DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ta furta “bai aikata ba,bazan tab’a yadda ace Aliyu zaiyi haka ba”

Da gudu ta shiga d’akinta tana kuka.
“Meyasa haka?meke faruwa dani ne?”

“Ki jini da yarinyar nan”
“Bakaji me kace ba kaima,yarinya ai yarinyarce”
“A hakan kike cewa zasu iya zaman aure”
“Mu bar wannan maganar yanzu”
“A to”

Sadeey S Adam????
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

ohhni Safnah shiru babu ita babu labarinta,pls dan Allah ina cigiyar Safeenah writer d’in Sunyi Sake dan kaf numbers d’inta switched off Allah yasa dai lafiya Ameen????

08

Tana zaune a d’aki tana ta kuka dan ta rasa mafita shikenan a karo na biyu ta rasa masoyi,ta san Abba bazai tab’a yarda ya bata shi ba tunda har haka ta faru kuma dama soyayyar a b’oye suke yinta dan ta san babu yadda za’ayi Abba ya aura mata direbanta cikin sauk’i.

Tana cikin yanayin nan taji muryar Abba yana fad’in “Arrest him” a tsawace.

Da sauri ta tashi ta fita falo,idanunta suka sauka akan Aliyu yana fad’in “Abba Ku tsaya ku fahimceni wallahi ita ta nemeni”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Janan ta fad’a tana kuka,da sauri ta k’arasa gabanshi “meyasa ta bugo waya tana neman taimako? kuma kace ita ta nemeka”

Kallonta yayi idonshi jajir yace “wallahi bani na nemeta ta ba ita tace na rakata hotel zata kaiwa wata mata kaya kuma tace bazata iya shiga ita kad……..”
Abba ya wankeshi da mari “Rufamin baki”

Janan ta juyo ta kalli Abba tace “bai aikata ba Abba”

“Janan baki da hankali ne?”

“Mameey da hankali na ku duba ku gani,akwai kissar wani malami da yake cewa duk macen da tace an mata fyad’e a duba a gani da takalmi ta shiga d’akin ko kuma babu,idan da takalminta ta shiga to tabbas ita ta kai kanta idan kuwa babu takalmi to da k’arfi aka jata,sannan kuma tayaya Aliyu ya kai Yaya Fauzah hotel?idan ta k’arfi yayi mata babu yadda za’ayi su shiga saboda ma’aikatan ciki ai ba mahaukata bane,sannan meyasa tabi Aliyu bayan tana da motarta Aliyu baya da kud’in kama d’aki a katafaren hotel kamar Najman sannan rigar Yaya Fauzah ta gaba ta yage bata baya ba kinga kuwa duk zancenta k’arya ne koda ace Aliyu yana nemanta to tabbas ta amince ta kuma yarda sannan ita ta kama musu d’aki a wannan hotel”

“Abba k’arya take wallahi” Fauziyya ta fad’a tana kuka.

“Ki rufa min baki munafuka” fahad ya fad’a yana huci
“Abba tabbas akwai duba a maganar Janan”
“Kin cuceni Fauziyya ban yi miki wannan tarbiyyar ba” Mameey ta fad’a tana kuka

Abba da kanshi ya fara dukan Aliyu sannan ya bada umarni akaishi cell har sai ya nemeshi a kuma bashi abinci sau d’aya a rana sannan kar a yarda da belin.

“Abba”
“yi min shiru Janan”.

Aliyu ya Ciro key daga aljihunsa ya mik’awa fahad “ga key d’in motarku”

Juyowa yayi ya kallesu d’aya bayan d’aya a lokacin ya k’ara k’udirar cewar sai ya shayar dasu ruwan bak’in ciki Wanda basu tab’a tsammani ba.

Suna fita dashi janan ta durk’ushe tana kuka.

“Na dawo kanki Fauziyya” a gigice ta d’ago kai ta kalleshi
“Ni kike neman zubda wa daraja da k’ima ko?”

Kai ta girgiza tana kuka “wallahi k’arya yake Abba,shine yace idan banje ba zai kasheni yaje ya wurga gawata inda baza’a tab’a gani na ba shiyasa na yarda na bishi” rufamin baki manufuka.

Fahad ya kalla yace “ka kulle min Fauziyya a d’aki kar ka yarda ko falo ta fito duk abinda take buk’ata a kai mata d’akin a k’wace system d’inta da wayarta har sai na gama bincike a Kansu”

Mameey dai kallonsu kawai take tana hawaye dan ta san duk abinda ya faru da ‘ya’yanta laifin mahaifinsu ne.

    *********

Umma kuwa ganin har dare yayi Ali bai dawo ba ta San tabbas akwai Matsala.

Kallon Ummi tayi tace “ko dai zaki bi Aliyu ne?”

“Umma ki bari sai gobe saboda yanzu dare ne kuma kinsan muna da nisa sosai mu cikin k’auye su kuma cikin gari mota ma zatayi wuyar samu”

“To shikenan Allah yasa dai lafiyarsa lau duk da dai na san ba lafiya ba”

Haka ranar suka kwana cikin rashin kwanciyar hankali.

Washe gari tun sassafe Ummi ta dama masu koko suka sayo waina suka ci,sannan ta gyara ko ina a gidan,kusan k’arfe goma ta shirya Umma ta bata kud’in mota dan adaidaita yana da tsada ga wahalar samu daga k’auyen nasu zuwa cikin garin Kaduna.

“Umma ko dai bari zanyi sai zuwa anjima dan naga jikin naki babu dad’i sosai”

“Ciwon kai ne kawai kuma naji d’an dama-dama inason muji halin da Aliyu ke ciki tun jiya bai dawo ba”

“To umma Allah ya sawwak’e bara naje”

Sallamar da aka yi ya dakatar da Ummi daga shirin fitar da take.

Zuhra ce shigo kanta a k’asa tazo ta gaida umma,umma ta amsa cikin jindad’i.

“Umma dama jiya ne Aliyu yazo yace min dai yana cikin Matsala amma in tayashi addu’a zai je cikin gari ya dawo sannan yace idan ya dawo zaizo da dare naji kuma shiru bai zo ba,sai d’azu naji labari a gurin Nura wai har yanzu bai dawo gida ba,shima so yake yaje birnin”

“Wallahi kuwa muma bamu san dalilin rashin dawowar tashi ba tun da bai saba haka ba amma yanzu zan tafi cikin birnin in gani”

“Umma idan babu matsala zan bita” zuhra ta fad’a tana kallon umma.

“Kin tambaya a gida?”
“Nace masu nan na taho dan ganin ko lafiya nasan babu matsala idan na bita”
“Okay Allah ya kiyaye Ku”
“Ameen umma” suka fad’a tare.

Suna cikin mota Zuhra tace ma Ummi “to yanzu ina muka nufa”
“Gidan da yake aiki”
“Kin san gidan”
Farin sani ma”
“Toh ba damuwa”

Sun isa k’ofar gidan lafiya amma shiga cikin gidan ya faskara,Alh.Hashim commissioner of police ne shiga gidansa bazai zama abu mai sauk’i garesu ba,dan ma Ummi tayi dubara tace ma securities d’in wajen Janan suka zo.

Da farko abinda aka fara tambayarsu shine compliment card basu dashi.

Wani daga cikin securities d’in yace “kaji wannan mak’aryatan wai wajen Janan suka zo babu compliment card,babu Waya da zasu kirata suce sunzo wai kuma su k’awayenta ne”

“Hahahah amma dai basu da hankali ka dube su a hakan ne suke k’awayen janan?kai wannan zance ne”

Maigadin ya tausaya masu sosai amma baya da wani iko daya wuce bud’e gate da rufewa.

Sunga wulak’anci da k’ask’anci duk kansu ransu ya b’aci musamman dariya da cin mutuncin talauci da suke masu.

Sun fi awa biyu a zaune a bakin gate tun suna rok’onsu har suka gaji suka daina.

Sai wani security ne daya ga sun kafe sun k’i tafiya kawai ya d’aga Waya ya kirawo Janan yana dariya yana sanar mata ga wasu ‘yan k’auye sunzo gurinta wai k’awayenta ne basu da ko waya kuma babu card a hannunsu

Daga d’ayan bangaren Janan tayi dariya tace “basu wayar na tambayesu”

Mik’a masu wayar yayi Ummi tayi saurin karb’a ta kara a kunne.

“Salamu alaikum”
“Wa alaikumussalam,yace min ke kawata ce amma ya akai bani da contact dake”

“Ni k’anwar Aliyu ce,ban san kowa ba a gidannan sai ke da yake yawan magana,dan Allah ki bamu dama mu ganki dan musan halin da d’an uwanmu ke ciki”

“Okay bama wanda ya baki wayar”
“Toh” ta fad’a tare da mik’a masa

“Hello hajiya”

“Ka shigo dasu cikin Babban falo”
“Okay”

Dariya yayi yace “to k’annen Ali direba Ku shigo”
“Oh dama k’annen Ali ne?hahah no wonder na gansu a haka” wani ya fad’a yana shek’a dariya.

Maigadi kuwa sai barka yake masu cike da tausaya wa dan ya san Ali mutumin kirki ne.

Janan kuwa da sauri ta sakko zuwa babban falo ta tarar da Mameey zaune tare da bak’inta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button