NOVELSUncategorized
BARIKI NA FITO (BOOK 1) 9

PAGE 9
NOT EDITED
Bariki ce cikin shiri tasa riga da wando Sun kamata ta saki gashin kanta fuskanta na d’auke da glass ba karamin kyau tayi
ba, d’an karamin akwatinta ta d’auko ta Fara ja domin zuwa airport, tana fita tahau taxi don a kaita airport, lokacin data shiga har an fara shiga itama shiga tayi sanda ta shiga ta hango alh madu tayi sauri ta zauna dan karya ganta, tace tsinanne da wani katon tumbinsa, jirgi d’agawa yayi bayan an gama jawabi akan kowa ya kashe waya tare da fad’in Koda jirgi zaiyi hatsari ga yanda za suyi, dai dai karfe 2 a kasar Nigeria suka sauka domin lokacin mu da nasu ba d’aya bane, bayan jirgi ya tsaya aka fara fita, bariki ce a gaban alh madu bai samu ya ganta ba, koda ta fita taxi tahau tace ya kaita garage, direct gareji aka kaita, inda tadau tashar mota golf dan a kaita kaduna.
Yarima Aliyu ne cikin shiri dan zuwa gaida sirikin sa wato sarkin katsina, fita yayi inda fadawanshi suka bishi direct inda sarki yake yaje a kasa ya zauna ya gaida Mai martaba, sarki amsawa yayi cikin sakin fuska a kullum yana kara son Aliyu saboda tarbiyanshi, Mai martaba yana ta dan jan Aliyu da surutu, ya d’auki lokaci Mai tsawo inda yayi ma Sarki sallama tare da fad’in gobe zai koma tafiyan safe zaiyi hala ba zasu had’u ba, nan sarki yaita sa mishi albarka, direct d’akin da aka saukeshi ya nufa, bai dad’e da shiga ba sai ga Gimbiya Wanda tunda abunda ya faru ta daina zuwa wajanshi sai dai Inya fito zashi wajan mahaifinta su had’u kuma taga yanda yake d’aure Mata baya bata fuska yanzu, zama tayi kusa dashi tare da fad’in Barka da Safiya, bai kulata ba tace Yarima nazo in baka hakuri akan abunda ya faru, wlh Sonka yasa nayi hakan, sai Bayan nayi kuma nayi dana sani dan Allah kayi hakuri, murmushi yayi tare da fad’in babu komai ina son mutum Wanda in yayi laifi ya bada hakuri, murmushi tayi tare da fad’in ngd Sosai daka hakura, tace ya kamata mudan zagaya tare kaga gidan koh? Bai musa Mata ba yace ok tashi muje, ganin haka yasa Gimbiya taji dad’i Sosai, fita sukayi suka fara zagaya gidan fadawa na binsu a baya, Yarima Aliyu binta kawai yake amma shi matsalanshi tafi karfinshi dan baida wani buri Illa gobe ya ganshi a kaduna dan a goben yake son zuwa maraban jos ko Allah zaisa yaga yarinyar da yake nema, ita kam Gimbiya idonta nakan Yarima tana kallonshi tana murmushi cikin jin dad’i ta rasa mai yasa take son Yarima Aliyu Sosai, bata kallon gabanta sai Yarima tun tube taci zata fad’i tayi dan kara da sauri Yarima Aliyu ya rukota, tare da d’agota ganin haka yasa ta wani kankame shi, tana sauke ajiyan zuciya, d’an janta yayi daka jikinshi tare da fad’in ki dinga kallon gabanki, kai ta d’aga alaman toh, yace zan koma ciki Inci gaba da shiri gobe da safe zan koma, yana fad’in haka yayi gaba, binshi tayi har d’akinshi din tace haba taya zan bar Yarima da kanshi yayi aiki, wannan ba aikin kowa bane sai nawa, bai ce mata komai ba, ta bud’e wardrobe din d’akin ta Fara zuba mishi kayanshi cikin akwati, tanayi tana kallonshi tace zanyi missing dinka Sosai ji nake kaman in bika, ya rasa mai yasa kwata kwata Gimbiya zinatu bata kama bakinta ta cika surutu, ido ya lumshe domin jin haushin maganan ta yake, sai dai wani lokacin takan dan bashi tausayi, jin bai bata amsa ba yasa tace kayi hakuri na cika ka da surutu koh? Ido ya bud’e tare da fad’in a’a kawai Ina bukatar hutu ne, shuru tayi Kafin tace ok nama gama had’a maka kayan, saida safe, har zata fita ya kira sunanta, waigowa tayi tare da fad’in na’am, yace zoki zauna muyi magana, zama tayi kusa dashi, yana takaicin irin halinta domin yaga kwata kwata bata kunyan son zama gab dashi, yace zinatu Ina son ki sani in kara fad’a miki wannan auran bada son raina bane, amma nayi accepting dinshi lokaci kad’an zaki zama matata in Allah ya yarda, but akwai abubuwan da kike yi Wanda ya dace in fad’a miki ni Yarima Aliyu daka ranan da aka d’aura mana aure zaki fara saka hijab zaki daina sa duk wannan kayan masu fito miki da tsiraici kina ketawa cikin maza, koda bana son aurenki dole In kara mutuncin iyalina da kaina, Gimbiya zinatu tace insha Allah zan daina daka yanzu Indai hakan zai faranta maka, kai ya d’aga alaman yaji dad’in maganan ta, yace zaki iya tafiya gobe tafiyan safe zanyi ba lallai mu had’u ba, tace dan Allah Yarima karka tafi sai munyi sallama dan Allah, yace OK in zaki iya tashi 7 dan lokacin zan wuce, tace insha Allah tare da fita, koda ta fita dariya ta saki tare da fad’in muje zuwa da haka zan mallake zuciyar ka, sai dai irin kayan da nake sawa bana tunanin zan daina amma zan gwada inna mallaki zuciyarki sai yanda nayi dakai, ranan kwanciya tayi cikin nishad’i domin Yarima yayi dogon magana da ita, ta gefen Yarima kam yaji dad’in yanda Gimbiya zinatu bata da girman kai sai dai bata da kame bakinta amma a hankali zai seta ta.
Habib ne da Hjy babba tsaye a kofar gida suna tattaunawa, Hjy babba ya hango bariki tana fitowa daka mota da sauri ya nufeta tare da fad’in ah ikon Allah, yana ganki a golf Ina jeep din? Tace hjyta dan Allah ki barni a gajiye nake, Hjy babba tabe baki yayi tare da fad’in ai dole ki gaji tunda kin tafi daka ke sai shi cin safe daban na rana daban na maraici ma daban, habib shima karasowa yayi yana fad’in ah oyoyo oyoyo tauraruwan gidan ta dawo, yana maganan ne yana bangare kirji, bariki shuru tayi bata ce musu komai ba, habib yace yau naga sabon iskanci ke bariki ana magana kinyi shuru, sai kace wani ne ya danneki, Hjy babba tace gane min hanya y’ar uwa, bariki tace Hmmm in kuna son jin matsalan muje amma ba’a nan ba, binta suka farayi suna rangwada har d’akinta zama tayi katifarta su kuma suka zauna akan carpet, Hjy babba yace wai bariki da wani sabon iskanci kika dawo ana magana kina wani tamke fuska kaman ba’kin hadari, filo ta jefa ma Hjy babba tare da fad’in ai duk kai kaja min ka had’ani da dan iskan mutum, Hjy babba ya fara salati tare da fad’in na shiga uku an fasa aurena, wa kike nufi? Tace Mai ayabar yara mana, habib yace oh ni habiba karku lalatani, bariki ta wurga Mai harara, Hjy babba tace maiya miki haka? Tace ni ya Mara Wlh saina nuna mishi ni y’ar iskance ta gaske, Hjy babba yace Mari? Oh ni Wai Mai yasa mazan nan basu da tausayi ne su kama mata suyi ta duka, habib yace ai maza basu da mutunci Sun Mai damu kaman bayinsu, in sun tashi biyan bukatarsu sai Kaga y’an banzan sun zo, Hjy babba yace Aini sai yasa Wlh nida maza sai nesa nesa tunda basa tausaya mana kuma sun San mu Mata rauni garemu, wayar bariki ne yayi kara dan dama bata canza sim ba, bud’e jakarta tayi taga alh madu, kin d’auka tayi tare da sakin tsaki, har wayan ya tsinke ya kara kira, ganin zai dameta yasa ta saka wayan a silent, Hjy babba tace uhm Kaga Abu Kala Kala tabe baki yayi tare da fad’in ki d’auki wayan mana, tace bazan d’auka ba dan Wlh sai n….. Shigowan Haulat yasa bata karasa abunda tayi niya ba, Haulat rungume bariki tayi tana fad’in bariki Ina kika jene? Bariki tace nayi tafiya ne, bariki ta kalli Haulat tace gobe sati koh akwai rawan gwatso Haulat ta tashi ta Fara kad’a duwawu, habib yace dad’in Abun Muma muna dashi, Haulat ta saki dariya tare da tura duwawunta dai dai wajan fuskan habib ta girgiza sannan tace amma ba irin wannan ba jin karan ihu kaman ana fad’a yasa suka fita su duka da gudu, dan suga maike faruwa, wata karuwa ce ita da saurayinta suke fad’a sai jibganta yake yana fadin dan ubanki Mai kika nema kika rasa? Yar iska kawai harta d’akin da kike zama ni nake biya abincin da kike ci ni nake baki amma sai kije kina kula wasu maza zabga Mata Mari ya kuma yi yana fad’in karuwar banza karuwar hofi ni nafi karfin wulakanci, bariki ce ta nufeshi tare da ture shi ta d’aga yarinyar wacce ya mata jina jina amma duk da haka bakinta bai mutu ba sai fad’i take aurena kayi dan iska aiba sadaki na ka biya ba, balle ka hanani hulda da wasu mazan shege karamin dan iska sai naci Uwar babanka, zabura yayi zai kuma cafko ta bariki ta tareshi tare da fad’in haba mlm ai wannan ba girmanka bane kaita dukan mace, Hjy babba tazo tana fad’in na shiga uku an fasa aurena Wai y’an mazan nan Mai yasa kuke mana hakane ku kamamu kuyi ta jibga kalli yanda ka fasa mata baki ni Wlh Ina takaicin halin maza, jamil da habib suma suka karaso suna fad’in oh sai kace ana ya’kin duniya, habib yace gaskiya Malam baka kyauta ba ka kama y’ar uwarmu mace kaita jibga sai kace ka sami gardin namiji irinka gaskiya mazan nan bakwa mana adalci, jamil ya tabe baki tare da fad’in ai wannan wulakanci ne wlh maza kuna cin zarafin mu haba dan Allah mutumin ganin Sun mishi ca yasa ya fita tare da kallon yarinyar yace zan kamaki yar iska mayaudariya, tace kaine dan iska shege dan zina, Hjy babba tace la na bani daman dan zina ne oh Kaga Abu in baka mutu ba, shewa suka saki tare da fad’in sawa suka had’a duwawu suka buga, bariki ta kalli yarinyar tace haba khairat mai yasa zaki biye mishi harki Bari ya duke ki? Khairat tace haba bariki Dan kawai yaga wani yana cina sai ya fara duka na sai kace mijina Aiba aurena yayi ba ina da ikon duk Wanda naga daman ya cini in yarda, bariki tace hakane khairat amma da baki biye mishi ba jiba yanda ya ji miki ciwo, khairat tace ai Wlh shi zai biya kud’in magani, habib yace oh kunji bariki ya jibgeki sannan kice ya biya kud’in magani? Wucewa khairat tayi tana fad’in ai dole ya biya dan uwarshi, Haulat data gama waya tazo tace kuban labari maiya had’asu? Hjy babba yace sai kije gidan radio a baki labari, Haulat tace Kai dai ka sani, yace dakata Waye Kai? Haulat tace wanda ya tsargu, Hjy babba yace caf durun uwa Wlh zan miki rashin mutunci, Haulat tace kaima kanka dai Hjy babba yace Wlh Haulat kinfi kowa sanin halina nafi y’ar iska iya iskanci ganin Hjy babba tayi zafi yasa Haulat tace haba kawata wasa fa nake miki Hjy babba tace banso gskya banso taya zaki dinga kaini jinsin daba nawa ba, Haulat tace bazan kara ba Hjy babba gaba yayi yana fad’in iskancin banza Mai za’a nuna min, Haulat jan hannun bariki tayi sukai gaba tace muje inada magana dake.
Washe gari Yarima Aliyu ne cikin shiri mota ya shiga dan dawowa garin kaduna, fita sukai daka cikin masarautar suna fita saiga Gimbiya zinatu ta kirashi d’auka yayi yace hello, tace Yarima Ina hangoku kuka fita dan Allah ka tsaya muyi sallama, yace kiyi hakuri in muka karasa za muyi waya, inna fito bana komawa, babu yanda ta iya dole hakura tayi, Yarima Aliyu sun Kai garin kaduna wajan karfe 11 da wani abu na safe, direct maraban jos suka nufa inda suka shiga cikin anguwar basu karasa gidan ba Yarima yaga habib yana tafiya yana rangwada, yarima yace ma driver dinshi tsaya da motar, bayan driver din Yarima ya tsaya yasa sauran motocin suka tsaya tunda suka shigo anguwar idon mutane ke kansu, yarima ya nuna ma driver dinshi habib yace ka kira min shi, driver din ya fita tare da fad’in angama ranka ya dad’e…… Muje zuwa
MARYAM OBAM