DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ina zuwa naga kin sakko da sauri”

Saida ta fara gaida bak’in sannan tace “wallahi mameey bak’i nayi yanzu Mudan zai shigo dasu”
“Okay”

Tana tsaye har suka shigo,Ummi sai kallon gidan take tana ganin yadda masu kud’i ke cikin aljannar duniya.

“Sannunku da zuwa” Janan ta fad’a tana murmushi.
Suka amsa sannan suka sunkuya suka gaida su Mameey.

“Ya sunan ‘ya’yan nawa?” Mameey ta tambaya cikin bark’wanci,suma suka d’an saki rai suka fad’a mata.

Kallon Janan tayi tace ki kaisu falon bak’i ko naku ko kuma k’aramin falo”

“A’a bedroom d’ina zamu”
“Okay ba damuwa”

“Ku muje”
Tashi sukayi suka bita.

Bayan sun shiga duk kansu zasu zauna a k’asa tayi saurin cewa a’a dan Allah karku zauna a k’asa ga sofa ga gado” ,Zuhra ce tayi murmushi suka zauna kan sofa.

Itama zama tayi kusa dasu tace “sannunku da zuwa” “yawwa” suka amsa

“Amma ni Ummi naji yana yawan fad’a min a matsayin k’anwarsa”

Murmushi tayi tace “eh wannan Zuhra itace wadda zai aura”

Gabanta sai da yayi mummunar fad’uwa ji tayi kamar an caka mata mashi a lokacin da Ummi ke fad’a mata”

Ummi ta lura da hakan dama ta fad’a ne dan ta k’ular da ita.

“Bai tab’a baki labarina bane?” Zuhra ta tambaya.

Murmushin k’arfin hali tayi tace “yana fad’a min amma manta sunan nake” ta fad’a ne kawai dan kar Zuhra taji haushi.

“Ai na san dole yayi maganarta yadda yake k’aunarta”

“Uhmm bara na kowa maku ruwa na san kunsha hanya”

“A’a ki barshi mu dai kawai munzo muji ko lafiya Yaya Aliyu bai koma gida ba tun jiya”

“Karki damu bara dai na kawo maku ruwan”

Da Sauri ta tashi ta fita.

Ummi ta kalli Zuhra tace “ga yadda aka k’awata gida da kud’inmu”

“Kud’inku kuma?” Zuhra ta tambaya

“Eh mana kud’inmu mu talakawa mana ai har ke”

“Uhmm dama,amma Kin San me?”

“A’a sai kin fad’a”

“A yadda ake cewa masu kud’i na da wulak’anci sai naga sauk’in kanta sosai tana da mutunci da sakin fuska”

“Na munafurci ba” maganar zuciya tayi Wanda bata san ya fito fili ba sai ji tayi zuhra tace “kamar ya”

Sauri tayi ta canza maganar da fad’in “gashi sun saka yayana a matsala bamu san dalili ba”

“Insha Allah komai lafiya”

“Ni wallahi haushi nake ga d’akin nan wai duk girmansa na bacci ne kawai”

Murmushi Zuhra tayi tace “amma kamar ya tab’a cemin ya tsani wata janan”

“Wannan shegiyar Janan d’in ‘yar Zaria ce taso raina masa hankali” ta maze

“Oh nayi tunanin wannan”

“A’a wannan ai tana da kirki ba karmar waccan ba”

Dariya zuhra tayi ba tare da ta fuskanci komai ba.

Janan kuwa tsaya wa tayi jikin step tayi kukan bak’in cikin wai Aliyu yana da wadda zai aura,sannan ta goge hawayenta,taje babban kitchen ta bada umarnin a kaiwa bak’inta abinci da fruit,sannan ta d’auki plate ta koma d’akin.

Sadeey S Adam
[9/6, 10:08 AM] prince_s_square: ????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

Wannan Shafin naku ne ‘yan group d’ina TASKAR SANAZ bazan iya musalta farin cikina a gareku yadda kuke bani k’arfin gwiwa akan novels d’ina,nagode sosai ina alfahari daku Allahu ya barmu tare ya kuma bar zumunci
#ILYMTYE????????

09

Fridge ta bud’e ta d’akko lemo da ruwa ta d’ora kan plate d’in sannan ta d’auki cups guda biyu ta nufo inda suke ta ajje
“Bismilla”

Ruwa suka zuba suka sha sannan Ummi ta sake tambayarta Aliyu a karo na biyu.

“Nafiso sai kun ci abinci kun huta yanzu za’a kawo maku”

“Dan Allah ki fad’a mana gaskiya ko dai ya mutu ne kike son b’oye mana?” Zuhra ta tambaya.

Ajiyar zuciya tayi ta kalleta tace “ki kwantar da hankalinki Aliyu yana raye nd am vry sure lafiyarsa k’alau”

“To idan hakane yana ina?” Ummi ta tambaya.

“Kinsan ai. ……….” Knocking da ake na k’ofa yasa tayi shiru tare cewa “shigo”

‘Yan aikinsu suka shigo hannunsu d’auke da tray na abinci da plates sai plate d’in fruit .

“Bismillah Ku ajje” tayi masu umarni,bayan sun ajje sun fita sannan ta juyo ta kallesu.

“Ai ya fad’a maku abinda ya faru jiya ko?”

“Eh amma wallahi yaya bashi da laifi bazai tab’a iya aikata zina ba”

“Hakane nima zan shaideshi akan hakan,amma matsala d’aya da suka zauna d’aki d’aya a hotel kuma da Abba yazo sai ya gudu,shiyasa kowa ya shiga zulumi akan shiya jata ko ita taja shi”

“Amma kinsan idan mahaifinku ya zo a lokacin yaya baya da wani uzuri zai iya fuskantar ko wace matsala”

“Toh,yanzu dai Abba yasa an tafi dashi cell tun jiya itama yaya fauziyya ya saka an kulleta a d’aki sannan yace babu belin”

“Na shiga uku ni Ummi me zan cewa umma meyasa rayuwarmu ke tafiya a haka”

Zuhra ta ruk’o Ummi tana kuka, hakan ne yasa Janan taji hawaye ya sauka a fuskarta.

“Yanzu ko ganinsa bazamu iya yi ba?” Zuhra ta tambaya.

“Za muje daku Ku ganshi”

Da sauri Ummi ta tashi ta kalli Janan “dan Allah mu tafi yanzu ki taimaka mana”

Tausayi ta bata sosai dan haka ta tashi ta d’auki mayafi sannan ta d’auki jakarta ta kallesu “zamuje mufara yiwa Mameey sallama amma dan Allah Ku goge hawayenku Ku saki ranku karta gane wane abu bare ta hanamu zuwa”

Haka suka tashi jiki a sanyaye suka fita,Mameey still tana falo,Janan ta zauna kusa da ita tace “Mameey ina son kaisu gida gashi babu direba”

“Ina Mato?”
“Kin san mato ba yawan zama yake ba,Baita kuma ya fita da Abba”

“To ya za’ayi?”
“Mameey inyi driving d’in?”
“Ina tsoron fad’an mahaifinku Janan”
“Zan dawo kafin ya dawo insha Allah”
“Okay ki kiyaye janan karki ja mana fad’a”
“Insha Allahu”
“Kije d’akina ki d’akko masu laces guda biyu da turaruka,ki basu 10k”
“To Mameey”

“Mun gode Allah ya saka da alkhairi” Zuhra ta fad’a.

Ummi kuwa ba yabo ba fallasa.

Da sauri Janan ta shiga d’akin mameey ta d’akko komai kamar yadda ta fad’a.

Suka yiwa Mameey sallama suka tafi.

      *******

A k’ofar police station tayi parking suka shiga.

Lokacin da aka fito da Aliyu saida Janan tayi mugun firgita dan kana ganinshi kasan yasha duka.

Ummi kuwa kuka ta fara yayinda Zuhra ta dafe kai tana karanto addu’o’i.

“An zalinceka yaya Allah ya saka maka”

“Idris amma akan me za’a dake shi haka?”

“Umarnine daga wurin Commissioner”

“A wane dalili akan me?”
Shiru kawai sukai dan basu san me zasu ce mata ba.

“Cab wallahi zan wa abba magana amma akan me bayan bashine da laifi ba”

“Ummi” ya kira sunanta cikin dakiya.
Kallonshi tayi ba tare da ta amsa ba

“Ina fatan keda umma duk kuna lafiya”
“Eh yaya meyasa bazasu bamu belin ka ba?”

“Karki damu ko shekara nawa zanyi anan dole zan fita”

Basu wani dad’e suna magana ba suka tashi suka fita.

Har k’auyen su Janan ta kaisu, sai da suka fara sauke Zuhra a k’ofar gidansu sannan suka wuce.

Janan kamar bazata shiga gidansu Aliyu ba sai da Ummi ta rok’eta sannan suka shiga.

Umma na ganinsu ta mik’e tsaye
“Ummi ya ake ciki ina Aliyu yake?”

“Ki kwantar da hankalinki umma yanzu ma daga gurin shi muke, an kulleshi ne akan dai matsalar data faru jiya”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un wannan wane irin zalinci ne”

Janan ta k’araso kusa da ita tace “umma kiyi hakuri insha Allahu komai zai zama normal”

“Ummi wace wannan?”
“Ita ce Janan”
“Meyasa kika taho min da ita me zata min?”

Fad’uwar gaban Janan ta yawaita,idan har Mahaifiyar Aliyu bata k’aunarta taya rayuwarsu zata cigaba da tafiya da Aliyun.

“Fitar mana daga gida” ta sinkayi muryar umma na fad’ar haka.

Har k’asa ta durk’usa tana kuka tace “dan Allah kiyi hak’uri karkiyi sanadin rabani da Aliyu”

“Rabuwarki da Aliyu tazo tunda har bazaki iya kub’utar dashi daga wannan k’azafin ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button