HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 41-45

   Text message ta sake tura masa na ban hakuri, kamar yadda take masa kullum amma baya reply, ko ranar da yazo gaisuwa gidan taso suyi magana amma kemaimai ya ki bata dama karshe ma ya daga wayar Hajiyar sa yayi tafiyar sa ya barta a wajen.

*Adamawa-Yola*

Ayi maneji????????????

_ZAFAFA2022????_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*????????????

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*????????

09134848107

2/24/22, 08:09 – Buhainat: ®*Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *42*

***

*Adamawa-Yola*

Dukkan su sunyi shiru da abinda yake sak’awa a rai, idan har ta tabbata Muhammad yana da evidence akan su, toh gaba daya lissafin su ya sauya. Amma kuma akwai abin mamaki ace yasan komai tsawon wannan lokacin amma be taba fadawa kowa ba, hatta mahaifiyar sa da yafi kusanci da ita akkowaan kowa. 

   Sanarwar shigowar sa masarautar ya sake saka su cikin tashin hankali, rige rigen lekawa suke kowa yana so yaga da wacce yazo, ba karamin kaduwa sukayi ba ganin shi cikin shigar saurata yayi masifar kyau, ya dauki wani siririn glass fari ya dora akan fuskar sa, murmushi ne kwance a fuskar tasa yana tafiya irin ta kasaita. Fada ya wuce kansa tsaye, bayan ya tabbatar da an gama tattara duk wasu masu fad’a aji na masarautar tasu, shi kanshi Bubu a cike da Mamaki yake musamman da irin hakan bata taba faruwa, ba ruwan Muhammad din da harkar cikin gidan balle har ya nemi ganawa da manyan fadar.

    yadda ya shigo fadar kai tsaye ya saka wasu da yawa daga ciki yin mutuwar zaune, sakon shi ya iso musu tun kafin ya karaso. Wajen da ya saba zama ya samu ya zauna bayan ya kwashi gaisuwa. Su hudu suka shigo a tare hadda Kamal, suka samu waje suka zauna, daga nan bubu ya soma magana cikin nutsuwa da makasudin taruwar su a wajen. 

“Mun taru ne domin danmu Muhammad yana da bukatar ganawa da manyan masarautar saboda muhimmiyar maganar da ta kawo shi, wadda muke kyautata zaton zata kawo cigaba a masarautar tamu baki daya.”

Mikewa tsaye yayi ya sake gaisuwa sannan ya soma magana idon sa fes akan wambai da jama’ar sa.

“Tsawon lokaci na dauka ina bin diddigin mutuwar marigayi tsohon sarki. Duk da karancin shekarun da nake dashi a wanchan lokacin amma ban manta ba, ban manta fuskokin mutanen da sukayi sanadiyar mutuwar sa ba.”

Hayaniya ce ta cika fadar kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa cikin tsananin mamakin maganganun Mohammad din wanda shi kansa Bubun be san da wannan maganar ba. Murmushi ne a kwance a fuskar sa yana karanta tashin hankali dake kwance a fuskokin su, tuni suka fara jikewa da gumi cikin yanayi na wahalarwa

” Wacce irin magana ce wannan yarima?” 

Gyara tsaiwar sa yayi, ya sake kafe su da ido yace

“Ayi min afuwa, na dauko maganar daga sama, sai dai ba kai tsaye nazo da maganar ba sai dana tabbatar da ina da gamsashiyar shaida wanda zasu zama madafa a gareni.”

Babu be tanka ba, ya dai zuba masa ido yana kallon sa yadda ya dake ya sake burgeshi, ya kuma ji a ransa lallai Muhammad ya shiryawa koma menene ,yadda ya dade yana nuna halin ko in kula da harkar gidan sai ya dauka be san komai ba, ashe yana sane har yana kokarin samun hujjar da zai tsayawa wan nasa da ya tabbatar da akwai wani bayanin a cikin labarin mutuwar tasa.

“Mecece hujjar taka Yarima? Ko zamu iya sanin ta?”

“Kwarai.” Yace yana matsawa gaban Bubu, ya fito da envelope ya ajiye a gaban sa. Wannan ita ce hujjar da na rik’e nake kuma fatan abi duddugin abinda ya faru tun daga farko sannan ayi hukunci ga duk me hannu a ciki.

 Wani irin zillo wambai yayi, ya kalli Kamal ya kafe shi da ido yana masa alama da ya kasa ganewa, gaba daya ma shi baya cikin nutsuwar sa sakamakon maganar mahaifin sa da Mohammad ya taso da ita haka ta sama ta ka.

  

   Matsawa jikin wambai hakimi yayi, yayi masa magana cikin rada yace

“Nayi zaton mun riga mun samu shaidar da yake magana a kanta a wajen Kamal ko? Ko wata shaidar ce daban da bamu sani ba?”

“Yanzu ba lokacin maganar nan bace hakimi, kasan Kamal din be san flash din menene ba ya kawo mana, muyi fatan babu wata shaidar kuma.”

Moh na ankare dasu, yana kuma lura da yanayin su, wato a tunanin su sun zata flash din da ya basu a matsayin Musaddik shi kadai ne shaidar sa, lallai suna wasa dashi.

  Budewa Bubu envelope din akayi, flash guda biyu ne a ciki sai hoto da aka dauka amma yayi dishi-dishi alamun ya kwana biyu. Kallon hoton Bubu yayi sosai amma be gane komai ba. Projector aka kawo, aka jona Moh ya harde a wajen zaman sa yana fatan duk wanda yake cikin video din ya yanke jiki ya fadi a wajen saboda tashin hankali.

   Jikin wambai ne ya soma kakkarwa lokacin da aka kunna video, shine yake magana da Kilishi,maganar sa radau a lokacin da yake ce mata in dai suna so su rufe sirrinsu sai dai su kawar da maimartaba, da fari batayi na’am da maganar tasa ba, amma yayi yadda zaiyi ya saka ta amince, daga nan sai hoton ya dauke sai kara shuuu da ta cika wajen, zare shi akayi aka saka dayan, wanda yafi tayar da hankalin mutane, tsohon sarki ne a kwance sanda suke kokarin kashe shi, babu irin magiyar da be musu ba, amma suka ki, suka kashe shi ta hanyar danna masa pillow har sai da ya daina numfashi gaba daya, akan dalili daya tal, dalilin ya gano zaluncin da suka dade suna masa shi da Kilishi, dalilin da su da kansu zasuyi wa fad’a bayani kafin yasa a tusa keyar su.

Salati ne ya cika a fadar, Bubu ya kawar da kansa yana jin dadi da Aji baya wajen, dalilin kenan da Muhammad din ya hanashi zuwa yace ya zauna a gida, dole idan yaga tashin hankalin nan ya rikice ga yanayi na girma.

  

Mikewa wambai yayi ya hau fad’a yana nuna Moh

“Karya yake yi wallahi karya yake, wannan shiryawa akayi amma karya ne, ni zaka wulakanta ko?”

Wasu fadawa ne majiya karfi suka taso, suka dankwafar dashi sannan suka ce

“Karya kake yi dan talakawa, Yarima yafi karfin ka jefe shi da wannan kalmar.”

“Ku kyale shi.” Yace kamar be damu ba, ya kalli Bubu da shima yake kallo ya yi masa murnushin kafin yace

“Za’a ji sauran bayanan da dalilin su na aikata wannan mummunan aikin daga wajen su.”

“Me zuku ce game da wannan video da Yarima ya gabatar?” 

Bubu yayi maganar yana dubansu dukkasu, kamar wanda aka soma a ruwan zafi haka sukayi tsamo tsamo, babu me magana a cikin su dan basu da bakin da zasu karyata shi, hawaye sosai Kamal yake bayan ya gama amincewa dasu ashe mayaudara ne. Juyar da fuskar sa Bubu yayi, yan sandan da Moh ya kira suka shigo, suka tattara su gaba daya suka fita dasu, jikin kowa yayi masifar sanyi da abinda ya faru, sannan sun yabawa kwazon Moh, sun kuma yarda da chanchantar sa na zama shugabansu, a take wasu suka fara maganar, Bubu na jinsu ya dinga murmushi yana kallon tilon dan nasa, cikin so da kauna, a yanzu ya kara tabbatar masa da shine zabi na kwarai da zai wa al’ummar sa, ya kuma gane dalilin sa na kin amsa tayin sa tsawon lokaci, ya kuma gane dalilin sa na zuwa a sauya dukkan tsarin sarautar gidan tasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button