HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

 

1/31/22, 19:12 – Buhainat: Halin Girma

      21

 

 

Ta kofar ya koma ya fice bayan ya tabbatar da ya isar mata da
sakon da yake son isarwa, yana kallon yadda tayi laushi sosai ta bishi da kallo
har ya fice gaba daya.

   Kai tsaye wayar sa ya dauka ya kira Bashir, ya
daga yana tafiya zuwa shashen Takawa dan yana son ganin shi

 

“Ya akayi Bashir?”

 

“Barka da warhaka Ranka ya dade”

 

” Barka dai, ya taro?”

 

” Mun gode Allah, an kawo amarya yallabai.”

 

” Yayi kyau, Allah ya baku zaman lafiya, ka kula da ita
sosai kar naji wani abu mara dadi, karka kuma taba yarda mahaifiyar ta ko wani
yace zai taka ka akan matar ka.”

 

” In Sha Allah ranka ya dade, hakan ba zata faru ba.”

 

“Yayi kyau, sakon ka na wajen Musaddik.”

 

Godiya ya hau yi dan dama abinda ya saka kiran kenan. Cilla
wayar yayi a aljihu sanda ya isa sashen Takawan da ya zata ya jima da isa a
adamawa.

 

***A tsorace take tun bayan da mutane suka yaye, yan matan biyu
da aka barta dasu suma basu wani jima ba suka cikawa wandon su iska dan ba zasu
iya zaman ba, babu kalar ma da bata yi musu ba akan su zauna amma suka ki, a
cewar su idan suka zauna basu san uban da zai maida su gida ba su ba samari
masu mota ba ga unguwar da shegen nisa kafin kaje titi. Haka tana ji tana gani
suka yi tafiyar su suka barta. Tasha kuka kuwa kamar ba zata mutu, ta dinga tsinewa
Bashir albarka taji kamar ta gudu ta bar garin ma baki daya.

   Tana nan a zaune cikin duhu taji ana saka mukulli
a kofar gidan, tashi tayi da sauri tana zaro ido,a duhu take dan dama da wayar
ta, ta haska kuma babu charge ta mutu tun dazu.

   Shigowa yayi yana haske gidan da wayar sa, ya
shigo ciki ya dalle ta, tayi saurin kare fuskar ta tana cewa

 

“Waye!” A tsorace

 

“Amarsu ta ango.”

 

Wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin muryar sa, tayi kansa
da sauri ta hau kai masa duka tana kuka

 

“Allah ya isa ban yafe maka ba, Allah ya isa.”

 

Rik’e hannun nata yayi da karfi ya juyar da ita ta dawo tana
jingina da bayan sa

 

“Ni kike wa Allah ya isa? Lallai ma yarinyar nan.”

 

“Allah ya isa na fad’a mugu, macuci maha’inci.”

 

Juyo da ita yayi ransa na soyuwa amma ya danne kamar be ji komai
ba, ya dalle mata baki da bayan hannun sa, yayi murmushi yana sake haske ta

 

“Duk abinda ma zaki ce ki fad’a amaryata.”

 

Kuka ta shiga rusa wa da karfi, ganin zata iya jawowa a jiyo su
a makota ya sakashi jawota ya shiga sumbatar ta, ta dinga dukansa tana harbin
sa a kafa amma ko a jikin sa, sai da ya gajiyar da ita sosai sannan ya saketa
yana murmushin, a kalla ya rage zafi dan yasan ba lallai Hajjaju ta yarda ta
barshi ba.

   A wajen ta duk’a tana kuka, ta dinga jin kamar ta
mutu ta huta da abinda take ji, tana jinshi yana waya har ya gama kafin ya
dagata tsaye ya rik’e hannun ta a cikin nasa su shiga barin gidan.

   Mota ce a kofar gidan irin wadda yake zuwa wajen
ta zance, bud’e mata gaba yayi ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga
mazaunin driver ya tada motar suka bar unguwar.

   Tafiya sukayi da dan nisa har suka iso unguwa,
gangarawa taga yayi zuwa wata doguwar hanya suka dinga tafiya kafin su isa
kofar wani babban gida, horn taga yayi da sauri me gadin ya bud’e gidan ya
shiga da motar ciki. Tunanin ta ne ya tafi wani waje daban, ko dai Bashir gwada
ta yake yana so yaga yadda zatayi idan ya kaita wanchan gidan shiyasa ya kai
ta? Ko kuma dai duk shiri ne. Murmushi ya sakar mata ta cikin hasken da ya
hasko cikin motar bayan ya tsaya a gaban ginin gidan.

   Sauri taga yayi ya bud’e motar sanda wata babbar
mata hamshakiya ta nufo su cikin wata irin kwalliya, ta sha ado sosai tana
walwali, katuwar gaske ce dan zatayi biyu ko ma ukun Bashir din idaan aka hade
shi da Zeenat din waje daya.

    Kafin ta kai ga garasowa Bashir din ya isa
wajenta. Yayi kamar zai zube a k’asa a gabanta, ta riko shi tana masa murmushi,
ware ido sosai Zeenat tayi tana tunani toh ko Maman shi ce? Karasowa tayi
daidai kofar da Zeenat din take ciki ta bud’e mata tana sakar mata murmushi

 

“Amarya.”

 

Ta kira ta tana sakin hannun Bashir din ta kama na Zeenat din
tana jawo ta daga ciki.

 

“Sannu da zuwa kanwata, sannu sannu.”

 

“Kanwata?”

 

Zeenat ta maimaita sunan tana bin Bashir da kallon neman karin
bayani amma sai taga ya fuske kamar be ganta ba. Takawa suka shiga yi har zuwa
cikin gidan wani babban falo da yasha kawa sosai. Wasu mata ne hamshakai suma
kamar matar farkon suka tarbi Zeenat din suna tafi, ita dai Zeenat gaba daya
kanta ya kulle jira take su samu kebewa da Bashir ta tambaye shi me yake
faruwa. Zaunar da ita matar tayi ta ja hannun Bashir din sauran mstan suka hau
shewa da dariya, bin su Zeenat tayi da ido har suka haura sama, zuwa anjima kad’an
sai gata ta sakko ita kadai babu Bashir din cikin shigar kayan bacci ta karaso
falon ta kalli sauran matan tace

 

“A rakata dakin ta ko?”

 

“An gama Lay, an gama.”

 

Suka tashi gaba daya, daya ta kama Zeenat din suka nufi wata
hanya da take a bayan kafar benen dake falon, wani dogon corridor ne suka bishi
har zuwa bayan dakunan gidan, sai wani daki guda daya a wajen da kofar sa tana
kallon kofar da suka fito, nan taga an bud’e, sannan sun shiga gaba daya ciki.

   Katifa ce a k’asa karama kamar ta yan boarding
sai wata karamar kujerar roba fara, suna shiga kamar jira dama suke matar da ta
shigo da ita ta wurgar da ita a saman kujerar har sai da kanta ya bugu da
bango, tayi kara saboda zafin da taji kafin wadda suke kira da Hajiya Lay
(Layuza) ta rankwafo akanta tana mata kallon tsana tace

 

“Ke dan yar iska ce ke, har kin isa mu hada miji daya? Kin
isa nayi sharing dake? Karamar yarinya da bata fi sa’ar yata karama ba, kece
kishiyata ko? Toh ni ko a zamanin kuruciya ban zauna da kishiya ba balle yanzu
da nasan ciwon kaina nasan abinda nake so, dan haka nan dakin da nake ajiye
masu aiki nane kuma na sallame su dan yanzu basu da amfani, sai ki cigaba daga
in da suka tsaya, shara wanke wanke, wankin undies dina da girki, komai ma dai
da kika sani.”

 

Gaba daya kwakwalwar Zeenat ta gaza gane me matar take cewa, ji
tayi kamar wani yare take mata na daban da bata sanshi ba, ta dinga jujjuya
kanta tana son gasgata abinda taji akan Bashir din, yana da mata dama? Mata
babba kamar wanna da ta yi sa’ar uwarsa? Abba ne ya fado mata, sanda ya kirata
yake mata magiya kamar ba Mahaifin ta ba, ya kaskantar da kansa yana rokon ta
akan ta rufa masa asiri ta hakura da Bashir amma ta shafawa idon ta toka, ta
kekeshe kasa tace taji ta gani, yanzu ta yaya hakkin Abban ta zai barta? Tun a
ranar farko ta fara fuskantar wannan tashin hankalin.

   Firgigit tayi sanda taji saukar abu kamar ruwa
asaman fuskar ta, ta saka hannu ta shafa da sauri tana daga kanta

 

“Kinji abinda na fad’a miki ko?”

 

A hankali ta daga kanta alamar eh, ta daka mata tsawa tace

 

“Baki zaki bud’e kiyi min magana bana son rainin
wayo.”

 

“Naji.” Tace tana barin kwallar da ta taru a idonta ta
shiga sakkowa saman fuskarta. Dariya suka kwashe da ita, suka juya suka fita
suna cigaba da zantuttukan su mara sa dadi ji.

 

***Bangaren amarya Iman kuwa komai na tafiya daidai, ta dade
batayi bacci ba tana tunanin Moh da kalar soyayyar sa me tsayawa a zuciya,
koman sa abin so da birgewa ne tun daga maganar sa har yadda yake tafiyar da
ita. Da k’yar ta samu bacci ya dauke ta bayan ta gama tunanin nasa. Tun asubah
da suka farka basu koma ba, kana jin yadda hayaniya take tashi a masarautar
kasan akwai gagarumin shirin da ake yi. Shiryawa suka hau yi ita ta fara wanka
sannan su Khadija suka yi. Suna fitowa falon suka tarar da abinci a jere na
alfarma yana jiran su, nan suka hau kai suka ci suka yi nak, sannan aka turo
tafiya da Iman din shashen Fulani. Alkyabba aka sake saka mata sannan suka fito
kanta na k’asa tana jin yadda take shan gaisuwa kamar ta tsaya ta amsa amma yan
matan nan sunce mata ksr ta tsaya amsawa haka sarautar take.

   Da murna Fulani ta tarbe ta yau din ma, ta saka
aka kaita har uwar dakin ta in da mutane suka dinga shigowa suna ganin ta wanda
suke da kusanci da gidan. Ta jima sosai anan har suka soma jin tashin kidan
kwarya in da adaidai lokacin su Mamma suka iso sai dai babu Mama, gaisuwa aka
sake kafin a rakasu in da ake kidan kwaryar aka nuna musu wajen zaman su, kafin
daga bisani a rako Iman din wajen itama.

   Da yamma kuma aka dawo ciki aka sake shiryawa in
da aka nufi hall din dan gabatar da bikin da kuma kyaututtukan da aka shiryawa
Iman din.

  Sakon Maimartaba ne ya samu Fulani akan yana son ganin
Matar Muhammad din dan a yau zasu wuce komai dare, mamaki ya kama Fulani dan a
yadda suka shirya kwanaki uku zasuyi a nan din kafin su tafi adamawar, bata
sani ba Muhammad din ne da kansa yaje ya samu Takawan ya roke shi akan a rage
bidiar dan shi kam ya gaji sosai, take kuwa ya amince har ma ya sanar da Bubu
tun a daren jiyan.

   Maimakon a wuce da ita hall din sai aka fara
kaita wajen Takawar. Kanta a k’asa sosai kwarjinin sa ya cika wajen ta yadda
kowa ya kasa sakewa, nasiha ya soma yi cikin maganar sa da ta saka jikin kowa
mutuwa, yayi musu fatan alkhairi sannan ya kare da sake jan hankulan mutane
akan yadda rayuwar ta zama, basu dade a wajen ba, suka fito kowa na yaba
karamci na Maimartaba da ya karbe su hannu bibiyu ba tare da nuna banbanci ko
wani abu ba.

   A gaggauce akayi taron, saboda tafiyar da zasuyi,
sosai iman ta samu kyaututtuka masu tarin yawa a yan awowin da basu gaza biyar
ba, kowa so yake ace shine yafi, kowa so yake ya burge Fulani da Maimartaba,
dan kowa ya san yadda muhammad din yake a zukatansu.

 

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button