Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 37

Mamuhgee 37_*
Wunin ranar cikin sanyi tayisa zazzabin ma tuni ya gudu sbd kunyar anty Sa’adah dake dawainiya da ita musamman da Abban yakirata tana zaune tareda Anty Sa’adahn sai kame kame take tana amsa Masa a Dan gajarce duk da irin maganganun dayake Fado mata.

Asibiti ma dasukaje kasa sakewa tayi tana ganin Kamar abbanta da Momy zasu gane Dan Haka duk tabi ta takura
Daqyar Suka Gama kwanakinsu anty Sa’adah ta karbe duka takardun asibitin dasukaje na sakamakon cikin da harsu scanning dasukai sbd kada tsautsayi yasa wani ganinsu a hannun Laylan,

Anty Sa’adahn tafara wucewa tanajin kamar ta tafi da Laylan tayi rainon cikin agabanta Dan har cikin ranta take Jin rashin nutsuwar barin Laylan a tareda Ms Na’ima sbd tana ganin irin girman qiayyar da Ms Na’ima ke Mata sbd kallon datake Mata a matsayin kishiyarta,
kadan take jira tasamu sanadin illarta rayuqarta,
To bare idan daga sama kawai tasamu cikin mijinta jikin ‘yar datakewa kallon ‘yar data Haifa, take raino agabanta,
Ba labarin aure ba komai tafara Jin ciki…. Tabbas komai zata iya aikatawa Dan kuwa ta wani bangaren an Mata saukar masifaffiyar bazata ta inda Bata tsammani.,

Dan Haka idan Takoma taji Bata nutsuba zata sanarda Anne Dan gwara kunyar da Laylan zatai akan wani abun ya sameta suna ganin sunfara samun lafiyar abbansu zuciyarsa bugawa zatai wani Abu yasamu Laylah.

Bayan tafiyar Anty Sa’adah itama jirgin dare tabi Takoma Atlanta bayan ta nawa kanta qwarin gwiwa ta tattaro karfinta da nutsuwarta Takoma yanda take Dan kada ta taba bada Daman ganin sauyi atareda ita har shi Abban Dan Yana gano da ciki jikinta tabbas bazaiyiwa kowa boyoba asirinsu tonuwa zaiyi,
Gashi kunya da tausayin mum Na’ima takeyi sbd tamkar taci Amanarta ne.

Tana sauka A Abdoul ne yazo daukanta yaja suitcase dinta har mota tana Shiga motar qamshin Bois elite daya cika motar ga sanyin AC ya shiga hancinya ta waiwayo da Dan sauri ta kallesa Yana zaune cikin navy blue Ralph Lauren suit dasukai masifar yimasa kyau sbd ta Jima Bata gansa acikin suit ba,
Da alama kodai yayi dare sosai daga office kokuma yayi taron aiki da baqi a office din.

Rufe motar A Abdoul yayi tareda shigowa ya tada motar yaja Suka wuce sbd dukkaninsu harshi din baby Wanda baya tareda gajiya Dan Suma yau din baqi yan china sukai shiyasa sukai dare a office.

Ahankali ya Kai hannu ya kamo nata ya matse cikin nasa da sauti Mai taushi Mara hayaniya yace”

Welcome.

Kallonsa tayi Jin yanda yayi Mata sannu da dawowan sai taji jikinta ya sake sanyi da gajiya ta matso ta shige jikinsa ta kwanta tana cewa”

Sannu da gajiyan aiki.

Lumshe fararen idanuwansa Dake sake bayyanarda gajiyarsa yayi har suka Isa gida har ciki A Abdoul ya shigo Mata da akwatinta Cindy dake murnar dawowarta ta karba sukai ciki.

Sama ya wuce itakuma ta wuce dakinta,
Cindy ta janyo akwatinta ta bude tana cire kayan ciki Dan maidawa closet ta jera ta cire masu dauda ta fita dasu itakuma wanka ta fada tayo jikinta ya sake da gajiya tana fitowa tasaka Riga da wando na bacci masu kauri da hula tayi sallar ishai dan ita kadaice batai ba.
Dukda tanajin gajiya Amma batajin nutsuwar barinsa ya kwana ahaka tunda tasan haryanzu Mum Bata dawoba Dan Haka ta nufi kitchen ta dafa Masa green tea ta Dan gasa sliced hudu na bread ta Madara Mai zafi daya Dan fara Sha yanzu sbd kwanakin Nan dasukai tare.

Samansa ta hau takai Masa har bedroom dinsa Kamar tasan Yana buqatan Dan har yayi wanka Yana zaune Yana kashe wayoyinsa zai kwanta.
Kallonta yayi da shanyayun idanuwansa harta qaraso da kayan jere ta aje Kan table din gabansa ta fara miqa Masa madaran ya shanye a hankali da qaramin sauti ya furta”

Thank you.

Qaramin cup din tea dinsa ta miqa Masa tareda gasashen bread daya gasu da butter kadan aciki.

Ahankali cikin nutsuwa yagama Shan tea din Yana kallonta tana zaune gefensa harya Gama yaje yayi brush tana zaune har Saida ya fito tajasa har gado ya kwanta taja Masa bargo ta rufesa tareda kashe Masa wuta ta kwashe kayan ta fice bayan ta furta masa” good night” ahankali Yana binta da wani irin kallon zuciyarsa na narkewa da kallon yanda take kulawa dashi kawai kafin ya lumshe ido ahankali take kuwa bacci ya daukesa kamar wani baby.

Kitchen ta maida kayan itama tasha Madara Mai zafi kafin ta wuce daki tana Isa hayewa gado kawai tayi ta kwanta bayan takashe wuta take bacci Mai Dadi ya dauketa.

Washe gari sai kusan 11 ta farka ta sauko gadonta ta nufi toilet tayi brush tafito ta zauna Kan couch tana daukan wayarta da massages suka shigo duk na Abban ta bude tana karantawa fuskarta daukeda boyayyan murmushi.

Anty Sa’adah tafara Kira Bata sameta ba Dan Haka ta Kira Anne,
Daqyar ta iya dannewa tayi waya da Annen.
Tana gamawa sofia takira data isheta da Kiran tadawo tana dauka tace”

Nadawo saikizo kiban abinda Zaki ban.

zira slippers tayi tareda miqewa ta fito tana waya da Sofia ta nufa dining sbd yunwar datake tsananin ji.

Tana shiga ta kashe wayarta tana kokarin ajewa ta zauna Kan dining din sakonsa yashigo wayarta tana budewa tabasa reply da tana dining room.

Ta zauna kenan tafara cin abincin taji qamshin turarensa ya Shiga hancinta ta saki wani murmushi tasan shine ya shigo..

Yana qarasowa ta dago ta Suka hada Ido kafin ya gangara da idanuwansa Kan bakinta datake cin avocado toast da cheese wrap,

Good morning” tace tana kallonsa da murmushi akan fuskarta.

Cheese din daya Bata gefen bakinta ya kalla Bai amsa gaisuwar ba ya ranqwafo yakai bakinsa ya cinye cheese din tareda kissing bakin…..

Dariya takeyi sbd yanda yake Mata harda waiwayi yake data.

Ta cikin qaton console mirror Dake dining room din ta hango Cindy shigowa daukeda madarar datace ta dafo Mata…

Janyewa tayi tana kallon fuskarta da Ido ta nuna Masa kofar da Cindy tuni tashigo tana ganin yanayin tsayuwarsa akan Laylan ta juya zata bar gurin ya Dan gyara murya tareda kamewarsa ya nufi kujerarsa ya zauna Yana cewa ta shigo kawai.

Qarasowa tayi tana kasa kallon gefensa tazo ta aje ta juya ta fice.

A Palo Cindy taja ta tsaya tareda daukanwa kanta aikin goge gogen rashin dalili a palon cikin fargaba sbd yau Ms Na’ima zata dawo Dan Haka tsoro takeji tunanin zata iya dawowa kowane lokaci hakama suma acan dining room din komai zai iya faruwa Dan Haka tsoronta tasan ba Laylan kawaiba kila idan Ms Na’ima tadawo Ana Haka ko su sai ansamu Wanda zata raunana Dan Haka ta tsaya aikace aikace palon farko Dan gudun bacin Rana.

Babu Bata lokaci kuwa tajiyo Kamar karar faduwa kaman cups daga dining room din..ta sulala taqara matsawa nesa da kofar dining room din tana cigaba da aikin datake Yi.

Saida Suka Gama Bata dakin Suka Bata lokaci Mai tsayi kafin suka bar dining room din zuwa bedroom dinta inda suka qarasa shiriricewa kafin yaje yayi wanka ya fice aiki guraren 1pm bayan A Abdoul tuni ya Isa office yafara ji da baqinsu na jiyan da Basu Gama dasuba.

Bayan fitarsa wanka tayi ta Sanya guntuwar doguwar Riga sofia tazo suka shiririce da fira wuni guda sai yamma sosai Suka fito ta sauya kayanta Dan Kai sofian gida da kanta.

Bayan fitarta yadawo Dan Haka shi kadai yaci abincin dare ya fito yakoma yayi wanka ya Sanya pyjamas black ya zauna Yana amsa wayoyi cikin nutsuwa da rashin hayaniya.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button