FITAR RANANOVELSUncategorized

FITAR RANA 31-35

ÆŠare É—are tay akan cushion kamar wata sarauniya tana ta harsashen kanta a matsayin matar me kudi, zaka iya rantsewa series din ne kawai ya tafi da ita amma ina shirmen tunanin ta kawai takeyi.

Batafi wani minti goma da kallon ba,taji kamar karar ana bude gate din ta waje, acikin wani muguwar sauri ta diro kasa ta dau remote ta rage muryan tvn gabaki daya dan tajiyo ma kunnenta da kyau.

gabanta ne ya wani fadi ita dama a can tay wurgi da hijab dinta yauma riga da skirt ta saka yar kanti shima sosai ya kamata.

Tashi tay cikin sanda ta leka windon ganin taheer na shigowa ciki tay wani wawan reverse cikin sauri ta komo kan kujerar
Ta zauna a karkace yadda komin ta zai bayyana masa sai tayi kaman bata ji komi ba.

Jim kadan Taheer yay sallama ya shigo bata ko juya kanta ba,kallon tvn takeyi irin ace hanklinta gaba ki daya baya wajen din nan…a zahiri kuwa kirjinta sai bugawa yakeyi da uban karfi

..kallo daya yay mata ya dauke kanshi fuskan sa ba asake ba yay gyaran murya,a dan firgice ta juyo cike da salon wani makirtaccen pretending tanayi kamar wacce ta razana,saida suka hade ido snn tay wani irin karairaya ta juya cikin sauri ta dauki hijab dinta ta saka,a makirci tay kasa ta tsuguna cikin sanyin murya tace
“laaa yaya na sannu da dawowa ashe harka ka shigo..”karasowa ciki yay, yace ya kike,sassanyar murmushi ta saki kafin ta amsa tace lapiya.

Zai wuce sama dakin wasime tay saurin mikewa tsaye cikin dakatar dashi cikib salo tanacewa uhmmm Yaya,wasimen tana zuwa dama taje dauko wani abune anma yanzu nan zata sauko.

Atakaice Yace ok..
saiya fasa zuwa dakin wasimen yaje nashi kawai, gani yay ko ina tsaf kominshi a tsaftace hakan bakaramin saka zuciyarsa yin sanyi yay ba

After like 10 min ya fito da tunanin zaizo kasa ya sameta, yana dosowa yaga najaha tana famar
Jera abincinshi akan dinning “da wani irin makirtaccen murmushi ta tarbe sa “ur food is ready da Kamar bazai zauna ba dai ya dawo ya zauna din kodan yunwar datake addabar sa dan yau kwata kwata bai samu yaci wani abinci ba tun safe Dama lokacin da zaicin kenan yay deciding ya garzayo gida kawai ya duba halin da wasime take.

Hanklinsa bai wani kwanta ba musamman daya fita yabarta bai aje mata kudi ba kuma baida tabbacin ko najahar zata zo mata akan lokaci

Zama yay agaban abincin cikeda da jan aji yanadan babbasarwa da uban rawar jiki najaha tay serving dinshi sharp sharp,she was perfect at it sabida ta riga ta saba da yin hakan a shagon su da customomin maman ta.

Qamshi da kyan abinci a ido ya saka taher ya soma tabawa kadan yanadan ci ahankli ahankli.

Gefe taja ta dinga kallon sa,ko tari yay sai kaga ta firgita ta miko mai ruwa.

Suna cikin haka saiga wasime ta sauko riga da zaninta ta saka ta daura dankwali da mamakin ganinsa ahaka ta karaso gareshi ta dan gaishe sa.

Suna gama gaisuwa ko jan nunfashi basuyi ba najaha ta soma tsoma musu baki tana cewa ai itace tay girkin,snn sam taki barin wasime ta gaya masa cewa wanka taje takeyi dazu ba dauko wani abu ba,sai tamaida abun yayi kamar wasime barinta takeyi tayi komi a gidan ita kuma taje dakinta tana hutawa

,wasime duk bata dagota ba intana karyanta sai kawai ta basar ta kyaleta

Ahaka ahaka anakan zuwa abun najahar saiya soma yin tsanani, kusan kullum tazo gidan wasime ce zata yi girki baifi tadan mata gyararrki kadan ba amma daga anzo gaban taheer sai ta nuna cewa itace ita kadai tayi komi snn wasime bata komi sai zaman banza

A kullum dai haka najaha take kkrin nunawa taheer acikin makirtaccen salo
cewa wasime batabiya komi ba Har abun ya soma damun shi aranshi.

Jin yadda abincin yake kkrin shiga ransa he wud have loved it ace matarsa ce take girkawa..

Shiyasa kwana biyu inya kalle wasime saiyanajin takaicinta,aganin shi duk sakalci ne da shegen son jiki..why wudnt she just cook for him kamar yadda yaga kawarta takeyi.

Bai taɓa sanin cewa ashe kullum ita din ce takeyin girki ba sabida najaha ta gama lura kamar hannun wasimen ya fi nata dadi,ta dawo bata tsinana ma wasime komi sai aukin comanding dinta daga tace suyi kaza saitace suyi kaza itadai master ce wajen kawo suggestion intayi ne ta dan tayata wanke wanke ko shara

Itako wasime abun baiya ko damunta sai da akaci kusan sati guda harda yan kwanaki snn ta soma shaƙar abubuwan da najaha take kullawa akanta

Gata da shegen rike abu acikin ranta,daga kan karyan da najaha takeyi agaban yayanta ta somajin haushi haushin ta musammn ma ayanzu dataga taheer ya dan soma sake fuskarshi kadan kadan da najaha har yana amsa maganarta,yana tambayan ta abubuwan da babu agidan ita kam abun nema ne ya samu nan danan ta soma fidda wasu makirtaccun halaye wa wasime

tsaban rawan kai Wasu maganganun ma bata sanin ta furta mata

Yau daga tace ita ce boss din gida,sai ta soma acting kamar itace ma matarsa, ga son bada oder akan abunda za’a masa kamar itace kadai mai iko dashi .ran wasime tuni ya soma baci da hakan…wani bin intana mata haka sai ta hade rai Tace mata ta tafi gida,tana ganin wasime ta hade rai Atake atake saita sauko tahau washe baki sai tace ai wasa ita take mata.Musamman ma akan kalman datake yawan furtawa nace wa itace uwargidan gidan lokaci ne kawai ake jira ta shigo,har wani ce ma wasime kanwata ta somayi, sosai wasime ta tsani wannan rahar ta ta kullum intanayi bata sake mata fuska sai ta hade ranta tace ita batason wannan wasar amma duk da haka najaha bata ko saka ranar denawa ba

Infact kowani rana tazo da sabuwar kisisinn datake zuwa dashi abun yabi ya ishe wasime sosai ta soma jin haushin ta.

hakan yasaka ta fara takurata dan tana koya mata abubuwan daya rage wanda bata iya ba, haka zasuyi ta girki ko bazasuci ba saita make sure takurata ta dan ta nuna mata yadda akeyi wasu ababen..

ahaka ahaka harta ta dan iya sarrafa abubuwa kala kala dakanta gashi yanzu hannunta ya soma mikewa sosai akan girka abinci dake abinma baiwace ajikiin maishi harta fi najhar iya sarrafa wasu abubuwan

Duk rintsi dai tanason kawancen ta da najaha
Amma karyan datakeyi agaban taheer yasa ta somajin tsanarta aranta,

ayanzu batada wani buri face taga ta gama koyan wasu abubuwan data saka agaba domin ta rabu da najaha

Sosai najaha take kkri wajen juya mind din taheer akan wasime
haka wata rana zaina gatsala mata magana aganinsa tafiye sakalcin da son jiki taki ta tsaya ta koyi komi awajen najaha.

Saida abun yafara zafanta,ya soma ci mata tuwo a kwarya sann ta zo ta dena ganin laifinsa ta fara kallon me najaha takeyi haryasa yayanta’
Yake yawan mata fada yana mata kallon sakaltaccya wanda bata iya komi ba…

Ranar haka ta shirya tsaf ta fito fuskanta ba a sake ba dan bata ko dariya

Samu tay har Najaha ta goga wasanta akan taheer ta amshe kudi mai yawa wai zasu sayi spices na abinci yana bata kuwa taje har kasuwa ita kadai ta sisisiyo abubuwan ta dawo

Yanzu kam ma direct take shiga kitchen tay abunda take so,sai in wasimen ta zago kawai saita ganta gatsau aciki tana abubuwan ta kamar wani gidan mijinta
,yauma kusan abinda ya faru kenan,najaha tana dawowa daga kasuwa bata tsaya neman wasime ba ta wuce kitchen tahau jejjera kayayyakin data siyo…

Daga kofar kitchen din ta tsaya tana kallon ta, wani uban tsawa ta daka mata tana cewa”………..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button