HALIN GIRMA 10

Halin Girma 10
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb
***Be ji sallamar ta ba, sai ganin ta yayi kawai a dakin bayan a zahiri tayi sallamar amma saboda baki daya hankalin sa na ga tunani shiyasa be ji ba sam.
“Ya Khalil wai a kawo maka abinci…”
Ai kafin ta karasa ya daka mata uwar tsawa
“Uban abincin, dallah Malama karki dame ni.”
“Toh… Me yayi zafi? Hajiya ce ta aiko ni ai.”
“Fitar min daga daki!” Yace yana tasowa, da gudu ta juya tana dariya, sai da ta ga ta fice sannan ta daga murya tace
“Bani na kar zomon ba…”
Ransa ne ya sake baci, ya bigi kofa yana komawa ya fad’a saman katifar sa yana jin kamar yayi ta cizon kansa.
A falo ta samu Hajiya ta zauna tana haki
“Allah ya taimake ni na kusa cin duka, daga tambaya kawai ya hayayyako min Hajiya.”
“Toh wai ko dai Khalil tsokana yayo ne aka tattaka shi, kinsan fa Khalil ba dai tsokana da cika baki ba.”
“Alamu dai sun nuna Hajiya, fad’a ya takalo da yafi karfin sa wallahi, gashi nan yaki fad’an abinda ya faru.”
“Toh Allah ya kyauta ” Hajiyan tace tana tashi ta fita zuwa dakin nasa.
***Tana tsaye a bayan kitchen dinsu, wanki ta gama tana ta sauri saboda kwana biyu bata maida hankali zuwa islamiyya saboda abubuwan da suka sako kai, tana wankin tana tunanin maganar da sukayi da Abba da ta zama tamkar bitar karatu haka take yin sa, takun tafiya taji, ta juyo sai taga Abban a tsaye yana duban ta, da sauri ta dan russuna,
“Abba sannu da zuwa.”
“Wanki ake ne?”
“Na’am.?” Tace tana zaro ido sanin cewa ba da sanin sa take wankin ba, musamman ya samu almajiri yake wanke musu kaya ita da Zeenat da Marwan yake biyan shi ta hannun Mama, duk da yasan dole zasuyi wanki irin kayan ciki da abubuwan da ba za’a iya bawa me wanki ba, amma kuma tarin kayan da ya gani a wajen da ya gane na Marwan ne sai wasu na Maman ya saka ransa mummunan baci, har a jiya sai da Maman ta karbi kudin wanki a wajen sa da zumar yau me wankin zaizo karbar kudin sa ya kuma bata babu musu. Yanayin sanyin garin zai yi wuya wajen wanki musamman da tun da dadewa yasan fatar Iman din bata son wahala idan tayi wanki hannun ta kanyi ja sosai, shi kuma Allah ya hore masa son yaya Kuma gasu ba wai yawa ne dasu ba shiyasa duk wani aikin wahala baya son siyi duk da ba wai kwata kwata ba zasuyi komai ba, amma kamar wanki yana ganin be kamata shima a saka shi a cikin aikin mata ba, mata na wahala da aikin gida kula da yara da girki wankin aka dauke musu zasu samu sassauci. Matsowa yayi ya sake leka kayan kafin ya girgiza kansa ya juya bayan yace
“Ki bar wankin nan kizo ki wuce ciki.”
Sakalo tayi a tsaye tsoro na kamata
“Bakya ji ne?” Ya daka mata tsawa, da sauri ta bi bayansa har cikin gidan, dakin su taga ya wuce ya kwankwasa sannan ya tsaya
“Waye?” Zeenat tace tana daga kwance cikin rufa, a yadda tayi maganar zaka gane knocking din ya takura ta, sake kwankwasa wa yayi sannan ya tura kofar da sallama, be shiga ba, ya tsaya a kofar yana karewa dakin kallo, gadon zuwa katifar dake shinfid’e a kasa da ta tabbatar masa da ta Iman din ce. Tuna lokacin da ya bada kudin gadajen nasu yace a siyawa kowa nasa amma sai Mama tace daya ya ishesu me dan girma saboda hakan zai sake shakuwa tsakanin su,da wannan yayi amfani a ganin sa hakan ne ya kuma dauki hakan a matsayin soyayyar da Maman ke wa yar tasa. A yadda yake jin zuciyar sa a lokacin zai iya yin komai, sai kawai ya fice daga gidan gaba daya ba tare da ya koma daki ba.
Tsoro ne ya kama Iman musamman da bata san me zata ce wa Maman ba akan wankin, shiryawa tayi cike da fargaba ta tafi makarantar tana fatan koma menene ya taso ya zama daidia kafin ta dawo dan a rayuwar ta, ta tsani tashin hankali ko kad’an.
Rabi da kwata bata gane kan karatun ba, haka dai ta taho gidan tana ta zulumi, tana shigowa ta ganshi a tsaye ya harde hannayen sa a gadon bayan sa yana kallon kofar shigowar. Shigar jikin sa ta bi da kallo zuwa gyaran da yayiwa fuskar sa, murmushin da ta gani kwance a fuskar tasa, ya saka ta samun nutsuwa har ta karaso wajen da yake a tsaye.
“Ashe kina kusa da shigowa, naji a jikina.”
Murmushi tayi kafin tace
“Sannu da zuwa.”
“Yawwa, ya hanya?”
“Alhamdulillah wallahi.*
” Akwai wanda ya kalleki da kina tahowa? Idan akwai fad’a min naje na same shi.”
Sosai ya bata dariya,
” Kai… Babu kowa fa, ya gida yasu Mama?”
” Mama? Ammi muke ce mata, tana nan lafiya tace ma na gaishe ki, na gaida wacce ta kwace mata yaronta kafin tazo haka tace.”
Rufe fuskar ta tayi tayi yar dariya
” Allah sarki, ina amsawa nagode.”
” Itama ta gode, tace ta matsu ta ganki.”
“Watarana zata ganni in Sha Allah.”
“In Sha Allah, very soon.”
“Abba Babba yace idan kazo ka shiga ciki.”
” Da gaske? Kice na zama dan gatan Abba.”
Dariya tayi
” Naga alama kam, Abba ya yarda da kai sosai.”
” Allah sarki, ai yana da kirki sosai.”
” Sosai.” Tace
” Bari na bud’e maka, chan ne seat room din sa.”
” Owk.” Yace ya harde a jikin ginin yana kallonta, har ta bud’e ta dawo sannan ya bita a baya yana admiring steps dinta zuwa ciki.
A kofar dake farkon kofar ya zauna ita kuma ta shiga ciki, yana zama Aliyu ya shigo da ruwa a tray, ya ajiye ya gaishe shi sannan ya fita, ruwan ya dauka ya sha sosai sannan ya kalle ta, gefe take kallo tana wasa da jikin kujerar da take kai.
” Zahraah, tafiya ce ta kamani, ba zan iya wucewa ban sanar miki ba, ba wani dadewa zan ba in sha Allah, inaso kafin lokacin da zan dawo mu sake fahimtar juna sosai, idan na dawo sai a shigo da magana me karfi, bana so a ja lokacin.”
” Allah ya kiyaye ya tsare, ya dawo da kai lafiya.”
” Amin ya Allah, Amin Amin Zahraah Nagode”
Shiru ne ya dan shiga tsakani, shi yana kallon ta yana sake ganin ainihin kyawun ta, ita kuma ta tafi tunanin Allah yasa ya dawo din kar taji shiru idan ya tafi, har zuciyar ta bata son tafiyar tasa, amma kuma ya zatayi? Ba zata hanashi ba ai.
“Ina wannan yayan naki da muka hadu ranar nan? Har ya korar min ke?”
” Uncle Khalil?” Tayi dariya
” Auw sunan shi kenan.”
” Eh kanin Mama ne, a nan gidan ya taso kafin ya koma gida.”
Gid’a kansa yayi kamar be sani ba
” Shiyasa ya nuna min iko kenan.”
” Uhum.” Tace kawai bata ce komai ba.
“Yana ina kuwa?”
“Kamar dai ya koma, naji dai mama na fad’an ya tafi be sanar ba.”
“Ai be isa ya sanar.”
“Na’am?” Tace tana kallon sa
“Sorry ba komai.” Ya maze kamar be ce komai ba, be san maganar zata fito ba shima.
” Bari na gudu, kar nayi rana.”
Mikewa tayi
” Daga nan zaka wuce?”
” Eh gaskiya, idan na koma gida na koma baya.”
” Ok ina zuwa.”
Ta fita ya tashi ya dan zagaye falon yana observing komai na ciki, yana tsaye jikin wani frame ta shigo dauke da leda ta mika masa tana dan russunawa
” Gashi ka kaiwa Ammi, ina gaishe ta.”
Rik’e ledar yayi yana kallon ta, tayi saurin dauke kanta k’asa ta sakar masa ledar gabanta na faduwa.
” I love you.”
Ya samu kansa da whispering cikin muryar da tayi masifar shigewa ciki, wani irin feeling taji, sarai ta jishi sai tayi kamar bata ji ba, ta ja baya sosai tana diriricewa, shi kansa wani iri yake ji, be taba tunanin haka daga gareta ba, da tasan yadda Ammi take a wajen sa, da kuma yadda sakon nan yayi nasarar kara masa son ta ninkin ba ninkin, da tun ranar da ya fara zuwa tayi, kasa matsawa daga in da yake yayi, sai murmushi yake shi kadai.