FITAR RANANOVELSUncategorized

FITAR RANA 31-35

Wani Tsandar dar najaga ta hargitso tace inxauna fa kikace?chab di wallahy saidai mu tafi duk inda zakije din tare. Ni fa ba yar gadinki bace.

Mikewa wasime tay tana dariyarta tace”hmmm kya ji dashi,toh muje cikin..

Sama suka dosa a tare wasime takaita harcikin’ dakinta suna shiga najaha ta tsaya tun daga bakin kofa tana karewa koina kallo, bata iya boye maitar kishinta ba ta dinga kalle kalle tana kyabe bakinta cikun ranta cewa take hmmm wannan katoton dakin duka wa ita daya..hmm lallai kam wasime tana cikin jin dadi,tana shanawa.karasowa bakin gadon tay lkcin wasime tanata magana bama jinta take ba Kallon gadon kawai take wanda akalla tasan ya doke wanda ita da maman ta suke kwanciya akai girma.

Wani gauron ajiyar zuciya ta sauƙe..
tana dada fahimtar harsashen mahaifyarta
Tasan inhar ta aure taheer rayuwarsu gabaki daya zai zanja…wannan uban gata da ake bawa wasime datake matsayin kanwarsa yo inaga ita intashigo a matsayin matar gida?

Wasime ce ta juyo cikin raha tace toh yaa kawata yaya kikaga daki na?yay kyau kuwa?..najaha tana kallon ta cikin yake tace “uhum kawata daki yay kyau.”Toh ina dakin yayanki yake?…

Batare da ta kalleta ba tace “mezakiyi dashi?

“Kai wasime ke badama’ mutum ya dan tambayeki?

Rau tay ido tace ai naga babu alakarki ne dayin wannan tambyar…
anyways dakinshi yana can ta waje dayan bangaren daga na gama gyaran nawa dakin nashi zanje in gyara yanzu

Cike da rawar kai Najaha tace “Allah?..toh mai zamuyi anan din pls lets do it sharp sharp saimuje chan din ko?..wasime batace mata uffan ba harsaida najaha ta gama sakar jikinta ta taimaka mata sukayi aikin tare suka wanke toilet suka gyara gado sukayi shara snn suka fetsa turaren qamshi.

Bayan sun gama suka fito suka kama hanyar zuwa dakin taheer.
Wasime tana gaba najaha na bayanta sai Allah Allah take sukai dakinshin tagani kodan ta samu rahoto mai dumi dazata kaiwa mamanta wayasani hala yau ma ta bata wasu shawarwari gameda hakan wanda zai iya dada jawo kusancinta tare dashi.

Har sukakai bakin kofar wasime bata juyo ta kalleta ba,sai suna daf zasu bude su shiga wasime ta sa fuska ta wani harde ranta tay banga banga a bakin kofar ta toshe hanyar wucewa da kafafunta ta hade rai”da mamaki najaha tabita da wani irin kallo”ke kuma meye haka?Murkuda bakinta tahauyi”nide wallh ki dan tsaya anan.Yaya na ai bazai ji dadi inya sameki anan ba…

Najaha bata san sanda taja tsaki ba tace akan me?…ke wasime wallhy bana son walakanci da iskanci da Allah kiban wuri

Dada toshe kofar wasime tay ta karayin banga banga tanacewa “yo akan me zaki shiga nan fa dakin yayana ne ai saida nace miki kizauna a falo innagama ai zaanzo muyi abubuwar mu….

haushi take ya kular da najaha muryanta a dagule da fushi tace ke ni bana son iskanci,kefa dramar ki tanada yawa.

Tace
“Drama ko? Hmm yau zaki ga drama kuwa in baki koma kasa kinjirani ba,wai ma dolene sai kinbini ha’aaa..nace miki yaya na bayason ana shigar masa daki ko?..kawai kije ki kasa…mtssss

Turus Najaha take kallon ta tanajin kamar ta shaketa kota kamata tamata shegen duka sosai iskancin wasime yasoma kaita makura
muryanta kamr na wanda zata saki kuka tace “kai Wasime wai gori zakiyi min sabida nazo gaban dakin yayanki?

cikeda bushe ido wasime tace yo ni Gorin me namiki anan?dan kawai nace bayaso ai bani nace ba shine ya fada…

Najaha dakejin kamar zata fashe cikin haushi tace “kai makaryaciya yaushe yace miki hakan

Kikkifata idanunta tayi tace ai ba dole bane kisani.

wani shiru nahaja tayi da’ fuska kalar tausayi can cikin kyabe baki tace Hmmm to ai shikenan.
Allah ya jikanmu muda bamuda yaya. .wasime ba damuwa kicinye dakin kicinye harda yayankin ai dama kekam ba a abun arziki dake dama can naga kamar walakntani kawai kike so kiyi hmm danma nazo gidanku ina son na taimaka miki..ba damuwa ni kawai zanyi tafiyata . ..

Tsaki mai tsayi wasime
Ta ja tana kikkifta idanu cikin turo bakinta gaba tace…ke toh da Allah kiyi hkri,nide ban walakntaki ba..yo aikece da shegen son bibiyar mutum kamar wata jela wai duk inda naje kema sai kinje?mtsww..tooh muje cikin amma nide karki taÉ“a masa komi bana son yaya yazo yamin fada.

Babu wani jan aji najaha ta juyo cikin sauke ajiyar zcya tace “okay muje naji bazan taÉ“a masa komi ba

Nan wasime tajanye kafafunta a bakin kofar snn ta bata hanya, ahankli ta bude shi a sann suka shiga ciki,tun da suka shiga kirjin najaha yahau bugu ji take kamar zata ganshi aciki,tsayuwarta tay tunda ga bakin kofar dakin tana ta deben ma wajen kallon kare dangi da idanuwanta.

Wasime tayi sauri ta isa bakin gado ta soma tattara kayan su da suka babbaza akai tana nannade su…

acikin balain sauri najaha ta dawo gefenta idanunta nakan kayan da ke hannun wasime,sket dinta ne na jiya data cire ta yasar a kasa, wani cak numfashin najaha ya dauƙe game da daga sauran kayan a kasa

Tace Ke wann ba kayan da kika saka jiya bane meyakeyi anan.

Wasime bata wani kulata ba tanakan nannade kayan tana ajiye sai can tace “ohhh anan ashe na kwana …Cikeda yanayin mamaki Najaha tace what?…anan fa?hnmm
Sai bata kara cewa komi ba tay tsinin baki

Tana tsaye har wasime ta gama komi ta gyara kan gadon,nan ma sai kallan kan gadon take, a take idanunta sukayi wani jimmm da ruwan kishi Jin wasime tace anan ta kwana yo akanme?abun dai nata cakalar zuciyarta..
Wasime kam kota kula tana kammalawa tajawo hannunta sukayi waje

Wani Shiru najaha tay na tsawon lokaci batace mata uffan ba har saida abun yadan wuce mata a zcyanta snn ta soma jin dama dama

Kitchen suka nufa atare ganin yanayinta with ruined mood yasa wasime batako kulata ba
Kunna gas dinta tay dakan ta ta kuma rageshi
Ya kasance dan daidai
tukunyar dafa indomie ta dora tayi blending kayan miya Ta sassaka akai can ta dauko sardines na gwangani ta fasa akai ta barbada mai magi da mangyada, jim kadan indomie dinta mai shegen dadi ya kammalu.

Koda da suka taho falo sunaci najaha ta sha bala’in mamakin wasim acikin ranta, gani tay agabanta wasime ta dafa indomie kuma bata wani saka mishi wani abu special aciki ba amma saigashi yay dadi harma ya Æ™ere nata a dadi,acikin zuciyarta kawai ta bar maganan batace ma wasimen uffan ba..bayan sun kammala ci suka soma zantawa akan abunda za’a girka ma yayanta,as expected najaha ce ta kawo suggestion akan suyi masa doya da miyar kwai da samosa harda kunun madara,kusan atare sukayi aikin har komi ya kammalu yadda yakamata,wasime tana dada samun wayewar kai akan yadda ake yin wasu abubuwan sosai,bayan sun kammala aiyukan su nan najaha ta dau ragamar soya miyar da kwaba samosa wasime kuma ta tafasa doya tay kunun madara akan anjima ita zatay wanke wanke.

Har suka kammala komi da komi taheer bai dawo ba.

A falo wasime tabar najaha tana kallo,ita kuma ta wuce dakinta a sama dominta ta dan watsa ruwa,dama duk zuwan najahan ne yanahata samun lkcin yin wankan safe, kuma baxata iya yi a lokcin da suke girki ba, so kawai take itama ta tsaya ta koya dan ta kwarance a iya dafa komi kamar najaha

Najaha ce kadai a falo tana zaune akan three sitter tay wani banga banga da remote a hannu tana kallon tashar zee world lokcin daf ana maimaicin wani series mai dadi mai cike da cakwakiya ga mutanen series din duk masu kudi ne,duk ta bada hanklinta akansu ne sabida taga rayuwar karya ita bawai jinma me suke fada takeyi ba,ita dai imagining kanta take tayi a matsayin wayannan irin matayen,matar mai kudi,ta tuna da itace da irin sheƙe ayar da zatayi bana kadan ba, da tsadaddun kayayyakin da zatana sakawa dan tana baza mulkinta iyakar son zuciyarta ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button