DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

DIREBAN GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Zanyi iya bakin k’ok’arina nayi maki alk’awarin Aliyu zai dawo gida gobe insha Allahu”

“Idan kuma bai dawo ba fa”

Tayi rau rau da ido tace “zai dawo da iznin Allah”

“To ki sani idan har Aliyu bai dawo gida gobe ba, babu ke bashi, ban tsaneki ba ina miki haka ne dan ki gane irin yadda Aliyu ya d’aukeki a zuciyarshi”

“To umma nagode” jikinta a sanyaye tayi masu sallama ta tafi.

Ummi tayi tsaki ta kalli ledar hannunta “umma har da bamu lace da kud’i”

“Akan me?”

“Wai kyauta ce, umma kinga kuwa yadda aka k’awata gidan wani tangameme kamar aljannar duniya”

“Ki rabu dasu sakayya zata zo nan bada dad’ewa ba, ba tana son Aliyu ba in har naga ta saka an saki Aliyu a gobe tabbas zanyi amfani da wannan damar a d’aura masu aure nan da wata gudu”

“Wallahi ni duk haushinsu nake, ita kuwa Zuhra sai yabonta take”

“Itama dan bata san wace ita ba shiyasa take yabonta, yanzu wannan kayan ajjesu zamuyi har sai ranar data shigo hannunmu zamu bata tsiyarsu”.

  **********

Tana shiga umma ta sanar mata dasu Raihan sun zo suna k’aramin falo.

Da sauri ta nufi d’akin cike da zumud’i.

“Ah harda wannan ‘yar rainin hankalin akazo”

Lubna tayi dariya tace “darajar besty kika ci da bazan zo ba”

“Oh zuwanshi ne kenan ba naki ba?”

“Eh mana aini na rasa tsakaninku da besty ko dai snatching kike son yimin”

“Ah to waya san abu a duhu”
“Aikuwa baki isa ba”

“Kedai kawai ki kama k’afa dani koba haka ba Raihan”

“Hakane k’awas dan besty yana mugun yinki”

“To kinji fa”

“Ai baki isa ba”

“Naji, bara na kawo maku ruwa”

Dariya Raihan tayi tare da fad’in “kodai a rud’e kike?bakiga ruwa a gabanmu ba”

Dafe goshi tayi tace “wallahi kuwa ina cikin matsala Raihan”

Labarin komai ta basu da yadda sukayi da mahaifiyar Aliyu sai dai bata fad’a masu ga dalilin rufeshi ba ta dai ce yayiwa Abba laifi ne.

“Wallahi mugun mamaki kike bani Janan”

“Mamakin me?ai kece kika dasa min son Aliyu dan haka duk abinda ya faru ko Alkhairi ko sharri to kece Sanadi”

“Ni kuma kiji zata min sharri Raihan”

“Gaskiya ce, gani nake kamar anyi min asari, na rasa wane irin so nakewa Aliyu wallahi har ya zarta son da nayiwa Salman”

“Baki iya soyayya ba Janan sannan kina soyayya da wanda bai dace dake ba”

“Babu rashin dace a soyayya, kuma soyayya bata shawara kiga irin cin mutumcin da nakewa Aliyu amma a yanzu shi nakeso ya kasance abokin rayuwata”

“Cab to babu yadda Allah bayayi mu dai fatanmu Allah ya zab’a miki mafi alkhairi”

“Ameen my Raihan na san Aliyu alkhairi ne a cikin rayuwata”

Kallonta kawai Raihan take ita kam kawai hakanan taji bata son tarayyarsu da Aliyu.

Lubna kuwa tsokanarta take akan taga kyakkyawa ta d’afe masa.

Sun shafe kusan awa biyu kafin su mata sallama su tafi.

????????????
DIREBAN GIDANMU
????????????

by SaNaz deeyah????

Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv

10

Bayan sunyi sallar isha’i sun ci abinci Abba ya buk’aci ganinsu a babban falon gidan.

Janan ta k’udiri niyyar zata fad’a masa cewar ya saki Aliyu dan bashi da laifi koda zai kasheta zata tsaya da k’afafunta dan k’watar masa hak’k’insa.

Su hud’u ne a falo, Abba, Mameey, Fahad, Janan duk kansu sunyi shiru, Abba ne ya fara magana da fad’in “zan saka a saki yaron nan sannan na sallameshi bazai sake aiki a gidana ba, ita kuma Fauziyya zan mata horo mai tsanani dan sai tayi wata bata fita ko ina ba, idan ta fara samun carryover zata nutsu tasan mahaifinta cikakken d’an sanda ne kuma baya da wasa”

Janan ji tayi kamar an sakata a aljanna, cikin sauk’i za’a saki Aliyu,hamdala tayi a zuciyarta ko babu komai ta san umma bazata hanata Aliyu ba.

Fahad kuwa yaji dad’in hukuncin Abba dan bai tab’a tunanin Fauziyya zata iya abinda tayi ba.

Mameey kuwa jikinta duk yayi la’asar, a haka tattaunawarsu ta k’are.

Washe gari

Kamar yadda Abba ya fad’a haka ya cika alk’awarinsa dama shi kam da wuya ya fad’i magana ya k’i aikatawa, sai dai baima yarda Aliyu yazo gidan ba daga can station yace ya tafi sannan baya son ya k’ara ganinsa a gidanshi, haka ya dawo masu da labarin ya sallami Aliyu kuma babban hukuncin da yayi masa shine rashin biyansa albashinsa na wannan watan.

Janan bata ji dad’i ba amma babu yadda ta iya da mahaifinta, ita dai dad’inta d’aya an sake shi.

A b’angaren Aliyu kuwa napep ya tara ya kaishi har k’ofar gidansu.

Yana yin sallama kuwa duk kansu suka tashi suka nufo shi, dama duk suna tsakar gida suna wanki.

“Aliyu haka ka canza?meyasa mutanen nan basu da imani?”

“Umma ai wannan ba bak’on abu bane a gurinmu kin san halinsu ai”

“Allah ya saka mana, Ummi maza d’ora masa ruwa yayi wanka”

“To umma”.

Bayan yayi wanka yasha maganin ciwon jiki ya huta sannan umma ta bashi labarin zuwan Janan, haka ummi ma ta bashi labarin irin cin mutuncin da aka musu kafin su samu damar shiga gidan.

“Janan zan fara azabtarwa Umma, sai na gasa mata aya a hannunta, nafi tsanarta ita da mahaifinta domin ita ta fara nuna min tsana, kuma ta zagi mahaifina”

“Bana so ka tausayawa duk wani zuri’ar Alhaji Hashim, ina son duk runtsi ka samu damar da za’a d’aura aurenku da yarinyar nan a wata d’aya”

“Duk yadda kika ce haka za’ayi umma wannan damar ce zata bani damar auren zuhra ba tare dana sha wahala ba, Janan kuwa bayan na gama k’ask’antar da ita sannan inyi mata sakin wulak’anci”

“Tabbas bazamu raga musu ba yaya domin sunyi mana babbar illa”.

      ********

Bayan kwana 4

Janan ce ta tura k’ofar cikin sallama ta shiga.

Hankalinsa na kan takardun da yake dubawa ko bayan amsa sallamarta da yayi kawai ya cigaba da duba abinda yake.

Kan sofa ta nufa ta zauna tare da fad’in ” magana nazo muyi yaya”

“Indai akan wannan mara mutuncin ce karma ki soma”

“Yaya hannunka baya tab’a rub’ewa kace zaka yanke”

Kallonta yayi tare da fad’in “idan har hannun bai isheka da azaba ba, amma idan yana azabtar dakai ai tuni zaka yanke ka wantsar dashi”

“Wannan bai azabtar ba yaya hukuncin da Abba yayiwa yaya fauziyya yayi tsauri da yawa, friends d’inta sai kirana suke ana tayi masu lectures har da test yaya ka duba fa koni Abba ya hana na ganta dan Allah ka bashi hak’uri”

“Janan Abba ya yarda da fauziyya fiye da tsammaninki shiyasa ya bata har mota ke yana ganin kina da taurin kai da rawar kai shiyasa ya hanaki amma a k’arshe ki duba kiga abinda tayi, ai Abba ya san tabbas Aliyu bashi da laifi ya saka a hukuntashi ne kawai saboda ya kasa kiranshi a waya tun lokacin da sukaje hotel kinsan Abba da zafin rai”

“Hakane amma na san Abba da ka bashi hak’uri zai sakko”

“To zan k’ok’arta nagani”

“Yawwa yaya nagode, bara na barka ka cigaba da aikinka”

“Okay”

Cike da murna da jindad’i ta koma d’akinta ta kira number Aliyu.

Tayi ringing har ta katse bai d’aga ba sai da ta sake kira, shima har ta kusa katsewa sannan ya d’aga.

Maganar da yayi ce ta bata mamaki yadda yana d’auka kai tsaye yace “ina wani uzurin ne zan kiraki idan na gama”

“Kada ka katse min Waya Aliyu na san baka da wani Uzuri da kake”

“Kenan nayi miki k’arya?”

“A’a ba haka nake nufi ba amma ya kamata ka zamo mai yafiya Aliyu,banyi maka laifi amma kana son ka dawo da komai kaina,kullum na kiraka sai kace min kana da Uzuri bayan ba haka bane”

Ajiyar zuciya yayi sannan yace “bai kamata mu cigaba da yaudarar kanmu ba muna wahalar da zuciyoyin mu domin nasan Abba bazai tab’a aura miki ni ba”

“Baka da tabbas akan hakan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Leave a Reply

Back to top button