ar da ita k’asa,dariya suka hau yi sauran samari uku”
Shi kuma ya d’urk’usa k’asa saitin fuskarta yace “Janan Hashim,yarinya mara kunya,duk rashin kunyarki baza kiyi dani ba ko kuwa baki tab’a sanin waye ni a cikin polytechnic?kije ki tambaya waye yarima”
Mik’ewa yayi tsaye yana murmushi yace “kije ki tambayi ko waye ni bani da wasa musamman da talaka kamarki”
Gaba d’aya sauran mazan suka saka dariya.
“Guys muje” sun fara tafiya tayi saurin cewa “idan ka isa kai namiji ne ka fad’a min cikakken sunanka”
Juyowa yayi yana dariya ya girgiza kai kawai ya wuce.
Tashi tayi tana kad’ai kayanta sai a lokacin taji wasu zafafan hawaye na fita a idanunta.
**********
Tana kwance tana juyi gaba d’aya hankalinta a tashe yake,ga abinda ya faru a makaranta ga rashin sanin tak’a mai-mai inda Aliyu ya tafi domin Mameey tace tunda ya fita kaita makaranta bai dawo ba,ta kira numbershi yafi sau ashirin bai d’aga ba tana tunanin ko ramuwa yayi,bata yi tunanin kiran Fauzah ba dan bata kawo suna tare ba.
Haka ta zauna cikin k’unci ga rashin sanin sunan wannan guy d’in wanda ya wulak’anta ta a skul.
A b’angaren Ali direba kuwa bayan ya dire Janan a skul ya juya zai yi hanyar skul d’in su Fauziyya tayi saurin dakatar dashi.
“A’a Aliyu Najman hotel zaka kaini”
Yayi saurin juyowa ya kalle ta,tayi saurin zuge jakarta ta fiddo sark’ok’in gwal dasu bangles tace zan Kaiwa wata mata kayan saidawa ne,tazo daga lagos so anan hotel d’in ta sauna”
Kai tsaye ya nufi wannan katafaren hotel d’in.
Bayan yayi parking ta kalleshi ta marairaice tace “please Aliyu ka rakani bani son a min kallon banza dan Allah ka rakani muje mu fito”
“Amma idan muka shiga tare ai shine za’a miki wannan kallon”
“A’a please ni dai tsoro nake saboda ban tab’a shiga hotel ba”
“Ba damuwa muje” ya kashe motar ya bita.
Kai tsaye yaga tana tafiya ba tare data kira wayar kowa ba koda matar da tace tazo gurinta.
Sun hau bene kusan hawa uku kafin su isa d’akin kasancewar hotel d’in babba ne.
Ganin ta fito da key daga Jakarta yasa abin yayi matuk’ar bashi mamaki.
“Kika ce gurin wata kika zo naga kina k’ok’arin bud’e d’akin da kanki
” taje ta dawo shine ta bada key a kaimin”
Murmushi kawai yayi dan ya san k’arya take.
Suna shiga d’akin kuwa ta rufe da key,cire mayafinta tayi sannan ta cire bands da d’ankunnenta ta baza gashinta ta fad’a kan gado”
Murmushi tayi ta kalleshi “na mallaka maka duk kanin kaina kayi yadda kaga dama dani”
“Subhanalla kin san kuwa me kike fad’a”
“K’warai ma kuwa domin son ka ya rufe min ido”
“Wannan ba so bane”
“Wannan kuwa shine so” ta fad’a tare ta tashi zaune.
“Kaji tausayina Aliyu nayi maka alk’awarin babu wanda zaiji sirrinnan zamu rik’a zuwa nan muna biyawa junanmu buk’ata batare da kowa ya sani ba”
“Bazan iya ba,bazan tab’a aikata zina ba”
“Nima ban tab’a ba sai yanzu nake son farawa saboda na kasa b’oye feelings d’ina”
“Tunda kin san haka ai sai kiyi aure gudun fad’awa halaka”
“Abba bazai mana aure ba sai lokacin da ko wacce a cikinmu ta kammala masters ta fara aiki”
“Sai ki fad’a masa ke bazaki iya ba”
Duro wa tayi daga kan gadon ta k’araso gabansa ido cikin ido tace “kasan halin Abba yana da tsauri,Janan data fara soyayya haka ya rabasu yace shi ba zai bawa mai k’aramin k’arfi auren ‘yar shi ba,sannan uwa uba baya da asali daga shi sai mamansa suke rayuwa a garin,tun lokacin daya rabamu ya hanamu kula kowa har sai mun gama masters sannan zai zab’a mana mijin daya dace damu”
“Baki da hujja,ki bud’e min k’ofa na fita”
“Aliyu pls”
“Ki bud’e nace” ya fad’a a tsawace”
Sadeey S Adam✍
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????
by SaNaz deeyah????
Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv
05
A bangaren Fauziyya kuwa tunda ta fita ta sauya tafiya,sai wani irin taunar chewing gum take irin na tacaccun ‘yan bariki.
Shi kanshi Ali yayi mamakin yanda take behaving a lokacin tamkar sabuwar kilaki.
Yayi sauri zai bud’e mata k’ofar baya ta dakatar dashi.
“Ban saka ka ba” ta furta tare da bud’e gaba ta zauna.
Shima zagayawa yayi ya zauna ba tare da yace komai ba.
Sun fara tafiya ne ya tambayeta ina zasu
“Park” ta bashi amsa
“Wanne”
“Duk wanda ya maka”
Maganar yaji ta wani iri dan haka kawai ya k’udiri niyyar zai ta tafiya koda zasu bar garin in har bata ce su tsaya ba.
Yanayin abubuwan da take yi ne yasa shi b’aro jirginta amma sai ya nuna baima damu ba.
Tana gani suna ta tafiya amma bata yi yink’urin tsayar dashi ba,daga tayi mik’a sai ta zame mayafinta daga jikinta kai duk wani abu da tasan zai ja ra’ayinsa haka ta rik’a yi har ya gaji yayi parking “naga mun tsaya?”
“Ina son ki fad’a min inda zan kaiki” ya furta ba tare daya kalleta ba.
Shiru tayi tsayin Rabin minti sannan tayi dariya tace “kayi kyau wallahi ka had’u”
Kallo ya bita dashi na ban fahimci me kike nufi ba
‘Daga gira d’aya tayi ta sake fad’in “kayi min Aliyu tun ranar da aka kawoka gidanmu nake sonka”
“So kuma?” Ya fad’a a d’an razane.
“Eh so,kasan me?”
“Sai kin fad’a” kawai ya tsinci kanshi a mai bata amsa kai tsaye”
“Ina so muyi wani sirri amma ba yanzu ba ka bani number ka zan nemeka dan maganar bada rana zamuyi ta ba”
ko dai Janan ta fad’a mata komai? ya tambayi zuciyarshi ba tare da ta bashi amsa ba.
“Yah kayi shiru” ta katse tunaninsa
“Yaushe zamuyi maganar?”
“Ka bani number ka sai na kiraka idan na saka time”
Babu musu ya bata numbershi,tayi masa umarni da su koma gida kawai.
*******
Tana kwance akan gado tana juyi tunani kala-kala take a cikin zuciyarta…
ki kalli kanki a mirrow zaki tabbatar da cewa ke d’in kyakkyawa ce ajin farko
Maganar Salman ta fad’o mata lokacin daya fara furta mata kalmar so.
Da sauri ta tashi ta nufi jikin mirrow ta kalli fuskarta,wani murmushi ta saki na jindad’i sai take ganin kamar a lokacin ne yake fad’a mata.
zan tafi bazan sake dawowa garinku ba dan bazan iya jurar ganinki a matsayin matar wani bani ba,k’addara ta raba mu dake,amma nasan bazan tab’a samun kamarki ba har k’arshen rayuwata
Zubewa tayi a k’asa lokacin da ta tuno maganarsu ta k’arshe da Salman,tun a wannan lokacin bata sake jin labarinsa ba sai labarin rasuwarsa da Abbanta ya kawo mata.
“Allah yaji k’anka Salman ya yafe maka laifukanka” ta fad’a tana zubda hawaye,a dai-dai lokacin Mameey ta shigo.
“Oh dama kin shirya shine kika zauna direba na can na jiranki kin kirashi kusan awa d’aya ko kin fasa zuwa skul d’in?”
Bata bata amsa ba kawai ta cigaba da goge hawayenta.
“Janan”
“Na’am” ta amsa a sanyaye.
“Kukan me kike?”
Nan ma shiru tayi.
Kusa da ita ta k’arasa ta tallabo hab’arta
“Nace kukan me kike?”
“Bakomai”
“Oh dama anayin kukan dad’i?”
Tayi shiru
“Tambayarki nake”
“Mameey Salman na tuna”
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil,Janan meyesa bakya jin maganar iyayenki?wace nasihace mahaifinki baya miki ita akan Salman?idan kin tuno shi meyasa bazaki masa addu’a ba”
“Ina yi masa”
“To ba kuka yake so ba addu’arki yake buk’ata oyaa tashi ki saka gyalenki ki tafi skul”
Jikinta a sanyaye ta tashi ta zura hijab ta d’auki handbag d’inta.
Tana fita ta hango Aliyu tsaye jikin motar shi kam tun daya ga fitowarta yake murmushi.