Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 9

Chapter Nine

………….Tunda jami’an suka dawo da labarin rashin nasara zukatan manyansu yay matuƙar ƙunci. Awanni ƙalilan suka rage musu da ga umarnin gidan gwamnati. Cikarsu babu Master a hannunsu kuwa yana nufin sun gaza a idanun al’ummar jiharsu da ƙasa baki ɗaya. Hakama ga gwamna da muƙarrabansa.
        A gefe ga gidajen jaridu da duk wata kafar yaɗa labarai sun baza kunnuwa da idanun domin ganin yanda awanni ashirin da huɗu zasu cika tare da wannan ɓarawo a hannunsu ko saɓanin hakan.
       Waɗan nan tunane-tunanen nasu yasa su shirya zaman meeting na gaggawa.

        Dukkan wani babba mai alhakin faɗa aji ya hallara a ɗakin da meeting ɗin zai gudana. Sai wanda ya jagoranci jami’an da suka dawo yanzun nan da shirin kamo Master da yaransa..
         Kowa ka kalla a ɗakin meeting ɗin kasan yaci ya ƙoshi, dan babu wasu kamannin wahala tare da su. Da’ace ƙasace mai ƙyaƙyƙyawan tsari sun cancanci yin ritaya duk su koma gefe a kawo matasa masu jini a jika da basirarsu ke aiki da kaifin ƙwaƙwalwa a zuba a madadinsu. Su kuma su zama dattijai masu bada shawara wa ƙasa ta bayan fage matsayinsu na iyayen ƙasa. Sai dai sam a wannan ƙasar tamu ba haka bane ba. Anyi sakacin barin matasan da ke da basirar zuwa da salonsu na ƙuruciya wajen kawoma ƙasa cigaba zama ƴan ta’adda, dukkan tarin basirarnan tasu da ƙuruciya ta koma aiki ne ƙarƙashin aikata laifuka. Iyayenmu da gwagwarmayar rayuwa da raunin shekaru sukaima yawa sun zama sune masu riƙe da madafun iko wajen zartarwa da hukuntarwa. A duk lokacin da ƙasa tai sakacin rashin amfani da basirar matasa da ƙuruciyarsu wajen aikata alkairi, to lallai shaiɗanu zasuyi amfani da basira da ƙuruciyar waɗanan matasan wajen kafa tantin ta’addancin da zai ruguza ƙasa.
      A ƙasarmu ta gado iyayenmu sune ƴan siyasarmu, sune masu riƙe da madafun iko na mulkin gargajiya da na siyasa, sune riƙe da hukumomin ladabtar da masu laifi, sune riƙe da manyan kuɗaɗe na kasuwanci, sune riƙe da makarantun da ake bamu ilimi, sune.. Sune… Sune komai.
      Babu wata hanya ko ƙofa da suka barma matasan wajen nuna bajintarsu da ƙwazon da ALLAH ya haliccesu da shi. Kallonmu suke masu yawan wauta, masu shashanci, masu ƙuruciya, masu rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da su. Masu… Masu… Ta ko ina. Amfaninmu kawai mu cigaba da zama a ƙasa har sai lokacinmu yayi. To yaushene lokacin namu zaiyi? Shin sai muma mun kai irin shekarunsu mu danne na ƙasa da mu kenan?. indai har a haka za’a cigaba da tafiya lallai da alamar ƙasar tamu bazata taɓa zama mai sauyawa ba ko samun ci gaba. Domin anyi sakacin ajiye lokaci an ɗauki rauni.
     Shi kuma lokaci a duk sanda aka gaza amfani da shi ta hanyar da ya dace wucewa yakeyi yabar mai shi da cizon yatsa da dana sani. A lokacin kuma daka buƙaci gyarawa sai ya kufce maka dan kayi sakaci wajen sarrafashi a sanda ya dace. To ya kamata manyan ƙasarmu su fahimci MATASANMU sune LOKACINMU. Cigaba da sakacin ƙinyin amfani da baiwarsu akan lokaci na nufin baragurbi amsarsu su su amfana da wannan damar wajen maidasu masu ruguza ƙasar da ku kuke ganin kunata ginawa. Sanda zakuyi ƙoƙarin son tarosu kuma sunyi nisan da bazasuji kiranku ba sam.
    Bawai munason fiddo da gazawarku bane ma duniya ko goyon bayan laifukan matasa. Muna buƙatar ku duba ku kuma fahimci sai da matasa ƙasa ke iya samun ci gaba. Basu dama kuma shike nufin daƙile dama a hannun masu ɗorasu bisa bigiren ta’addanci. Kun cancanci kuma muyi alfahari da ku, dan kun bamu gudunmawa ta musamman bayan kasancewarku iyaye a garemu.

       Bayan ƙarin bayani da suka samu a bakin jami’in da suka fita bibiyar Master zukatansu sun ƙara ɗaci. Ɗakin yayi shiru kowa na nazari da tunani a cikin zuciyarsa. Ɗaya da ga cikinsu da zuciyarsa ke raya masa wani abu ya nema izinin yin magana.
          “Bismillah, an baka dama. Ya kamata kowa ya faɗi abinda ke bakinsa ko hakan zai bamu wani haske da ga kullewar da kawunanmu sukayi.” Ogan nasu ya faɗa cike da taraddadi.
         Kansa ya jinjina da faɗin, “Thanks you sir. Dama wani tunanine yakemin yawo a zuciya game da ita wannan yarinyar datai mana aikin. Shin baƙwa tunanin shine ya tsara duk hakan kasancewarsa shu’umin mutum kuwa?. Al’amarin da matuƙar mamaki ta yanda ta bibiyesa cikin sauƙi. Idan har dama ba shirinsa bane ta yaya akai ta jefa masa abunda ta samu damar bibiyarsa?”.
       Da sauri wanda ke a kusa da shi ya ashe da faɗin, “Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba. Tabbas da alamar akwai lauje cikin naɗi game da wannan al’amarin. Nasan za’a iya samun mai ƙwazo da kaifin basirarta, amma yanda al’amarin ya faru da ƙanƙantar shekarunta sai nake ganin kawai shiri ne na musamman akai. Dan bana hangen tana da wani ƙyaƙyƙyawan tunanin da har zuciyarta zata bata damar aikata hakan. Banda shirme da shiririta mi yaran yanzun suka iya? musamman ma ita da ta kasance MACE”. Ya ƙare maganar cikin jin zafi sosai.
          Wanda ya gana da Hibbah dake ta faman buga pen a kan laɓɓansa yana kallonsu da nazarin maganganunsu yay murmushi. “Wannan tunanin namu na ganin yaranmu bazasu iya komai ba wajen taka rawar gani ke maida ƙasarmu da mu baya a koda yaushe. Da hakan kuma suke samun damar yin amfani da basirar tasu a gurɓatacciyar hanya. Tabbas ita ɗin MACE ce kuma ƙaramar yarinya, amma kallonta da rauni na ɗiya mace shine babban kuskuren mu. Banace inada tabbacin bata da alaƙa da shi ba, dan shi shu’umin mutum ne hatsabibi da zai iya aikata duk ma abinda bamuyi tunaninsa ba ko munyi. Sai dai banason mu kasa fahimtar cewar itama duk da kasancewar tata MACE zata iya taka wata rawar gani a harkar tsaro da duk wani sha’ani na rayuwa duk da raunin da ALLAH yay mata. Shawarata anan itace mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya”.
        Sake maida hankalinsu sukai garesa domin sonjin ƙarshen zancen.
      Ya gyara abin maganar gabansa yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. “Ma’anar mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya shine muyi amfani da wannan yarinyar ta hanyar riƙeta a jikinmu ta zame mana ma’aikaciyar sirri. Ta wannan hanyar zamu amfanu da alkairinta da kaifin basirarta. Mu kuma saka mata ido wajen gano shin akwai alaƙar da zuciyarmu take zargin tsakaninta da shi ko babu?”.
          “Yes! Wannan shawarar taka tayi matuƙa A.G”. Ogansu ya faɗa yana tafa masa. Hakanne yasa suma sauran tafa masa duk da wasunsu batai musu ba sam. Dansu babu abinda zukatansu ke ayyana musu sai ganin babu abinda Hibbah zata iya matsayinta na ɗiya MACE mai kuma ƙarancin shekaru.
          Sun cigaba da tattaunawa har zuwa wani lokaci, kafin ogan nasu ya bada damar shigo da Hibbah.

           Hibbah da damuwar ahalinta kecin ranta ta shigo fuskarta a cinkushe babu ko ɗigon walwala. Babu abinda zuciyarta tafi bukata a yanzu kamar tozali da Ummi da yayunta dan tabbatar da babu abinda ya faru da su. Zama tai a kujerar da aka nuna mata bayan ta gaishesu ranta fal jin haushinsu, musamman mutumin ɗazun da tun shigowarta da shi ta fara haɗa ido yana mata murmushi.
          Bayan sun gama nazartarta da ƙare mata kallo ogan nasu yay gyaran muryar da ta saka Hibbah ɗago manyan idanun ta kallesa. Ganin yanda ya kafeta da nasane ya sata sake maida kanta ta duƙar tana wasa da yatsun hannunta.
       “Muhibbat Aliyu Hamza!”.
Ya kirayi sunanta murya babu alamar wasa. Hakanne ya saka gabanta faɗuwa, ta sake ɗagowa tana amsa masa da rawar murya. “Na’am yallaɓai”.
        “Miye alaƙarki da Master!?”.
  “Master kuma yallaɓai? Ni ban sanshi ba”.
       “Kin tabbatar?”.
Kanta ta jinjina masa.
     “Taya za’ai mu yarda baki da alaƙa da shi?. Bayan tsahon shekaru biyu kenan kowace hukuma ta jami’an tsaro farautarsa suke, amma sun gaza koda ganin farcen yatsansa. Sai gashi ke a cikin kwana ɗaya rak kin haresa akan dai-dai?”.
        “Ni wlhy yallaɓai bansanshi ba, bakuma ni da wata alaƙa da shi ko sanin wanene shi. Na aikata duk abinda kukaga nayi ne saboda wasa da rayukan mutane da sukeyi ta hanyar power rider amma badan wani dalili ba”.
       “Okay, mu ɗauka hakanne kamar yanda kika faɗa ɗin. Yanzu wane tunani kikeyi game da makomar ahalinki?”.
        Saurin ɗagowa tai tana kallonsa idanunta cike da ƙwalla. Muryarta na rawa tace, “Amma yallaɓai naga na muku aikin da kuka buƙata dan na tabbata kun kamasa. Kuma kun tabbatar min hakan shine fansar ahalina ai”.
        “Eh tabbas haka muka faɗa, sai dai kuma ba’a samu nasara ba kamar yanda mukai tunanin za’a samu. Rashin samun nasarar kuma na nufin shigar ahalinki a haɗari ta fuska biyu. Na farko mu jami’an tsaro ba zamu barsu ba har sai wancan hatsabibin yazo hannunmu. Hakan shine zai wankeki a garemu mu tabbatar baki da alaƙa da shi, ahalinki kuma su kuɓuta. Na biyu dole ne mu baki kariya yanzun dan tabbas zaki zama abin farautarsa kema dan bazai barki ba tunda kin karya masa tarihi. Dolene kowane motsinki dana ahalinki su kasance a tare damu. Idan kin amince ki cike wannan. Kokuma kiyi tafiyarki amma babu ruwanmu da abinda zai samu ahalinki. Zakuma mu fitar da bayanan sune ke aikata laifukan da muka nuna miki ɗazun da mabanbanta fuskoki. Kinga za’a kamasu a kaisu kotu, da ga ƙarshe a yanke musu hukuncin kisa bayan duniya ta sansu matsayin ƴan ta’adda”
           Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Hibbah. Idanunta suka ciko da hawaye ta shiga girgiza musu kai laɓɓanta na rawa. “Dan ALLAH yallaɓai karkuyimin haka. Wlhy bani da alaƙa da mutumin nan sam, iya gaskiyata na sanar muku.”
           “Ta hanyar shigowa kiyi aikin sirri da mu ne kawai zai tabbatar mana da hakan, ahalinki kuma su kuɓuta da ga garesa da mu kammu. Gashi ki cike waɗan nan takardun idan har kin amince”.
         Da ƙarfi Hibbah ta rumtse idanunta. Wani irin zafi da ɗaci na sauka mata cikin zuciya. Karan farko na rayuwarta da taji tsiwa batai mata rana ba. Tanajin tsana mai yawan gaske akan mutumin da batasan wanene shi ba. Yayinda gefe na zuciyar tata ke jin haushin waɗan nan jami’ai da ke son yin amfani da damar da ALLAH ya basu ta hanyar amfani da ita. Wani gefen kuma na haske mata ahalinta cikin bala’i mai muni da idan har ta zama sanadin shigarsu cikinsa har gaban abada bazata taɓa yafema kanta ba. A take wani irin kangarewa da bushewar zuciya suka saukar mata. Batare da yin wani dogon nazari ba wautar ƙuruciya ta fisgeta da zuciya wajen ɗaukar pen ta hau cike takardun da ɓarin jiki, batare data duba mi suka ƙunsa ba..
       Fusatar tata ta basu matuƙar mamaki da al’ajabi. Sai dai zukatansu na ayyana musu tanayin komai ne domin ahalinta. Dan fahimtar sune rauninta ya sakasu yin amfani da su wajen tursasata. Aiko sunci nasara, dan ta cike takardun kamar yanda suka buƙata. Ta kuma saka hannu bisa takardar contract ɗin zatai musu aikin sirri har sai sun kama Master. Su kuma bazasu saki wancan bayanan ƙaryar da suka shirya ba domin mata ɗaurin talala saboda ƙarancin shekarunta.
         Sun mata bayanai sosai da zata iya fahimta. Tare da bata date ɗin da zata fara amsar horo na musamman a ɓoye. Da ga ƙarshe sukai mata dogon gargaɗi akan riƙe dukkan abinda suka tattauna matsayin sirri. Dan inhar ta fitar tamkar ta bayyana ƴan uwanta ma duniya ne matsayin ƴan ta’adda. Daga haka suka sallameta.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button