FITAR RANANOVELSUncategorized

FITAR RANA 31-35

Taheer yabita da kallo daya snn ya dauke kansa gani yay yau kam tay kkri wajen yin shigar mutunci,doguwar hijabi mai kyau mai style ta saka pink colour kalar da yafi tsana arayuwar sa kallon ta yy da gefen idonshi baice mata uffan ba.

Wasime ne tadan kikkifta idanunta akanta tace”kai najaha haryaushe kika iya shigowa gidan mutane babu ko dan sallama Allah ni harkin tsorata….da har zata ce “mu”..ganin yana harar ta da gefen idon tay saurin gyara maganan tace har kin tsoratani.

Wani irin kallo najaha tay
Mata tana dan tsuke baki atake ta sauya fuska kalar tausayi tace “toh kuyi hkri dan Allah..dama naga banga kowa bane agidan sai kuma naji motsi motsi atanan kawai saina leko dan naga waye ne.

Wasime tace oh Toh ai bakomi snnu da zuwanki.

Mikewa tay da salon rangwadi tace yawwa
Taheer zai fice cikin sauri najaha ta wani juyo tanabinshi da kallo a dan sassarfe tace”yayan wasime zamu iya maka panken? juyowa yay da mamaki fusknsa ba a sake ba,fiskewa tay ta cigaba da maganan ta kamar ma bataga hakan dayayi ba tana cewa”Wallhy yaya na iya kuma zakaji dadinshi yaya na,wasime zamuyi mishi ko?…ta faÉ—a confidently tana washe baki game da tattaba kafadun wasime..

Dan dauke kansa yay akansu,cikin ranshi yana ta tunanin yadda akay najaha tasan sunyi maganan panke duk abunda suke cewa har tajiyo su kenan? yasan definately labe tay musu cos when they were discussing dis bata nan awajen tayaya har zatasan cewa sunyi hirar panke?

…yana cikin tunanin hakan saiga wasime har ta matso kusa dashi..
cikin langwame murya tace”yaa dagske ne fa ta iya,ai maman ta tana saida abinci a can kasuwa itama fa tanayi sosai.Zakaga kafin ma ka shirya har mun gama…”baice komi ba ya dan shafa kanta gently snn yay smirking ya wuce ya fita abunshi.
ahnkli wasime tabi bayansa da karamin murmushi tana mai sauke ajiyan zucya.
Wani abin na gaya mata aranta sabida tay farinciki kawai yasaka yake barin najaha.

Boyayyar ajiyar zcya ta sauƙe Tana juyowa kuwa suka hade ido da Najaha da bata fahimce komi ba.

cikin bugun zuciya “tace toh ya?..yace muyi ne?

Dawowa ta gefenta wasime tay tace eh man
Amma fa muyi sauri mugama yanzu karmu É“atamai lokaci,nasan in muka gama on time inna kai masa zaici. tana fadin hakan ta tsuguna a gaban drawer ta hau fidda musu flour.
A cikin zumudi najaha ta zare hijab din jikinta wani mahaukacin blue jeans ne ya bayyana ajikinta ta dame da shi tasaka wani farar rigar crop top dan karami wanda da kyar ma yagama rufe mata cibiyarta,a dan sace wasime ta kare mata kallo da mamaki snn ta kyabe bakinta a shashance cikin basarwa.

Nan bada jimawa suka fara kwaba panken najaha tana farawa wasime ta amshi kwabin daga hannunta tace kee dan Allah barmin inyi tunda banwani iyaba keda kika iya in nayi kuskure ai saiki gyaramin ahaka nima zan koya yadda akeyi sosai,babu musu najaha ta sakar mata kwabin duk dama ranta bai wani so ba,ayanzu shawarar mahaifyar ta kawai zatabi dan tanabin wasime a hankli kar tay wani kuskure asake korarta a gidan.

Tana kallo wasimé tay abunta,suprisingly taga babu wani kuskure harta gama bataci gyaranta ba,maimakon taji mata dadi wani haushi ne ya dabaibaye zuciyarta tanajin kishin da ba itace tayi kwabin.

Itafa tazo nan gidan ne domin tayi yaƙin samun wani muhimmiyar gurbi
Acikin rayuwar taheer.

And mamanta ta gaya mata the way to a mans heart is thru his stomach ai tunda ta iya abinci kuma kanwarsa wasime bata iya ba, wannan kusan wani babban dama ne agareta da zata soma murza nata wasan acikin gidan harse ta cimma burinta na samun kan muradin zcyanta wato taheer.

Wasime Tana kammala kwabin,najaha tasaka hannu ta amshe “tace toh ya isa nice zan soya aikinyi naki kkrin..nima kibarni nayi nawa.

Karamin Murmushi wasime ta saki game da matsawa gefe”Tace toh ga hanya, ni wallh dama gas din nan yanaban wahala, tsoron sa nakeji, kinsan fa ance yana bombing ya kona mutane.

Fashewa da dariya najaha tayi cikin raina mata wayo tace “kai wasime matsoraciya.toh uban wa ya faÉ—a miki hakan?wallh karya yakeyi hmm gas din ne yake bombing din mutane?

dakewa wasime tay Tace…”kikace Uban wa?to bilti ce ta gayamin aikinsan bazata taÉ“a mini karya bako.

Kyabe baki najaha tay tace Hmmm toh wann karon kam ai tay miki,shifa gas babu abunda yafishi dadin amfani. wahalrsa kawai shine in bakada kudin refiling dinsa amma ai ku bakuda wann matsalar naga yayanki yana da kudi ko?

Kyabe baki wasime
Tayi tarasa mesa najaha take son fiye kawo tsabgar yayan ta acikin hirarsu,rolling idanunta tayi snn ta amsata ciki ciki tace”yaya na yanada kudi?to wayace miki yayana yanada kudi? Da can kinma sanshi ne?
Najaha tay rau da idanunta “kai wasime daga tambaya kawai ni bance miki na sanshi ba

Tsaki Wasime taja ohh nima ai bansani ba..kije man ki tambayeshi dakanki da can ni aljihunsa ce…?

Baki bude najaha ta juyo zatay magana cikin datsar numfashinta
Wasime tace ke malama ni wallhy bana son kananan gulma yo ina ruwanki da kudin shi,kedai kiyi shiru kawai kiy abunda ke gabanki mana,kiyi sauri kigama suyan nan kar muyi lattin gamawa yay shirinsa yace Ma bazaici ba.

Najaha bata kara ce mata komi ba ta maida hanklinta akan suyan datakeyi da maganganu taf acikin zuciyarta wanda bata firta su ma wasime ba,Nan da nan sai gashi sun kammala suyan dake basu wani yishi da yawa ba.

Kafin nan wasime harta dauƙo tea cup ta fara shirya masa shayin sa a nitse,nan danan ta dauko katon gwangwanin madarar peak milk ta fara hada masa shayinsa yadda taga yake so,gaba ki daya hanklin najaha nakanta itakam ma bata sani ba,najaha tanata famr marking duk wani abunda takeyi,karamin tea spoon ta dauko ta zuba spoon biyu na sugar,da mamaki najaha ta riƙe hannunta

“ke dan wann sugar ne zaki saka mai?..batare da ta juyo ba ta kwace hannunta tace “yaya na baison sugar mai yawa..gyada kai najaha tay batace uffan ba aranta tanajin dadin sanin haka!a fili kuwa tay kamar abun da tace din bai wani darata Ba,.
matsowa ta karayi kusa daf da wasime tace
Uhumm toh shi meyake so ne acikn tea dinshi?
Ko amsata wasime batay ba,ganin haka yasa ta hade rai”ke wannan tea din naki harzai masa dadi kuwa dama bani kikayi na hada masa.

Wasime tace”toh ki tsaya kigani mana..shifa madara ne kawai tea dinshi ba kayan zaki ba sai kuma kitabbata kinsa kayan qamshi yaji ya dan fito shikenan,kyabe baki najaha tay “Toh kawo na tayaki gaurayawa naga kamar bayi kauri sosai ba.

.,sake mata wasime tay ta fara motsa shayin,snn ita jawo pancakes din ta hau zuzzuba masa a serving plate..nan da nan suka kammala komi dan karamin tray ta dauko
najaha tana kallonta taje har gaban sink ta kunna ruwa ta dauraye kai duk dama babu abunda ya sameshi,tana kammala hakan ta dauko neat kitchen towel tay drying dinshi up tazo kan kitchen island Ta aje snn jejjera abincin akai ta dauka zata fice dashi.

A take najaha ta soma jin wani iri iri a zcyart,tanajin kamar taje ta kwace tray din ita takai masa ba wasime ba.

Kuma tasan da wuya ne wasime ta bata raganar rike tray din,binta abaya kawai tahauyi zuciyarta cike da kishi hakan aranta tana cewa bazaiyu kura da shan bugu gardi da shan romo ba,ai tare mukayi aikin.
yanzu inna kyaleta takai abun nan ita daya zaiga kamar ita kadai dince tayi kkori,barin ma da panken yay masifar dadi da kyan gani a ido ,inba itama nuna masa tayi tayiwani abu ba ai saiya raina mata wyo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button