DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani zugi taji kanta nayi ganin fuskar Aliyu take tamkar ta Salman.
A take ta zube a gurin a sume.

“Subhanallah” wasu daga cikin securities d’in gidan suka furta.

Da sauri d’aya daga cikinsu ya nufi cikin gidan dan sanarwa dasu mameey.

Aliyu ma a rud’e yazo gabanta ya tsaya a dai dai lokacin da mameey da Abba suka fito a tare.

“Me aka mata ne?”
“Fad’uwa kawai tayi bamu San dalili ba” Ali ya bashi amsa.

A kafad’a Abba ya sab’eta sukayi cikin gida.

2hrs ago

Fad’a sosai Abba yake yi ita kam tana jingine da fuskar gado tana kuka.

Fauzah da Fahad suna tsaye yayinda Mameey ke zaune gefen gadon.

Ganin Abba yak’i daina fad’an sai maimaita Abu d’aya yake yasa mameey cewa “fad’an nan fa bashi zai saka ta nutsu ba”

“Kamar ya kenan? Duk ba laifin ki bane,ina amfanin yarinya k’arama kamar Janan ace namiji ya shiga ranta haka,ki gaya min dalilin dayasa ta fara soyayya da Salman ba tare da iznina ba???”

“Me kake nufi da hakan?kana nufin kace Janan bata isa aure ba ko kuma bata isa soyayya bane?”

“She’s just 18 me ta sani game da wannan?”

“Ko ka so ko karka so gaba d’aya yaranka sun isa aure”

“Ni kuma bazan tab’a aurar da ‘ya’yana ba ba tare da sun gama karatu ba”

“Shi kuma Fahad da yake aiki fa?meyasa ka hanashi ya fito da yarinyar da yake so ka aurar dashi ba?”

“Hadiza mu bar wannan maganar na san lokacin daya dace ko wanne na aurar dashi”

“Nima ina da right d’in bawa ‘ya’yana zab’i”

“Oh haka kika ce?”

“K’warai ma kuwa”

“Mu zuba mu gani”
Ya fad’a a fusace sannan ya fita ya bar d’akin,mameey tabi k’ofar da kallo ranta a b’ace.

Ranar haka kowa ya yini a gidan da b’acin rai.

Sadeey????✍
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

07

Tsayawa tayi tana masa kallon mamaki yadda har yau yake mata shouting dan ta buk’aci taimako daga gurinsa.

“Kin tsareni da ido baza ki bud’e ba saina kirawo Abba”

Dariya ta k’yal’k’yale da ita tana tafa hannu “ka kirawo Abba kaga yadda zan maka sharrin da sai kayi dana sanin zama direban gidanmu”

Aliyu kayi a hankali ka kuji sharrin mace dan tana da had’ari sosai

Maganar mahaifiyarshi ya tuna lokacin daya fara soyayyar k’arya da Janan.

“Aliyu da yanzu munyi abinda zamuyi mun tafi saboda kaga lokaci na tafiya har munci awa d’aya da wani abin anan”

ban tab’a aikata zina ba bazan fara a kanki ba,da ace ni mazina cine da yau kinga k’ask’anci da daga yau baza ki k’ara sha’awar wani d’a namiji ba,yadda na tsaneku haka zanyi fata fata dake in barki cikin nadama.

“Kai nake jira”
Ta haye kan gadon ta kwanta tare da lumshe ido “wallahi ko zamu kwana anan bazan bud’e ba sai ka biya min buk’ata ta”

Zama yayi kan kujerar dake jikin mirrow yana kallon ikon Allah,abin yana matuk’ar bashi mamaki wai mace ce ke nemansa.

Sun shafe awoyi sama da 8 dan anan yayi sallahr Azhar da la’asar,yana gani itama tazo tayi.

“Aliyu na fara jin yunwa ya kamata muyi abinda ya kaw………” Mari ya d’auketa dashi wanda ya hanata k’arasa maganar.

“Ni ka Mara?”
“Ki bud’e min k’ofa”
“Wayyo Allah zai kashe ni” ta fad’a da k’arfi tare da kama rigarta ta yaga har zuwa k’irjinta”

Janyo waya tayi ta danna kira “Cikin kuka da kururuwa tace ” kuzo Najman hotel zai kasheni dan Allah ku ceceni” d’if ta kashe wayar.

Baiyi wani yunk’uri ba dan mamaki ya sandarar dashi a tsaye.

“Zan nuna maka ni cikakkiyar makira ce”

Suna tsaye taji jiniya alamar su Abba sun iso,tayi saurin yace bedsheet d’in ta rufe jikinta ta wullah masa key d’in ta Shiga toilet ta rufe.

Kusan minti 20 basu zo d’akinta tasan k’ila ana duba each and every room tunda bata fad’i d’akin da take ba.

Kamar daga sama taji ana fad’in ” ‘yata kina d’akin nan?”

Da Sauri ta bud’e ta fito tana kuka ta rungume Abba tana matsanancin kuka.

“Naga motar Janan a waje ina Aliyu?waye ya kawoki nan dan ya keta miki haddi?”

“Abba Aliyu ne”
“Yana ina?” Ya fad’a ransa a b’ace.

“Yana ganin shigowarku ya gudu”

“Arrest him” ya fad’awa ‘yan sandan da suke tsaye a gurin,da sauri suka fita.

Suka duba ko ina a cikin hotel da wajenshi basu ga Aliyu ba sai dai motar Janan.

(Kun san ya akai Aliyu ya gudu)?

Tana wurgo masa key lokacin data shiga toilet shi kuma ya bud’e k’ofa ya fita,kasancewar hotel d’in yana da steps ta ko wane side shiyasa ya rik’a bi yana b’uya daga securities d’in Abba da k’yar ya samu ya fita dan an baza ‘yan sanda ko ina,amma bai samu damar d’aukar mota ba.

A gigice ya ya hau napep ya kaishi gidansu.

“Yaya lafiya?”
“Ina umma?”
Tana d’aki.

Da sauri ya wuce zuwa d’akin,zaune ya tarar da umma tana goge hawaye.
“Umma lafiya”
Kallonshi tayi yadda ta ganshi a birkice ta tsorata da hakan.

“Bakomai ina tunawa da mahaifinka da ‘yar uwarka da suka rasu ta hanyar Muggayen mutanennan”

“Umma ina cikin tashin hankali”
“Na me?”

Labarin duk abinda ya faru ya sanar da ita,tashin hankalin da ta shiga a lokacin ba na wasa ba.

“Akan wane dalili zaka bita ku shiga cikin hotel?kenan maganganun da nake fad’a maka duk sun tashi a banza?”

Kuka ta fara sosai,Ummi ta shigo ta rik’e ta “ka rugaza duk wani shirinmu Aliyu,ka cucemu”

Furucinta ba k’aramin d’agawa Aliyu hankali yayi ba.

“Umma karki ce haka ki gafarceni,nayi alk’awarin k’wato mana hak’k’inmu kota wane hali”

“Ta wane hali kenan?Auren yarinyar ne kad’ai mafita,kana tunanin wani mahaifine zai d’auki ‘yarsa ya bawa fasik’i”

A gigice ya kalli umma yace “kina nufin kin yarda umma zan Iya aikata zina?ni d’anki ne na halak dan Allah ki daina jifana da wannan kalamai”

“Bance kai mazina ci bane amma kana tunanin akwai wanda zai yarda a cikinsu cewar baka aikata ba bayan kun shafe kusan awa takwas Ku biyu a d’akin?”

Kai ya dafe yana nadamar binta ciki da yayi,bai tab’a tunanin zata mai sharri haka ba.

“Yanzu meye mafita”

“Anjima zan je gidan saboda makullin motar janan ma yana hannuna”

“Inaso ka tafi yanzu Dan bana so ace an maimaita abinda ya faru a shekarun baya da suka wuce”

Jikinsa a sanyaye ya tashi ya fita.

Ummi na kuka ta bishi “Yaya bana son abinda ya faru damu ya sake faruwa dan Allah karka je”
Dafa kanta yayi yana murmushin k’arfin hali yace “karki damu zan dawo lafiya lau insha Allahu”

     ********

A bangaren su Fauziyya kuwa sai da Abba ya kaita asibiti aka tabbatar masa da lafiyarta k’alau sannan suka wuce gida,idanunta sun kad’a sunyi jajir kya kyace da gaske duk abinda ta fad’awa Abba gaskiya ne.

Mameey,Janan da Fahad duk suna falo hankalinsu a tashe suna jiran zuwan su Abba.

Aikuwa suna jin horn duk kansu suka fito.

Sunyi cirko-cirko Mameey ce ta k’arasa gurin Fauziyyar ta ruk’ota.

Falo suka koma duk suka zauna.
“Wai meya faru da fauziyya ne?”

Ajiyar zuciya yayi yace “Allah dai ya tak’aita amma daya lalata mata rayuwa”

“Waye wannan?”
Suka fad’a a tare.

“Wannan yaron Aliyu mana,ai na saka amin arresting nashi duk inda yake”

Tuni janan ta mik’e tsaye “wane Aliyu Abba?”

“Direban gidan nan mana,wai yaron nan ni zaici amana dubi duk abinda nake masa amma baya godiya,har ya yaga mata riga yana nemanta ta k’arfi sai shiga tayi ta kulle kanta a band’aki”

“Ai dama mutum ba abin yarda bane dan wa zaiyi tunanin Aliyu zaiyi haka” Mameey ta fad’a.

Janan kuwa ta sandare ta rasa me zata ce ma,kallon Fauzah kawai take.

“Abba kayi masa hukunci mai zafi” Fahad ya fad’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button