Uncategorized

HABIBI DA’IMAN 141-160

        *PAGE141~145*

 _Two days later_

 *F*itowarshi kenan daga bedroom yana d’aura agogon hannunshi don har yaso ya makara, kallon khadijah yayi dake zaune a parlour ta d’aura k’afa d’aya saman d’aya tana mashi kallon ukku saura kwata, har zai wuce sai kuma ya dawo Inda take yana kallonta cikin ido yace

 

 

“Uhm khadijah kenan yakamata ki gane ni ban can-canci zargi a wurinki ba, kwata-kwata kwana biyun nan kinfita lamarina, baruwanki dani ko abinci baki girka mani saidai nafita na saya naci, kanki kawai kike dafamawa, duk miyayi  zafi da zaki horar da ruhinmu haka”

 

 

Ak’ulaface take kallonshi tace “mizai hana kaje wajen karuwan naka su dafamaka kaci” daga haka ta tashi ta Ruga d’aki saboda kukan da taji ya taho mata

 

 

Fita yayi daga gidan don bazai iya jure jin kukanta ba, ita kuma tanajin tashin motarshi ta kara fashewa da kuka tana cewa”yayana ka cuceni ka yaudareni ina danasanin saninka da nayi a rayuwata”

 

 

Girki suke ita da Mama a kitchen babu mai magana can  ihsan ta katse shirun tace “wai Mama meyasa Baba yasa akayi ma Yaya khadijah Jere a Kaduna bayan Abuja suke zaune?”

 

 

“Saboda insun zo gidan su zasu rink’a sauka ba gidan iyayenshi, don haka yanxu kiyi sauri ki karasa Mani girkin nan ni zanje in shiga wanka Babanku ya kusa dawowa” toh Mama shine abin da ihsan tace

 

 

Tana gama girkin itama ta wuce d’aki don tayi wanka, wayartace ta d’auki ringing da sauri ta d’auka tana cewa “eye amaryar nan da 2 month’s” daga can bangaren Islam tace “ai harda ke ni wallahi gani nake ansa abin kusa sosai ko dayake angwayen ne suka matsa ba kamar Rafeeq…”

 

 

“kema  kinsan wanan sai dai Mujaheed ni su samra ma gani nayi ba ruwansu abin ta masu dadi”

 

 

Islam tace “ke ni bawan nan ba, dama na kirakine ince maki kawai Ku fidda duk ankon da yayi maku keda twince duk yadda kukayi kin sanar dani kawai”

 

 

“Ok toh ba damuwa sai kinjini” daga haka suka aje wayar

 

 

 

*****

 

 

A cikin kwana biyun nan laila duk ta gama had’a yadda plan d’inta zai kasance shiyasa take farin ciki saboda gobe ne zata ai watar da nufinta, kallonta Ashanty tayi tace

 

 

“Uhm laila a gaskiya kina shirin aikata babban kuskure Wanda bai kamata ace na zuba maki idanu ba ina gudun abin da zakizo kina da kin Sani, yakamata kituba tun kafin lokaci ya k’ure ma….”

 

 

saukar Marin da taji ne yasa tayi shiru tana kallon Laila da mamaki tace  “ni kika mara?..”

 

 

“eh an mareki kuma daga yau idan kisan wanan zancen zakiyi Mani kada k’afar ki ta sake takowa  inda nake” hawayen da suka cika ma Ashanty ido ne suka zubo mata, bawai dan zafin marin da Laila tayi mata ba sai don tausayin Laila da takeji, tare da d’ago kai tace

 

 

“Kada ki damu bazaki sake ganina ba dama naso ace kamar yadda muka shigo bariki tare mu fita tare sai dai Allah bai k’addara haka ba,

Don Haka ina maki ban kwana dafatan alkhairi,  gobe da safe zan wuce Kano in koma wurin iyayena in nemi gafararsu kema ina fatan Allah ya shiryeki da sauran masu hali irin naki”

 

 

Daga haka ta fita tana tunanin yadda zata kubutar da Jiddan daga tarkon Laila, don ta tabbatar bazai tab’a  yimata abin da takeso ba

 

 

Itakuwa Laila tsoki ta buga tana cewa “aini ba kanwar ubanki bace da zakice mutuba tare” nan ta zauna tana zumudin gobe tayi donta aiwatar da k’udirinta

 

 

Zaune take a palour tana kallo tana jin alamun shigowarshi amma ko daga kai ta kalleshi batayi ba shima bai cemata komai ba ya wuce d’aki don yayi wanka amma tunani yake a ranshi idan  ba khadijah ba’ai yi macen da zatayi mashi haka ya kyaleta ba, har ya fito tana nan Inda take zaune, zama yayi bisa cushion d’in da take tare da aje mata take away na abinci don haka yakeyi yanzu tunda bata dafa mashi amma idan ya bata bataci sai dai yaci da dare domin tana dafa nata taci

 

 

Tashi tayi da niyyar ta bar mashi wurin yayi saurin rik’o hannunta yace

 

 

“pls zauna magana zamuyi” ba musu ta zauna tare da juya mashi k’eya, yace “aww bazaki kalleni ba?” Bata cemashi komai ba hakan yasa yace “toh naji dama inaso ince ki shirya anjima zamuje muyi sayayya kinga bikin mutum hudu ke gaban mu gashi ko Ihsan banga kin siyo mata komai ba…”indai da kud’inka ne bani so kuma ban zuwa”

 

 

tashi tayi da niyyar barin wurin,  saurin jawota yayi taf’ada saman kirjinshi don bayajin zai iya d’aurewa, kiciniyar kwace kanta tashiga yi amma takasa, don yasamata k’arfi dabazata iya kwantar kantaba,  shinshinarta ya shiga yi daga baya kuma ya Dora da kiss, tana jin haka ta bare mashi baki tana kuka da sauri ya d’ago yana cewa “menene?”

 

 

Cikin kuka tace “bana so kabari” yace “toh shikenan na bari amma sai kin yarda zamu fita” da sauri ta shiga daga mashi kai tare da kokarin tashi, yayi saurin kamota yace”haba andeejana ko kadan ne”  saurin  fizge hannunta tayi, tashige d’aki, dafe kanshi yayi a hankali kuma ya furta “ina sonki andeejanah”

 

 

Suna gama sallar Asr suka fita sayayya sukayi sossai don gaskiya ko kayan da khadijah zata sa a bikin ba kananan kudi ya kasheba har sai da khadijah tayi mashi magana, lokacin da suka dawo sun gaji sosai don har d’inki sai da suka bada don haka kowa ya shige wanka

 

 

A bangaren Laila kuwa tana jin baccin jiddan soldier ne gidanshi akwai tsaro sosai daba abin da zai hana akai mashi hari cikin daren nan saidai zata bari har zuwa gobe idan ya fito kamar yadda ta tsara

 

 

Al’amarin da ya hana Ashanty bacci shine ta sama ma kanta mafita akan cewa gobe da sassafe zataje ta gaya masu Jiddan komai tun kafin ya fita, da wanan shawarar bacci ya d’auketa

 

 

Da wuri yau ya gama shirinshi don yana so su tattauna da General akan tafiyar da zasuyi gobe saboda an turasu Lagos sai dai ba wani dad’ewa zasuyi ba duka 3 weeks zasuyi kuma lokacin da zasu dawo saura 5 weeks bikinsu Rafeeq,  shiyasa Rafeeq ketajin haushin tafiyar

 

 

Har yaje bakin k’ofa sai kuma yadawo saboda yadda yakejin gabanshi na fad’uwa, wurin khadijah ya nufa ya durk’usa gabanta tare da riko hanunta yace

 

 

“bakiyi Mani addu’a ba” a hankali tace “Allah ya kiyaye hanya” saboda yadda takejin gabanta na fad’uwa, kiss ya manna mata a goshi tare da fad’in “thanks” sannan ya fita da sauri

 

 

Abin tsautsayi motarshi na hawa bisa babban titi suka sha gabanshi tafiya yake ba tare da tunanin komai ba dai-dai lokacin da yashiga wata kwana suma suka shiga, duk bailura da yadda suke binshi ba, shigarshi kwanar daba kowa ke bin wurin ba kawai sai gani yayi ya buge mutum kamar daga sama

 

 

Da sauri ya fito yana salati,  bai k’arasa Inda Wanda ya kad’e yake ba sai jin saukar icce yayi akanshi nan ya…

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

         _*Mrs Abdul Sule*_

[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI DA’IMAN*

 

 

 

 

 

 

*WRITTEN BY*

 

 

 

          _*HALIMA Mk*_

 

 

 

 

 

 

 

DEDICATED TO

      SA’ADATU ALIYU KABUGA

 

 

 

 

 

 

 

         *Page136~140*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*D’*auke da ciki, tunanin tane ya katse da taji Laila na cewa “idan yazo ki bashi sannan ki gaya mashi bazan zubar da cikin nan ba saidai in ya aureni ko kuma na haife mashi abinshi

 

 

Murmushin yak’e khadijah tayi wanda yafi kuka ciwo tace “aidama yasanar dani komai a kanki, batun aure ma kicireshi a ranki dan bazai tab’a auren kamar kiba marar kamun kai wanda tarabarma guys darajarta a waje, don haka inkin haihu zaki iya kawo mana d’anmu mu rik’e”

 

 

Kallon baki isa ba Laila tayi mata tace “kece zaki iya rik’e mani d’ana, uhmmm airik’on d’a sai uwarshi balle ke asuwa dazan baki d’a mafi soyuwa ga ubanshi, wanda duk wanda za’a haifa mashi a bayanshi yake”

 

 

“uhmmm ni a matarshi ke kuma karuwarshi, don Haka zaki iya fitar mani daga gida tun kafin nasa a fiddaki”

 

 

Tashi Laila tayi ta nufi bakin k’ofa sannan ta juyo tace “zaki san kinyi da Laila” sannan ta banko mata k’ofar ta fita

 

 

Laila! Laila!! Khadijah ta shiga nanatawa yanzu abinda Jiddan zaiyi mata kenan lalle zaizo ya sameta wata kuma zuciyar tace kada ta yadda da abinda wannan k’adan garuwar bariki tafad’a tana sone kawai ta had’aki da mijinki dukda dai Namiji ba tabbas gareshi ba, haka dai tayi ta tunani har Jiddan yadawo

 

 

Tunda yadawo ta lura dashi a dirice yake itadai bata nuna mashi komai ba amma shi yak’osa su tashi kwanciya ya kwashi shokinshi san ranshi

 

 

Har ta kwanta yace ta tashi tayi alwala zasuyi sallah, bata mashi musuba taje tayo, yajasu jam’i, saida suka gama yayi mata tambayoyin da yasan bazasu caza mata kwakwalwaba tunda tana da matsala

 

 

Naman talo-talon da yayi mata alk’awari shi zasuci ranan daren farkonsu shi ya d’auko da niyyar ya bata, dandanan kwakwalwarta ta shiga rud’ani gani take kamar antab’a yimata irin haka a rayuwarta, lura da yanayin da take ciki yasa yamaida komai inda yake sannan yajata saman gado yana mata fira harya samu tamanta

 

 

Lokacin da yafara Romancing d’inta duk yarud’e dan ak’agare yake ita kuwa abinda Laila tafad’a shike mata yawo cikin kunne kamar lokacin abin yafaru, jitayi takasa d’aurewa hakan yasa ta tureshi ta tashi tsaye tana jada baya

 

 

Cikin tashin hankali yafara cewa “don girman Allah karyi mani haka, ba haka mukayi dake ba don Allah kitaimaka mani pls….. Kinji….. Koyaya ne kitaimaka mani kinsan ina k’aunarki sosai”

 

 

Girgiza kanta take tace “k’arya kake bazan iyaba bansani ba ko kana d’auke da wata cuta” daga haka bata k’ara cewa komai ba taruga da gudu ta shige d’akinta ta kulle

 

 

Maimaita kalamanta yake aranshi don yagaza gane inda zancenta ya dosa, tashi yayi yaje bakin k’ofar d’akinta yana kwankwasa mata amma tanajinshi yak’araci magiyarshi, ganin ba bud’ewa zatayi ba yasa dan dolenshi ya hak’ura yatafi

 

 

Da safe ma haka yayi-yayi da’ita ta bud’e amma tak’iya saidai aje mata break fast d’in da yahad’a mata tare dayimata rubutu a pepper sannan ya wuce d’akinshi don d’aukar key d’in motarshi, har zai wuce ya hango wata takadda bisa dress mirrow, d’aukarta yayi ya karanta, nan ya fuskanci inda fushin khadijah ya dosa, don ko yaga sunan Laila ajikin takardar, watau ita ta haddasa zargi a tsakaninshi da khadijah, kwafa yayi na inyaga Laila baison wane irin hukunchi zai d’aukar mata ba ta kuma gaya mashi yaushe ya kwanta da ita har yayi mata ciki

 

 

Tanajin tashin motarshi ta fito ta nufi dinning don tayi break fast, note d’in dataga ya aje mata ta d’auka takaranta _don Allah kici abinchi karki horar mani da kanki da yunwa_  tab’e baki tayi tace

 

 

“yo dama saboda kai zank’i cin abinci ne, kuma wallahi bazan yarda dakaiba har sana tabbatar da zargina, haka kawai kaje kasa mani cuta”

 

 

Saida tagama taje ta zauna palour tana tunanin abinda zatayi mashi ta bata mashi rai, wani Murmushi naga tayi daza’a iya kiranshi da na mugunta, tashi tayi ta shiga gyaran gidan tana gama ta wuce kitchen ta d’ora tuwo miyar kuka don tasan Jiddan baya son tuwo, saida tagama ta gyara kitchen d’in sannan taji ana knonking, lekawa tafarayi ta window taga Laila ce, komawa tayi kitchen ta d’auko muciya tana cewa “yau zakici ubanki karuwar banza mai bibiyar mazan mutane”

 

 

B’oye muciyar tayi a bayanta, ta bud’e k’ofar, yauma kamar jiya tana bud’e mata tashige ciki kamar gidan ubanta

 

 

Bata ankaraba taji saukar muciya bisa kanta nan take tafad’i sumammiya, igiya taje ta d’auko ta d’aureta sosai yadda bazata iya kwancewa ba, d’auko ruwa masu sanyi tayi ta watsa mata ajiyar zuciya tasaki ganin ta d’aurene yasa tacika da mamaki, bari tayi saida tadawo cikin hankalin ta sannan

 

 

Ta d’auko sessiors ta datse duka k’arin gashin dake kanta saida taga tamaidata kamar Namiji sannan ta kyaleta tace

 

 

“wallahi ina warning d’inki idan kika k’ara shigo mani gida saina illataki don gabama kaciya zanmaki inkika yi kuskuren k’ara shigowa gonata”

 

 

Duk wannan abin banda kuka ba abinda Laila keyi, shewa khadijah tayi tace “ashe ke iskancin naki k’arami ne tunda d’an wannan abu danaimaki yasaki kuka, kad’an ma kika gani don ni nan dakike gani nafiki iya hatsabibanci, don haka karna k’ara ganin maikama dake wannan layin bare kiyi kuskuren shigowa nan”

 

 

Kai tad’aga mata da alamun bazata sake haka ba tace “don Allah kiyi hak’uri kibarni natafi”

 

 

“zanbarki kitafi amma saina k’ara yimaki tabo” daga haka tashiga jibgarta kamar tasamu jakka saida tafasa mata baki sannan takira maigida ya fidda ta

 

 

Saida tagama hucin dukan da tayima Laila tace “saura kaima zakazo kasameni nasan yadda zanmaka” d’aki ta shige tayi wanka sannan ta zauna kwalliya sai lokacin ta lura da yad’auke takkardar, Murmushin mugunta tayi tace “uhmmmmm kenan dagaske ya santa”

 

 

Wani d’an k’aramin mini siket tasaka da wata ‘yar bingilallar riga wace za’a iyacewa da ita da babu duk d’aya sannan ta feshi jikinta da turare ta tafi palour ta zauna

 

 

Har suka tashi office Rafeeq na lura da yanayin shi saida ya bari bakowa inda suke sannan yace ma Jiddan  “meke faruwa kodai jikin khadijah ne?” shuru yayi sai kuma ya zaro takkada daga cikin aljihun wandonshi yamik’a mashi

 

 

Zaro ido Rafeeq yayi yace “kasani a duhu kayi mani bayanin da zangane”

 

 

Iyakar abinda yasani yagaya mashi yak’ara da cewa “nidai nasan bantab’a zina ba ballantana kuma Laila dako birgeni  batayi” Nisawa yayi yace “da’ace nasan inda zansameta wallahi dasai nasa ankulleta amma bakomai indai kare na yawo zabo na yawo wata rana za’a had’e”

 

 

Dafashi Rafeeq yayi yace “insha Allah nima zan tayaka nemanta kaidai kayi k’ok’arin wajen shawo kan mutuniyar taka”

 

 

Tana zaune taji k’arar shigowar motarshi, tashi tayi ta duba ta window don ta tabbatar dashi ne, fitowa yayi daga cikin motar taga damuwa k’arara a fuskarshi, Murmushin mugunta tasaki akaro na ba adadi, kwanciya tayi saman 3seater tayi wata kwanciya ta d’aukar hankalin wanda zaiyi arba da’ita, duk tabaza gashin kanta sannan ta rufe idonta kamar mai bacci

 

 

Yana shigowa yaji ba alamun motsinta sai tv dake aiki, tunanin tana d’aki ne yafad’o mai, saida yashiga cikin palourn sosai ya ganta kwance tana bacci, tsaye yayi yana tasbihi ga Allah daya azurtashi da mace abociyar kyau da kamala, Kallonta kawai yake yakasa koda motsawa sai had’iyar yawu yake Jiyayi k’afafunshi sunkasa d’aukarshi duk’awa yayi dai-dai saitin k’irjinta da yafi d’aukarmai hankali

 

 

Itakuwa duk tana ganin abinda yake, hamdala kawai yake furtawa cikin ranshi a hankali yakai bakinshi dai-dai k’irjinta yafara kissing, zumbur tamik’e tace

 

 

“malam menene haka kada kasake tab’ani katafi wurin karuwanka kayi dasu bani ba” dasauri yajawota ta fad’a k’irjinshi don kada ta gudu yafara cewa

 

 

“Pls… Pls…. Kada kiyi mani haka wallahi bantab’a kusantar wata ba balle har nayi mata ciki” fizge kanta tashigayi tana cewa “Ni zakayi ma dad’in baki wallahi banyardaba”

 

 

Ganin yak’i sakinta yasa ta gartsa mashi cizo sannan ta tashi tashige d’aki ta kulle, cikin rantako cewa take “nasan idan harda gaske kake baka neman mata zangani, don nasan inkanayi dole kafita kabiya buk’atarka”

 

 

Duk ‘yan mitina tana lek’ashi taga ko yafita batare da yasan tana hakan ba

 

 

Shikuwa bayan sha’awa yunwa ta isheshi don yasan da gayya tadafa abinda baici tashi yayi ya fita yaje restauranat ya siyo abinci yadawo, fitartashi ya tabbatar mata da zargin nata yazama gaskiya, wani irin kishi yataso mata zuciyarta na harbawa, harbata lokacin da hawaye ke silalowa daga idon ta

 

 

***

 

Tana fita wurin Ashanty ta wuce, kuka take gaban Ashanty tamkar ranta zaifita kyaleta tayi mai isarta sannan tace

 

 

“Laila yana ganki haka meyafaru?” kuka laila keyi tana gayamata abinda yafaru

 

 

“kema Laila nace ki hak’ura ni kinga tunda naga mutuwar da silly tayi naji tsoron duniya da abinda ke cikinta,, wallahi na tuba nakoma ga Allah nadaina sab’a mashi ta wannan hanyar yakamata kema ki tuba mukoma ga Allah

 

 

Kallon bazan tayi mata tace “amma Ashanty baki da hankali in tuba fa kikace, ai wallahi sai naga abinda yaturema buzu nad’i tunda tayi mani haka saidai murasa J d’in dagani har ita saina maidata bazawarar k’arfi da yaji”

 

 

Girgiza kai Ashanty tayi tace “Allah yashiryeki Laila”

 

 

 

 

 

 

 

       _*Mrs Abdul Sule*_

[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI DA’IMAN*

 

 

 

 

 

 

 

*WRITTEN BY*

 

 

     *HALIMA MK*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA

 

 

 

 

 

 

 

 

*page 146~150*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*J*iddan na tafiya kamar da 3 minutes sai ga motar Ashanty, parking tayi ta fito tare da gaida maigadi sanan ta tambayeshi ko matar gidan na nan yace mata “eh tana nan” kaitsaye ta shiga cikin gidan batare da tsoron komai ba

 

 

Tana nan zaune Inda yatafi ya barta, gaba d’aya tarasa me yasa takejin fad’uwar gaba  duk tabi ta damu sai jitayi ana knocking

 

 

Tashi tayi duk jikinta a mace taje ta bud’e k’ofar, murmushi Ashanty tayi tace “sannu mun tashi lpy” hakan yasa khadijah tadan saki fuskarta tace “lpy lau sai dai ban ganeki ba” cikin ranta ko tace wannan ina kuma ya kwasota

 

 

“Eh toh sai dai da zaki Mani izini  mu shiga daga ciki sai nayi maki bayani” “ba matsala” khadijah tace, shiga sukayi suka zauna sannan Ashanty tace

 

 

“Nasan baki sanni ba kuma kina mamakin yadda nazo maki gida da sassafe haka” daga kai khadijah tayi alamar haka ne sannan Ashanty taci gaba da cewa

 

 

“Toh gaskiya dole ce tasa nidai sunana Aisha k’awa ga Laila wacce tazo tace maki tana d’auke da cikin mijinki sai dai k’arya take kawai tana so ta biya buk’atar ta ne” nan Ashanty tayi ma khadijah bayanin duk abin da ya faru tun daga had’uwarsu da jiddan har yanzu da Laila ke shirin aiwatar da nufinta, sanan ta k’ara da cewa

 

 

“Ni yanxu daga nan Kano zan wuce na koma wurin iyayena sai dai nace Allah ya k’ara sada fuskokin mu da alkhari don haka kada ki bari jiddan ya fita idan ba haka ba d’ayan cikin biyu zai faru kodai ya biya mata buk’atarta ko ta kashe shi Ku rasa baki d’aya”

 

 

Bazan iya rubuta maku irin tashin hankalin da naga khadijah ta shiga ba, nan take jikinta ya d’auki rawa, muryarta na rawa tace

 

 

“Na shiga ukku wallahi yazun nan ya fita don Allah ki taimakeni” duk cikin rud’ewa take fad’in haka don bata ma San me yakamata tayi ba, da sauri Ashanty da itama ta shiga firgici jin jiddan d’in ya fita tace

 

 

“Yi sauri  ki kirashi ya dawo tun kafin yayi nisa” cikin kyarma don har wayar na neman fad’uwa khadijah ta d’auki wayar ta shiga kiranshi

          

 

***

 

 

 

Dafe kanshi yayi dai-dai Inda yaji an bugeshi hakan yasa yaji duniyar na juya mashi, ba tare da yayi wani yunkuri ba yaji an d’aureshi tare da cire bindigar dake sakale a aljihunshi

 

 

Cikin juwa yake kallon k’attin  mazan majiya k’arfi da sukai mashi wanan illar sai dai ya kasa magana, basu tsaya b’ata lokaci ba sukayi saurin sakashi cikin motar su sanan sukaja zuwa bayan gari Inda Laila ke jiransu

 

 

Zaune take ta sako k’afarta d’aya daga cikin motar, wasu arnakun kayane a jikinta Wanda ko a bariki bakowa ke iya saka irin kayanba sai kad’a key d’in motar ta take tana jiran isowar su

 

 

Ba b’ata lokaci sai gasu sun iso suka gurfanar da jiddan a gabanta, murmushi tayi ta kad’a idanuwanta sanan ta d’ora hanunta saman fuskarshi tana shafa sajenshi da yake mutukar birgeta cikin wani salo tace

 

 

“J meyasa kake son ka dinga wahalar dani, yanzu da ka bani had’in kai ko sau d’aya na d’an-d’ani zumarka da  yanzu mun wuce wurin” abinka da soldier sai ya kalleta a wulak’ance babu alamun tsoro a tattare dashi yace “ke jahilar ina ce da har kike tuna nin zan’iya had’a jikina da k’azamin jikinki, ni ban tab’a ganin jarababba irinki ba ko kina tunanin da kikasa aka kamoni shizaisa ki samu abi da kike so? Uhm ki guji ranar da zan kamaki”

 

 

Wata irin mahaukaciyar shewa Laila tayi sanan ta daure fuska tace

“Kana tunanin zan barkane, ita kanta wadda kake wulakantani a kanta saina maidata abin tausayi don haka tsaya ka gani” tana fad’ar haka ta zaro desire tablet tare da wani poison cikin kwalba sanan ta kalli Jiddan tace”dole ka sha kuma ka biya Mani buk’atata ko kuma in kashe ka”

 

 

“Toh ki kasheni mana sai me ko angaya maki ina tsoron mutuwa ne? Aiko da ban zama soldier ba, don nasan kona biya maki bukatarki ba barina zakiyi ba matata kuma baki isa ki mata abin da Allah bai nufeta da shi ba” ran Laila ne ya soma baci nan tasa wadanan k’attin suka shiga dura mashi desire tablet d’in

        

 

***

 

 

 

General ne ya kalli Rafeeq cikin mamaki yace “ina mamakin yadda har yanzu captain J baizo ba bayan jiya da kanshi yace Mani zai shigo da wuri anya lpy?”Rafeeq ya Dan kad’a kai sannan yace “Nima abin da nake tunani kenan but bari in kirashi inji”

 

 

Rashin dace aka samu dai-dai lokacin da yake kiranshi itama khadijah tana kiranshi hakan yasa  ya kasa samunshi itama haka, koda yaga ya kira sau biyar bai samu ba sai yace ma General

bari yaje gidan yaga ko lafiya, har ya je bakin motarshi sai kuma ya tsaya yana kiran no d’in khadijah yaga ko ita zai samu but still bai samuba saboda itama lokacin shi take k’ok’arin kira ta gaya mashi gashi ta kira Mujaheed but switch off sai Ashanty ce tace tak’ara kiran Jiddan d’in

 

 

Duk cikin tashin hankali take kiran sai dai yanzu tayi sa’a tana ringing, amma ba’a d’auka ba

 

 

Mujaheed ne ya karaso Inda Rafeeq yake yace “har yanzu J baik’arsoba?, gashi inta kira dagashi har khadijar amma ban samu ba, ko kai ka sameshi?”

 

 

“A’a ni wayata kashe ma take but mu tafi kawai”cewar Mujaheed, daga haka sukaja motar suka tafi

            

 

Idanunshi har sun canza kala saboda maganin ya fara mashi aiki, koda Laila taga haka sai ta fito daga cikin motar fuskarta dauke da murmushi ta tsugunna gabanshi tana shafa fuskarshi, cikin wani salo ta furta “J”

 

 

Aiko dagowar da zaiyi ya watsa mata uban miyau a fuska, da mamaki take kallonshi sai kuma tayi murmushi tare da goge fuskarta tace “kusa Mani shi cikin mota”

 

 

Duk da k’arfi irin nasu amma sun kasa sa jiddan cikin motar saboda yadda yatirje kuma hannuwanshi a d’aure suke ganin ya k’iya yasa sukayi niyar d’aukar shi gaba d’aya amma sai ya shiga cizon su

 

Cikin fushi babbansu ya zaro bindiga zai harbeshi, Laila tayi saurin dakatar dashi sanan ta dauko wanan poison din ta mika masu tace “ba sai kun harbeshi ba”

 

 

Suna k’ok’arin d’ura mashi sai wayar shi ta hau ringing, Laila ce ta d’auki wayar taga ansa PRINCESS murmushin keta tayi tace zakayi ban kwana da matarka kafin ta biyo ka, tana fad’in haka tayi receiving call din tare da sa mashi a kunne

 

 

Cikin wahalaliyar murya yace “Khadijah…sai Laila tayi saurin janye wayar, ta fashe da dariyar da ta k’ara tada ma Khadijah hankali sanan tace

 

 

“Kina magana da Laila don haka zaki iya zuwa ki d’auki gawar mijinki” tare da siffanta mata wurin daga haka ta kashe sanan suka shiga d’ura mashi poison din

 

 

Saida suka tabbatar yasha sannan suka tafi suka barshi, dukda basu Sani ba Dan kad’an  yasha amma nan take ta fara mashi illa saboda gubar mai k’arfi ce

 

 

Tashin hankali Wanda ba,a sa mashi rana, jin abin da Laila ta fad’a batasan sadda ta saki wayar ba ta fad’i k’asa tare da tarwatsewa

 

 

Da gudu ta fita Ashanty na tayi mata magana amma ina batasan tanayi ba, Allah ya taimaka Riga da wando ne na Pakistan a jikinta kuma mayafinsu na bisa kanta

 

 

Tattara wayar Ashanty tayi ta had’a tare da kunnawa sanan ta aje saman center table ta fita, gate man ta tambaya ko yaga Inda Khadijah tayi

 

 

Yace eh yaga ta fito da gudu ta tsaida taxi amma baisan Inda ta tafi ba, godiya tayi mashi ta shiga  motar ta takama hanyar Kano aranta tana cewa

 

 

“Nasan idan wani Abu ya samu Jiddan ko Khadijah ni za,a tuhuma Inda Laila take bayan ni taimako nayi ” haka ta tafi tana fatan Allah kada  yaba Laila nasara

 

 

Mai taxi d’in take cemawa ya k’ara sauri but gani take kamar ba tafiya yake ba, wani irin birki taji yaja sakamakon go slow din dake gaban su, sanadin wani accident da akayi da sauri mai taxi din ya fita don gane ma idonshi

 

 

Ganin babu hanyar da zasu wuce gashi sun kusa isa yasa ta fito da gudu batare da tabi takan kowa ba

 

 

Gudu take sosai tana kuka ba abin da take tunawa sai lokacin da suna yara yanayi mata wasa, yana dagata sama tana dariya a hankali ta fara tuna wasu maganganunshi cikin kunnuwanta kamar haka:

 

 

“Kinsan bazan tab’a cin amanarki ba …” Meyayi zafi zaki rinka horar da ruhimmu haka?.. Aw bazaki kalleni ba?.., ina sonki har gaba da abada…

 

 

Takalminta ne ya katse hakan yasa ta ta tsaya sanan ta cire taci gaba da gudun ita dai burinta ta isa Inda Jiddan yake

 

 

Jitayi ta taka wani Abu hakan yasa ta tsaya sai taga Ashe wata katuwar kwalbace ta taka gashi taji mata ciwo sosai amma saboda tashin hankali ko zafin bataji ba sai cire kwalbar tayi taci gaba da gudun

 

 

Ganin duk Inda ta taka sai yayi sawun jini yasa mutanen da take wucewa suke mata magana amma Sam bata San sunayi ba saboda saura k’iris  ta isa Inda yake

 

 

Haka taci gaba da gudu kamar ranta zai fita, sai dai kash! Tana zuwa ta tarar da Jiddan …

 

 

 

 

 

 

 

 

 

     *_Mrs Abdul Sule_*

[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI DA’IMAN*

 

 

 

 

 

 

*WRITTEN BY*

 

 

     *HALIMA Mk*

 

 

 

 

 

 

 

DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA

 

 

 

 

 

 

 

 

*PAGE 151-155*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*S*una isa gidan Jiddan Rafeeq ya danna horn maigadi ya bud’e masu suka shiga ba tare da sun tsaya tambayarshi komai ba

 

 

Parking sukayi tare da shiga cikin gidan, tsaye sukai sunata sallamma amma shuru, ganin shurun tayi yawa yasa suka shiga cikin palour

 

 

Tunda Rafeeq yaga k’ofar a bud’e take bayan yasan Khadijah kullewa takeyi saidai ayi knocking sannan tabud’e, yasan ba lafiya

 

 

Ganin suna takiransu ita da Jiddan shuru alamun ba mutum cikin gidan yasa Mujaheed yace su shiga bedrooms su duba sugani ko suna ci, saida suka fara k’wank’wasa wa sannan suka shiga amma ba kowa a ciki

 

 

Haka suka zagaye ko ina na gidan amma ba kowa, mai gadi  suka tambaya ya gaya masu iyakar abin da yasani, nan Rafeeq da Mujaheed suka tabbatar daba lafiya, amma abin da ya d’aure masu kai wacece wadda maigadi yace tazo da safe haka?

 

 

General suka kira suka gaya mashi halin da ake ciki da kuma abinda suke zargi sannan suka shiga motarsu

 

 

Maimakon su biyo ta hanyar da sukazo sai suka bi ta wata hanyar wadda itace Jiddan yafibi, basuyi tsammani ba sai sukaga motar Jiddan a kan hanya gashi wurin ba kowa

 

 

Da mamaki suka fito daga cikin motar don su tabbatar ma Kansu, wayar Rafeeq ce tahau ringing, dubawa yayi yaga general ne hakan yasa ya d’auka da sauri

 

 

A d’ayen b’angaran general kema Rafeeq bayanin cewa shima yakira wayar Jiddan and’auka amma ba’ayi magana shine sukayi tracing sungano inda yake yanzu haka antura soldiers suje wurin

 

 

shima Rafeeq nan yake sanar dashi inda suka ga motar Jiddan amma suma yanzu zasu nufi wurin tunda kusa suke

 

 

Suna katse wayar Rafeeq yaja motar, shi kuma Mujaheed ya d’auki waya don k’ara kiran jiddan

 

 

***

  

   

Tana isa ta tarar da Jiddan kwance dukda bai mutu ba amma har miyan bakinshi ya tsinke don gab yake da yarasa rayuwar shi, da sauri ta ruga ta rungume shi tana kuka tare da cewa

 

 

“Don Allah yayana ka tashi Kada ka barni don…” Wayar Jiddan dake gefece ta d’auki ringing cikin kyarma ta kai hannu ta d’auka duk da irin jirin da takeji

 

 

“Hallo! Hallo! Jiddan…”Mujaheed.. Mijina..ya..” Sai kuma ta sume saboda tashin hankali ga kuma jini mai yawa da ta zubda

 

 

Mujaheed da yaji abin da Khadijah ta fad’a kuma yagane itace amma sai dai yaji shuru, katse kiran yayi yasake kira but ba’a d’auka ba sai ya kalli Rafeeq yace

 

 

“Duk yadda akai Khadijah da Jiddan suna tare, saidai ga dukkan alamu akwai babbar matsala a tare dasu” take Rafeeq yak’ara speed d’in motar domin isa inda general yayi mashi bayani

 

 

Suna isa Rafeeq ya fito da sauri ko rufe k’ofar motar baiyi ba ganin Khadijah da Jiddan kwance a k’asa, left hand d’insu da ke d’auke da zoben su rik’e da juna, ga alamun zubar jini a wurin

 

 

Bai San sadda ya isa wurin su ba ya fara girgiza su yana cewa “Jiddan! Jiddan!! ..Khadijah!!! Khadi…”dai_dai lokacin wasu bak’ak’en Hilux suka iso, sojojin dake ciki su fifito, Mujaheed da zuciyar shi ta gama karaya yayi saurin ce masu

 

 

“Kusa su mota mu tafi asibiti” da sauri suka Sara mashi tare da cewa “OK Sir” daga haka suka kwashesu sai asibiti

 

 

Da hanzari aka karb’esu ba bata lokaci suka gano matsalar Jiddan na take suka shiga tsotso gubar ta tare dayi mashi wasu allurai hatta hancin shi sai da suka rink’a samashi wani Abu yana fiddo da gubar tare da jini

 

 

Saida suka d’auki lokaci mai tsawo akan Jiddan sannan  likitocin suka fito, sai d’aya daga cikin su ne ya tsaya yi masu Rafeeq bayanin cewa

 

 

“Shi jiddan poison yasha saidai ko wacce guba da irin illar da takeyi ma mutum, k’arshe ma Ana iya rasa rayuwa indai ba’ayi hanzarin d’aukar mataki akan haka ba, toh amma shi Jiddan Alhamdulillah babu abinda ta lalata mashi ko’a cikin shi komai lafiya lau yake saidai zai Dan dad’e kafin ya farfad’o, koda ya tashi ba lalle bane ya iya motsa ko ina na jikinshi sai a hankali zai warware”

 

 

Numfashi Rafeeq ya sauke sannan yace “ita macen da aka kawosu tare fa?..”eh ita ba Wata babbar matsala bace ba, taji ciwo ne sosai a k’afarta Wanda yayi sanadin zubar jininta mai yawa ga alamun tashin hankali a tattare da’ita don haka yanxu anyi mata dressing sannan akwai wasu blood tonic dazamu bata insha Allah zatayi replace blood d’in data zubda”

 

 

Daga haka doctor d’in ya tafi shi kuma Rafeeq ya kira general ya sanar dashi abinda yasamu Jiddan

 

 

Yayi matuk’ar girgiza najin cewa Jiddan guba yaci, take Abinka da babban soja military ta aiko da soldiers don bada tsaro ga Jiddan, musamman jin cewa poison aka bashi

          

 

***

 

 

Adaidaita sahu ce wato keke napep tayi parking a k’ofar gidansu Khadijah, fitowa sukayi su ukku tare da sallamar mai napep, kayane da yawa suka siyo daga kasuwa ga alamun gajiya a tattare da su, Ihsan  ce tafara cewa

 

 

“Toh kun wani tsaya Ku d’auka mu shiga gida ko” Samra da tafi kowa nuna gajiya tace “keni wallahi gida zan wuce kawai kije da kayan ajima sai mu shigo mu tattauna”

 

 

“Toh uwar son jiki wlh Yaya muhsin ya bani dake, ita kuma waccan ta wani yi shuru sai tunani take “cewar ihsan dake k’ok’arin d’aukar kayan ta shiga gida, girgiza kai Seemah tayi tace “uhm Allah sarki yaya SS dayana nan nasan bazamu sha wannan wahalar ba” jikinsu ne yayi sanyi kafin ihsan tace

 

 

“Kuyi hakuri mu daina wannan tunanin addu,ar mu yafi bukata” Samra dakeda saurin kuka har idanun ta sun ciko tace “naso ace Yaya yaga ranar auran mu amma Allah bai nufa ba, gashi kuma yanxu aure zai rabamu” dafata ihsan tayi tace “kiyi hakuri Seemah ai muna tare” cewar Ihsan

 

“ki daina kuka ni yakamata nayi tunda ku duk Kaduna za,a kaiku Niko ina nan katsina ni kadai don haka zan gaya ma ummi sai na raka Ku sannan indawo akaini” Samrah tace “lalle Seemah toh munji amma ai itama d’auketa Rafeeq zai dungayi yana tafiya da’ita Abuja”

 

 

Ihsan tace “toh saiki bimu” daga haka hirar tasu ta koma wasa kafin kowa ya shige gida

 

 

Da sallamar ta ta shiga gida saidai tayi turus ta tsaya jin wayar da baba keyi ga Mama dake gefe ta kuka, hawayene suka shiga zirarowa daga idanta, aranta kuwa cewa take yanzu kuma meyasamu yaya Khadijah, kullum suke nan cikin jarabtar ubangiji, saurin istigifari tayi ganin tana neman jafa kanta cikin halaka

 

 

Babane ya ida wayar dagaya ma Rafeeq cewa lnsha Allah yau zasu biyo jirgi su taho sannan ya aje yana kallon Ihsan da tasaki kayan hanun ta tana hawaye yace

 

 

“Haba Ihsan ba kuka zakiba keda baki tabbatar da kome ya samesu ba” a hankali tace “meya faru?” saida ya kwantar mata da hankali sannan yayi mata bayani, itakuma ta d’auki kayan da ta shigo da su ta nufi d’aki

 

 

Kallon mama yayi yace “ji don Allah yadda kike hawaye duk kin tada ma yarinya hankali, yanzu je ki d’auko Mani passports d’inku” zuwa tayi ta d’auko sanan tayi mashi Allah ya kiyaye kafin ya fita

 

 

K’arshe dai basu samu tafiya ba sai k’arfe 7:30pm, jirginsu yad’aga zuwa garin Abuja

 

 

 

***

 

 

General ne ke gaya ma Rafeeq cewa tafiyarsu ta gobe tana nan sai dai an cire Jiddan kuma za’a cigaba da bashi tsaro har ya warke, shidai Rafeeq komai ya dagule mashi kanshi kawai ya iya d’agawa sannan ya fita

 

 

Asibiti ya nufa dayake Mujaheed nacan, yana zuwa  Mujaheed yaja hanunshi yace zauna muci abinci, ba musu ya fara ci don yunwar dayakeji saboda tun safe rabonshi da abinci, daga shi har Mujaheed d’in hakalinsu ba kwance yake ba

 

 

Da misalin k’arfe 8:15pm su Ihsan suka iso Abuja lokacin iyayen jiddan sun dad’e da zuwa harda Islam

 

 

Kowa ka gani fuskarsa da damuwa, sai lokacin allurar baccin da akayi ma khadija ta saketa ta tashi

 

 

Koda ta ganta a gadon asibiti gasu Mama kusa da’ita, sai ta fara hawaye momy ce ta shiga lallashinta, a hankali saboda yadda take jin bakinta yayi mata nauyi tace “ina ya Jiddan?.. “Yana Nan lafiya lau bacci ma yake” cewar momy “toh Ku kaini in ganshi”

 

 

Sai lokacin Mama tayi magana tace”ki bari kici abinci mana” shiru tayi batace komai ba, sai Ihsan ce ta had’o mata abinci itakuma Islam ta taimaka mata ta zauna

 

 

Saida ta gama cin abincin tayi sallolin dake kanta sanan aka kaita wurin Jiddan, da yake duk mazan suna can koda aka shiga da’ita sai ta sadda kanta k’asa tana hawaye

 

 

Abba ne yayi mata bayanin abin dake damun Jiddan d’in tare da kwantar mata da hankali, sannan itama tayi masu bayanin duk abin da ya faru har taje inda Jiddan yake, nan kowa ya shiga jimamin abinda ta fad’a

 

 

Rafeeq ne yayi gyaran murya yace “Abba kada Ku damu muna nan munsa ana bincike da yardar Allah za’a kamota, Baba yace “toh Allah ya taimaka” nan Rafeeq yayi masu bayanin tafiyar su ta gobe, sannan kowa yayi masu fatan alheri

 

 

Washe gari tunda safe kafin su Rafeeq su tafi sai da suka zo asibitin sukayi ban kwana da kowa Wanda har yanzu Jiddan baifarka ba

 

 

Har bakin mota ta rakoshi fuskar ta cike da damuwa, dakewa yayi don kada taga tashi damuwar yace “haba my pretty ki daina damuwa haka insha Allah duk zasu warke kuma nima 3 weeks ne kwai zanyi in dawo don haka Dana samu dama zan kiraki kinsan ruwa zamu shiga”

 

 

Dago idanun ta tayi suka had’a ido sai kuma ta Sadda kanta k’asa tare dayi mashi fatan alkhairi  takoma cikin asibitin

 

Girgiza kai yayi yace “Ihsan kenan” daga haka shima ya shiga mota Yana jiran Mujaheed ya gama ban kwana da Islam

 

 

_nace su Rafeeq kenan bacin damuwa da yanzu ya farayi ma Mujaheed sharri_

 

 

Kwana d’aya da tafiyar su Mujaheed, zaune take bakin gadonshi amma ta tafi duniyar tunani, da yake ita kad’aice a d’akin

 

 

Jitayi kamar ana shafa hanunta da sauri ta juya ta kalli jiddan sai taga….


*page 156-160*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*T*ana juyawa sai taga jiddan ne ke shafa hannunta yana murmushi, da sauri ta rik’e hannun nashi, kwalla cike da idonta tace “yayana katashi? yaka…” girgiza mata kai ya shiga yi alamun kada tayi kuka

 

 

Bata iya hana hawayen da take tarewa zubomata ba, bayan hannunta tasa tana sharewa, k’ara matse hannunshi tayi tare da cewa “na daina yayana, mekake so yanzu?” Dan k’aramin murmushi yayi tare da d’aga hannunshi na Dama ya shafi gefan fuskarta ba tare da yace komai ba

 

 

Rik’e hannun nashi tayi tace “bari in kira doctor” bai musa mata ba ta tashi taje  kiran doctor, yana lura da k’afarta datake d’angyashi, nan take yaji wani iri don yana da tabbacin ta silarshi taji ciwon,donkuwa koda yabaro gida yasan lafiya lau k’afarta take

 

 

Bayan doctor ya gama dubashi ya kalli Khadijah yace” komai yana tafiya normal sai dai wasu jijiyoyin jikin shi da suka rik’e, suma a hankali zasu warware sannan yanzu ki had’a mashi madara da da d’an ruwan d’umi a bashi yasha” daga haka ya fita ita kuma ta shiga had’a madarar

 

 

 

Zaunar dashi tayi jikin gadon tare da sa mashi pillow a bayanshi amma hakan bai mashi ba sai da ya kwantar da kanshi saman kafad’arta, ba yadda ta iya a haka ta fara bashi madarar yanasha

 

 

Abba ne da Momy suka shigo don doctor ya fad’i masu tashin shi, jitayi kamar ta nutse don kunya shikuwa Jiddan dad’in hakan yakeji

 

 

Gaidasu tayi ta fara kokarin tashi daga jikinshi amma duk yabi yak’ara langab’e mata

 

 

Abba ne yalura da atakure take ganin suna cikin d’akin gashi shikuma gogan sai wani k’ara kwantawa yake jikinta, Kallonta Abba yayi yace

 

 

“eh zamanki cigaba dabashi” hakanan tacigaba dabashi, ganin duk a takure take yasa su Abba suka fita sukabar masu d’akin

 

 

Jitayi Jiddan na k’ara shigewa jikinta hakan yasa ta kalleshi ta gane bacci yake ji, d’an murmushi naga tayi sannan ta gyara mashi kwanciyar tana shafa kanshi har yayi bacci

 

 

 

Yau kimanin kwana biyu da farfad’owar Jiddan amma bai iya aiki da hannunshi na hagu ,tafiya ma da kyar yakeyi duk Khadijah ce ke taimaka mashi duk da itama ba wani iya taka k’afarta take sosai ba

 

 

Sukuwa su Mujaheed da Rafeeq tun tafiyarsu basu kira ba

 

 

A b’angaren su Ihsan suma sun koma katsina, saboda gobe ne za’a sallami Jiddan daga Asibiti don jikin nashi yayi sauk’i, su Abba ma gobe zasu wuce kaduna

 

 

Fitowar shi kenan daga toilet sai ga Khadijah ta taho da sauri don ta rik’eshi, dariya ma abin ya bashi yace “lalle Khadijah mai kika maida nine? Kuma idan fad’uwa zanyi ni dake wa zai rike wani” turo baki ta shiga yi sannan tace “yo kaima kasan yanzu na fika k’arfi”

 

 

yace “Allah ko! Kamar haka?” Saiji tayi ya jawota da k’arfi zuwa jikinshi, da sauri tace

 

 

 

“Na yarda wlh ka fini k’arfi yi hakuri” tayi maganar cike da shagwaba da salonyin kuka, bai saketa ba sai yaci gaba da kallon cikin idonta, itama shi take kallo

 

 

Hannuwanta duka biyun tasakalo saman wuyanshi tare da yin tantad’o saboda ya fita tsawo, bata daina kallon cikin idonshi ba shima haka, tace

 

 

“Yayana pls kayi hakuri da abin da……..shihhhhh! “bakiyi Mani laifin komai ba andeejah na nidai fatana Allah ya barmu tare” ” toh amma ya..” Bata ida ba saboda ganin yadda ya tsure bakinta da ido yana k’ok’arin had’awa da nashi

 

 

Da sauri ta sakeshi hakan yasa ta dira ma kafarta mai ciwo ayayin da hannunshi mai lafiya yake bayan kanta saboda yayi niyyar kissing dinta

 

 

Zafin ciwon da taji ne yasa ta tapi zata fad’i, roko rigar jiddan tayi batare data Sani ba, shi kuma bai lura da fad’uwa zatai ba gashi ba wani kwari jikinshi ke akwaiba, Kawai sai ya bita

 

 

Lokacin da ta isa k’asa ta d’auka zataji ta bige, amma sai taji sab’anin haka saboda hannun Jiddan dake bayan kanta

 

 

A bangaren Jiddan kasa tashi yayi sai wani kallon kwayar idonta yake har hacinsu na kokarin gogar na juna, itama haka take kallonshi dake nuna kauna da tausayi a tsakanin su

 

 

Sun d’auki kusan 3 minutes a haka, a hankali ta sauke idonta k’asa shiyasa Jiddan ya dawo cikin hankalin shi, dakyar ya samu ya tashi don shi hannunshi Wanda ya tareta yadan bugu amma bai bari ta gani ba

 

 

Ganin jikinta yayi sanyi yasa yajata saman gado ya shigayi mata wani salo nadaban, neman zasu fita wata duniyar yasa khadijah ta ankarar dashi

 

 

 

 

 Waya ta gama yi da Islam cikin damuwa ta kalli su Samra tace “itama Mujaheed bai kirata ba Allah dai yasa lafiya” Seemah tace “lalle pretty kamar bakece soyayya take ba haushi ba ke da zaki rinka wata ukku nan gaba baki ganshi ba” hararar ta Ihsan tayi, Samra tayi saurin cewa “kyaleta addu,a zamu rinka yi masu”

 

“Ni ba dad’ewar bace damuwa ta at lease kasan halin da mutum yake ciki,” sai Seemah tace “haba matar sojan ruwa sorry” tare da kama kunnuwanta

 

 

 

***

 

 

“Aikin banza! kuma kunsan fad’i kawai kuke, taya zakuce na biya Ku kud’in Ku bayan kun kasa

kashe shi da anyi magana kuce sojoji ke tsaron shi, bakusan idan Jiddan ya tashi ba na kad’e, bani kad’ai ba harda ku” tare da binsu da wani wulak’antaccen kallo

 

 

Wani daga cikin yaran yace “toh mu ina ruwan mu, bayan munyi niyyar kasheshi  kika hana”

 “Kuje kukashe Captain J idan kuna buk’atar kud’in ku, domin kashe shine kawai kwanciyar hankali garemu” cewar Laila dake zaune saman kujera tana kad’a k’afa

 Babban cikinsu ne, da tunzuwansu baice komi ba, takowa yayi har gaban Laila yace “mikika ce”

  “cewa nayi bazan……….. Bata idaba yakifa mata mari, zumbur tamik’e tare da cewa “nika mara” batayi aune ba saiji tayi and’ora mata bindiga akai

  Ganin mutuwar ta muraran yasa tashiga bashi hak’ura, amma ina zuciyar rashin imani tana kusa gareshi yace “kafin mu kasheshi ke bari mufara rage mugun iri, don barin irinku cikin al’umma hatsari ne” take yasakar mata harsashi a kirji

 Nan take tafad’i, tadafa wurin da’aka harbeta tayi tana wata irin kuwa, bata d’auki lokaci tana tanayi ba rai yayi halinshi, bakinta na zubda wani irin miyau, k’asanta na zubda wani ruwa mai d’oyi

 Ganin tabbas sun shek’ata barzahu yasa suka kama gabansu suka barta nan yashe a banza { _Allah yasa muyi kyakyawan karshe_ }

 _*INA BA MAKARANTA WANNAN LITTAFIN HAK’URI NAJIN SHURU NA KWANA BIYU, UZURIRIKA NE SUKAYI MANI YAWA, AMMA INSHA ALLAH NESA TAZO KUSA, PAGES KAD’AN YARAGE IN KAMMALA CIKIN AMINCHI ALLAH*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button