FITAR RANANOVELSUncategorized

FITAR RANA 31-35

FR31

Desperate13:my only one

Na kudi ne,300₦ via 0152983148..GTB
08060712446

Ajiyar zuciya taheer ya sauƙe ya juya da wasimé a kafadarsa suka bar wajen suka nufi hanyar gida,shikansa baisan yadda akayi ya kawo su gidan ba tunanin duk abunda ya afku shiya mamaye zuciyar sa musamman ma na tausayin halin da bilti take ciki ayanzu.

Jikinshi yana kan basa cewa bilti bata cikin kwanciyar hankli a duk inda take damuwa da rauni duk ya bayyana a yanayinta,dan tunda suke da ita bai taɓa ganinta acikin irin wannan mummunan yanayin ba.

Wasimé kuwa duk ta galabaice tanata kuka marar sauti tare da yin lamo akan kirjinsa,da kyar take sauke ajiyar zuciya,numfashi mai bala’in kara da wahalar wa shi yake fita daga bakinta.

Har ya shigo dasu gida bata san ina hanklinta yake ba,sunkucanta yay suka shige ciki bai tsaya da ita akoina ba sai dakin sa.

Akan gadonsa ya shimfidata ahankli snn ya dawo gefenta ya zauna ya soma rage mata kayan jikinta tare da bata taimako cikin gaggawa.

Yau Allah ya soshi tana zuƙar inhaler ta sau daya ta samu bacci mai nauyi.
Kallonta ya tsayayi ganin ko acikin baccin ma kuka takeyi duk alamar hakan ya bayyana bisaga yadda take jajjan zuciyarta tana juye juye da hawaye cif a kan fuskarta duk dama idanuwanta a rufe suke cikin bacci.

A bakin gadon ya zauna daf da ita ya shafe ilahirin fuskan sa da tafin hannun sa cikin rasa nayi tausayin ta gaba daya ya kashe masa lakar jiki.

Yaukam yasan komi ya kare masa babu wani abunda ya rage face ya sake ransa yay rayuwar sa a daidai yadda tazo masa..

ya dade yana zaune awajen cikin tunani kafin nan can cikin dage kafadun sa sama ya sauke ajiyan zuciya mai sanyi,Daga nan tashi yay ya nufi masallaci Domin gabatar da sallahn asr.

Bai shigo gidan ba har sai can wajen karfe hudu da rabi na yamma har lokcin ya samu wasime tana kan tikar baccinta

Tsayawa yay akanta yanata kallon yadda ta dukunkune waje guda game da rungume kanta gwanin ban tausayi.

Babu abunda yake dawo masa aransa daya kalle fuskanta ayanzu face maganganun data dinga furtawa wa bilti dazu musamman cewa datake yi yanzu komi nayi mata wuya,tace ana barinta a gida ita kadai,bata iya abinci ba,hakan yana nufin babu wanda zaina mata abincin da zataci
Hakama yaji tana cewa babu mai mata kitso,”
Tausayin ta yakeji aransa..bai san sanda ajiyar zuciya ya kufce masa ba..ya dade a tsaye akanta cikin nazari can kafin nan ya sauke ajiyan zuciya cikin maida numfashi snn yabar wajen ya shige bathrum domin yin wanka.

Sauri yake yana Allah Allah ya gama ya fito kafin ta tashi ta kallesa acikin wani yanayin da bai dace ba,after like 15 mins ya fito jikinshi yay wani fresh kugunsa dore da white towel.

Gaban mirronsa ya wuce sharp sharp ya shafa mansa na aloevera vaseline ya bi jikinshi da turare mai qamshi sannan ya dauko wata neat coffe brown colour jallabiya ya sakata akan wata three qtr shot dake jikinshi..

Tsayawa yy agaban mirror yana kkrin taje suman kanshi daga nan yaji kamar Wasime tafara motsawa.
Da sunan bilti abakinta ta farka cikin gigin baccin da baigama saketa ba tana juye juye.

Idanunta a kulle cikin muryan kuka da magiya mai ban tausayi tafara cewa Dan Allah Dan Allah bilti karki tafi kibarni,aje comb din yay cikin sauri snn ya taho ya zauna a gefen gadon yana kallon yanayinta,
tausayi sosai take basa dan yasan ba’ayi mata daidai yau ba.

But there is no way he is gonna let all they problems disturb his peace,gwara ya maida komi bayan keyansa ya fuskanci abunda zai ficcesu gaba daya.

Yau damuwa yasaka shi neman layin iyayen sa dazu dayaje masallaci amma to his greatest suprise none of them was available to pick his call,Mahaifinshi ma layinsa a kashe ne kamar tsawon lokaci yay bai buÉ—e layinsan ba.

Daga nan ya cire ransa akansu kawai Dan Yasan Babu wanda zai taimaka masa akan wasime
shikuma he cant really concentrate on her fully, ga jarabawar sa ga aikinsa ga zuwa training, dolene kawai yasan yay zaiyi wasime tayi hakri ta mance da zancen bilti.

Haka rayuwan su ya kasance kwana biyun baiya samun sukuni kullum yana kulawa da lpyar wasime sosai.

Kwana biyu adan dolenshi ya dawo da ita ganga da jikinsa tana kwana tare dashi a dakin sa suna baccin su tare akan gado daya.
Kafin ta kwanta haka zai
Lullubeta da jikinshi yay musu addua.

Kullum sai ya jira tayi nisa acikin bacci snn yake jawo ta ya rungume ta ajikinshi suyi baccin su atare domin ta dena jin tsoro aranta ta samu wadataccen bacci da kuma cikakken nitsuwa.

Da alamun dadin hakan wasime takeji dan kuwa daga ya jawota jikinshi take sakar masa jikinta gabaki daya snn ta manne masa ko ta kankame sa cikin gigin bacci ta hana sa sakat da juye juye.mostly ita take hankarar da shi har yasan asubah yay cos a lokacin wani sabuwar sanyi ne mai ratsa kwakwala yake sauka toh rungumar datake masa ma na dabanne awann lokci Mannesa takeyi kamar bazasu taba rabuwa da juna ba.

Kullum kafin ta farka yakanyi sauri ya rigata farkawa harya yi abubuwan dake gaban sa shiyasa haryau bata fahimce abunda yake faruwa atsakanin su wajen bacci ba.

Ita dai tasan Hanklinta yana kwanciya inyana mata nasiha akan datay hakuri akan tafiyar da bilti tay tabarsu,duk da haka wasime kullum sai tay masa kukan banza.
shiyasa gabaki daya ciwonta ya fiye tashi akai akai, shi tun anan ya fahimce cewa Yarinyar tana da riƙo da kuma zuciya mai zafi.
saidai Kuma kowani salonshi nayin tasiri mai girma acikin zuciyarta.

Wani bin har mamakinsa take sha acikin ranta dan Bata taɓa tsammanin
Ya iya dadin baki da lallashi ba har saida ta shiga wannan yanayi
,kowani dawowar sai ya kawo mata soyayyen kaza ko grilled fish da juice ko wani shawarma koma ya siya mata kala da kala na vanilla and chokolate ice creams da sauransu.

Inya kawo abinci taci a washe gari haka zai tashi tun asubahin farin duk gudun wai kartana taɓa ruwa kar ciwonta ya tashi,haka zai daure yay mata wanke wanke,yay moping snn ya wanke kayayykin su yay mata komi na aikin gida.
Bai iya komi ba kam amma dan dole ya koya makansa.

Kwana biyu Sam Baya barinta tana aikin komi musamn aikin daya shafi ruwan sanyi da kuma ƙura,daga ta zauna shiru sai kaga tana karatu sai kuma kwanciya da kallo,ahaka har saida ciwon nata ya rabu da ita ya lafa mata sosai ya dena tashi akai akai.

Kafin sati ya kare Kukan banzan Ma duk ta rusuna ta dena yinshi,duk dama haryau zaka ganta shiru shiru sam bata walwala sosai kamar kwanakin baya da suka wuce

Ranar lahadi da taheer baije koina ba bayan ya sissiya mata kayan dadi taci ta koshi,tana tsaye tana kallonsa ya tsaftace gidan.sann yasata taje tay wanka daga nan Suka dan fita gari tare,.

yau har barracks dinsu ya zaga da ita,suka kai har wajen hostel din female soldiers wajen wata course mates dinshi elizabeth daya fiye taimaka mata acikin exams hall in abubuwa suka cirke mata..
tana respecting din taheer sosai sabida bata taɓajin ya bazata ko ya tona mata asirinta awani waje ba.

Sau daya ya taɓa cin karo da ita tanayiwa co inmates dinta kitso kamar da wasa yace mata zai kawo kanwar sa tayi mata aikuwa ta takura masa harsaida ya mata alkwarin zai kawo wasime ranar sunday.

Sosai tay murnan ganin su wajenta cos she have been looking for a slightest way to repay his kindness towards her,barracks wasnt a fun environment,sojoji riƙeda bindigogi da ta dinga cin karo dasu yasa duk ta tsorata tazama shiru shiru,duk yadda suka so wasime ta saki jikinta da su ta kasa yin hakan Tsabar jin tsoro da fargaba,haka taki kowa ya taɓa mata kanta ta dinga narke mishi tana bori wai saida ya mata kitson dakanshi, haka ya cire girman kai ya zaunar da ita awajen ya tsefe mata kan ya barta ta taje dakanta.Shidai baisan ya ake kitso ba,wayo yy mata ya sabule jikinshi ya fita da waya a kunnen sa yace mata ana kiransa ne yanzun nan zai dawo.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button