HALIN GIRMA 41-45

Yana kallon yadda mutane suka dinga zuwa suna kwasar gaisuwa, fuskar sa a sake yake amsa musu, da haka ya samu ya zame ya fice daga fadar ya nufi bangaren Kilishi wanda yasan sakon sa ya riga ya iske ta, ko tana wanne hali yanzu? Zai je ya gani da idon sa kafin ya karasa wajen Ammin sa, yana son ganin Laila suyi maganar Samha bayan nan.
A duk abinda ya faru abu daya ne yayi masa ciwo, shine bayyananr asalin Kamal wanda ya kasance da ne ga wambai da Kilishi, ba dan tsohon sarkin bane, dalilin da ya saka su kashe shi kenan, saboda su binne gaskiya, su binne cin amanar da sukayi masa, duk don soyayyar su da mulki. Amma dole ba yadda ya iya, dole ne gaskiya tayi halin ta, ko da be fad’a a gaban kowa ba, yasan wadanda suke da hakkin su sani zasu sani din.
Da kwarin guiwar sa ya isa shashen nata, ya shiga kai tsaye ba tare da wani ta tsaida shi ba, ya kuma sameta a zaune tana ta kuka wiwi, kamar wadda aka ce wani nata ya mutu, Kamal na tsaye a kanta ransa na suya, be taba tunanin abinda suka aikata ba kenan.
Wani abu ne ya daki Moha, a karo na farko yaji tausayin su dukka, yasan rudin duniya da shaidan ne ya dibi Kilishi ta aikata abinda ta aikata din, shiyasa a kullum take shakkar sa, ta kasa aikata masa komai saboda yasan wani bangare na sirrinta, a tunaniin ta maganin ta ne ya ci shi da ya nuna halin ko in kula da harkar gidan, bata san yayi hakan bane domin ya samu gamsassun hujjoji, wanda zai karya duk wani mara gaskiya da tsoron Allah, ya kuma karbi kujerar da ta jima tana dakon jiran shi. Ya kuma amsa sunan Sarki Muhammad Ahmad Santuraki!
*****
Satin ta daya aka sallameta, suka tattaro suka dawo gida,kwana daya su Mamma ta kara itama ta tafi dama Mummy ta wuce tun a kwana uku da tayi a asibitin. Gidan ne duk taji yayi mata ba dadi, ta mike daga kwanciyar da tayi tunanin mutuwar Mahfuz na bijiro mata, tayi kuka sosai da ta samu labarin dalilin ta ne ya gamu da iftila’in, shiyasa aka ce ajali ko aina yake komai nisan wajen sai kaje ka tarar dashi.
Ranar da Yaya mahaifiyar sa tazo sai da kowa ya tausaya mata, dan yadda take magana kadai zaka gane yadda mutuwar ta dake ta, mutuwar danka saurayi matashi ya tasa, bata tafi ba har yanxu kuma kusan kullum sai tazo asibitin taga Iman din wadda take sake sakata jin nauyin ta har ma da shi kansa Muhammad din, kwata kwata sai ya rage zuwa asibitin dan baya son suna haduwa zuciyar sa karye wa take, daga baya ma sai ya shirya tafiya adamawa yana kuma chan har aka sallame ta be dawo ba sai waya da suke yi.
Sallama taji anayi daga falo, ta mike a hankali saboda rashin kwarin jikin da take fama dashi, ta bud’e kofar ta fito. Da dan saurin ta ta karasa ganin yan matan nan ne da suka taba zuwar mata. Su biyu ne yanzu suka gaishe ta ta amsa a sake tana zama kusa da daya da take kan three seater tace
“Ashe zaku zo?”
“Eh Fulani ce tace muzo mu tayaki zama kafin Ya Moha ya dawo.”
“Kai amma naji dadi, sannun ku da zuwa ya mutanen gidan?”
“Lafiya lou, ya jikin? Allah ya kara sauki.”
“Amin ya Allah, Nagode.”
Sai suka shiga hira suna bata labarin gidan su da wasu yan uwansu da duk sai a dubiyar ta sassansu. Ummimi ce ta shigo ta gaida su ta gyara wajen dining sannan ta fita, ta dawo dauke da manyan warmers ta jera a wajen tsaf sannan ta sake fita.
Su kadai suka ci abincin dan bata da appetite har lokacin, tea kawai ta sake sha tace zata dan kwanta, ta haye sama ta barsu suna kallo da danne dannen waya.
Tayi nisa sosai a cikin baccin ta wayar ta dake jikin socket ta shiga kara, kamar ba zata tashi ba, saboda yadda baccin ya soma dadi, kiran ne ya kara shigowa bayan wanchan ya katse, ta tashi da k’yar ta dauko wayar ta daga
“Hajiya kinyi bakuwa.”
“Wacece?”
Mike mata wayar yayi
“Nice Iman…”
“Zeenat, sannu da zuwa bashi wayar.”
“Sister dina ce, ku kyale ta.”
Ta katse kiran ta mike gaba daya ta shiga toilet ta gyara jikinta ta sauya pad sannan ta sakko. Da fara’a take kallon Zeenat din dake zaune tana karewa falon kallo cikin yanayi me ban tausayi, bata san Iman din ta fito ba har sai da ta dan dafa ta, ta kira sunan ta
“Sannu da zuwa.”
Tace tana murmushi
“Yawwa, bacci kike kamar na tashe ki.”
“Wallahi kinsan har yanzu ban gama samun sauki gaba daya ba, ya gida yasu Mama?”
“Lafiya lou wallahi.”
” Ya jikin?”
” Da sauki Alhamdulillah.”
” Allah ya kara sauki, ya bada na aike me albarka.”
” Amin.”
“Sai kika ganni kawai.”
“Umm…”
Tace tana mikewa tayi hanyar kitchen, taje ta fad’a musu abinda zasu kawo sannan ta dawo tace ta taso, suka shiga wani daki a k’asan, suna shiga ta cire mayafin jikin ta da dankwalin ta ajiye a gefe.
Sallama Ummimi dake dauke da tray da abinci da ruwa tayi ta ajiye ta gaishe ta sannan ta ja musu kofar.
“Bismillah ga abinci.”
“Toh…” Ta jawo kayan ta bud’e, yawun ta ya cinke ta zauna dirshan ta shiga dibar abincin nan babu kakkautawa, Iman na kallon ta bata ce mata komai ba, sai data ci ta koshi tasha juice da ruwa sannan ta mike kafarta sanyin AC na ratsa ta sosai.
“Magana ce ta kawo ni, dan Allah taimako na zakiyi Iman.”
“Me ya faru?”
“Dan Allah yallaban zaki ma magana ya kira Bashir dan Allah ya zo ya maida ni, wallahi na gaji so nake na koma dakin mijina.”
“Kina nufin dama kina gida?”
“Tun yaushe? Tun sunan Anty Bilki fa.”
“Kai wallahi ban sani ba, matsala kuka samu?”
“Uhmm..”
“Ina jinki.”
“Shi da Mama ne, bayan yazo mu tafi mama tace ba in da zani taje ta same shi a waje bansan me ta gaggayawa masa ba, shikenan ya kyale ni.”
“Abba kuma ya sani?”
“Ya sani, har magana yayi min wallahi, amma Bashir din yaki zuwa kemaimai, har gidansu Mama tasa Ya Habib ya kaini amma sam yaki, a dah ban damu ba, amma wallahi yanzu nayi karatun ta natsu, ko dan dan tahalikin nan da yake cikina.”
“Kema kinyi wauta, ita rayuwar nan baki daya da kika gani kowa hakuri yake da yadda tazo masa, shi kuma arziki lokaci ne.”
” Haka ne, na ga aya ai, son zuciya bacin ta, daga kin gaskiya aka ce sai bata, kema sam ban kyauta miki ba abubuwan da nayi miki a baya, ko yanzu kinga sakayya, Allah ya baki miji me sonki na nuna sa’a, gashi ya hada duk wasu qualities.”
” Ni ban rik’e ki ba ko da din ma.”
” Um um Iman, ni dai kiyi hakuri dan Allah.”
” Na hakura toh.”
” Nagode Allah ya saka da alkhairi, dan Allah ki taimaka ki masa maganar nasan shi idan shi ya kirashi ba zai taba ki ba.”
” Bari kiga.” Tace tana tashi, taje ta dauko wayar ta dawo, ta zauna sannan ta kirashi
” Bari naji idan yana free sai muyi maganar kawai.”
“Yawwa dan Allah.”
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikisalam Baby, na zata bacci kike ai, shiyasa ban kiraki ba ina jira ki tashi.”
“Na tashi ai, ban jima ina baccin ba. ”
” Kar dai yaran chan ne suka hanaki baccin da shegen surutun su. ”
” A ah, Zeenat ce tazo. ”
” Zeenat? ” Yace cikin son tuno sunan,
” Zeenat fa. ”
” Oh wai matar Bashir? ”
” Kai ko? ”
” Allah na manta ta, lallai ta kyauta, duba ki tazo. ”
” Eh. ”
” Ok yayi, ya gidan ya missing dina? ”
” Ina nan inayi, amma kad’an. ”
” Kiji tsoron Allah, ni nasan kinyi missing dina kamar yadda nayi ”
” Umm.. haka dai kace. ”
” Haka ne ma, idan na dawo zan gasgata kai na ai.”
” Can’t wait.” Ta saka dariya
” Toh me yake faruwa? Babu wata matsala dai ko?”